Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

TARAR ARADU littafi na daya page 6

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 6
Ta nuna min dakin farida.
“Tana nan inaga shiryawa takeyi”
Ba’ajimaba ta leko
“Umar shigo mana”
Na karasa ,bayau na fara shiga dakinba yanada tasari
matukar tsari.
Akalla yalunka nawa ko uku ko hudu.
Na cusa kaina bayan nacire takalmi.
Tuni tagama shiryawa tana daure gashin kanta ne da
ribbon.
Na kalli dressing din nata na doguwar riga mai hade da
wandonta,da kuma gyaran mayafi. Hakika sun yimata
kyauw
Ni kaina sai na tabbatar da cewa farida tafi karfina.
Sai kuma na sami zuciyata tana mai rayamin cewa afasa
tafiyar kar naje wani ya ganta ya kwacemin ita.
Maganarta ta katsemin tunanina
“Muje ko umar”
Nafito yayin data biyoni.
Mahaifiyarta ta kallemu ta jinjina kai gami da cewa
“You match each other”
Cikin wani harshen dabashi da banbanci dana turawa ,
nida farida muka kalli juna gami da musayar murmushi.
Bisa gaskiya .
Gasikaya ne abinda tafada ta dubemu
“Kuna da camara ko”
Na girgiza kai
“Bamu da camara”
“Tafiyar taku bata cika ba, a london duk duk inda zamuje
da Alhaji da camera muke tafiya haka kuma zaka rinka
gani ga duk saurayii da budurwa”
Ta mike tsaye
“Bari dauko muku tawa”
Ta shiga daki bada jimawa ba ta fito.
Yar karamar camara ce mai ban sha’awa, ta bude kwalin
film ta loda, sannan ta dubemu
“Kuzo nafarayi muku kala daya”
Muka jeru nida farida muna jiran muga ta dauka,
maimakon haka sai ta kama dariya, tafara magana
“Karfa nace muku kauyawa, ahaka za’ayi hoton? To
ma’anar me yabayar? Kubari kuga yanda za’ayi”
Ta nuna mana wata fulawa dake tsakiyar gidan
“Ku koma can, kusa fulawar a tsakiya”
Muka kamar yadda tafada.
Sannan tace
“To kai umar tsinki fure ka mika mata ke kuma miko
hannu ki karba, ku kumayiwa juna murmushi”
Mukayi kamar yadda tafada , sannan hoton,
Kyamarar taja film automatically.
Ta mikomin kyamarar
“To kunga yadda ake hoton soyayya , idan anyi aure
kuma akwai wani salon daban,dasannu zan nuna muku
shi duk randa aka daura maku aure”
Nayi dariya
“Mungode mummy”
Surukartawa tana burgeni, yadda take bidani ta hanyoyi
na musamman babu abin da yadameta tamkar ba suruka
ba.
“To zamu tafi mummy”
Farida tace daita
“To adawo lafya”
Gab da zamu shiga soro tafara magana
” Ina kara tunatar dakufa”
Muka waiwayo domin jin abidna zata fada , tayi
murmushi
” Kun dace da juna “
Muka kalli juna nida farida mukayi musayan murmushi.
Sannan muka juya gareta gaba daya.
Akuma lokaci guda muka hada baki
” Thank you mummy”
******** ********** ********
Na bude shagona bayan dana dawo daga koyarwa .
Bayan na ajiye takardu sainafara tunanin yin wanka.
Na dubi ruwan wankan wanda ni kawai yake jira na
watsashi, adai dai lokacinne aka turo kofar cikin gidar
“Umar ana waya”
Inji matar yayana na dubeta
“Wanene yake waya? Ko baba ne?”
Ta juya hannu
” Ba baba bane yadaice kai yake son yagani”
Na jawop kofar shagopn na bita ciki, ina zuwa na dauka
na kara akunne
“Hello! Wake magana?”
“Ina ruwanka koma waye? Kadai kasa kunne da kyau kaji
abinda za’afada”
“Ina jinka”
Nace dashi yacigaba
“Karabu da farida tun kafin karasa ranka,karabu da ita
tun kafin ta zamto maka cowon ajali”
Na gwale ido saboda tsoro , akuma lokaciguda dana fara
tambayarsa cikin rawar murya .
“Saboda me”
Yadaka min tsawa , duk da awayane saida cikina tai kuka
“Karabu da ita muddin kai kanason rayuwarka ,inkuma
duniya ta isheka sai kafada
“Wai me isa”
Nakara tambayarsa
“Farida bazatayi aure ba har abada”
Lafazinnasa yabata min rai bansan sa’an danace
“Kar ya kake ba”
Ya barke da dariya wadda saida na kauda kan wayar yaci
gaba.
“Dan samari da karambani kake inakai ina karyata abin
da’aka ba ka labarinsa”
“Karya kake”
Nasake fadi
“Farida zatayio aure kuma ni zata aura”
” Shikenan babu mamaki amma dai ba’awannan duniyar
ba”
Na fusata
“Kai makaryaci awannan duniyar kuwa”
Yasake dakamin tsawa
“To shikenan tun da zaka iya TARAR ARADU DAKA .naga
kai mai musune, zamuyi wasa dakai yanda akeyi da dan
biri,sannan a karramaka kamar yadda ake karrama kudi”
Kafin nasake magana ya ajiye kan wayar.
Na dawo shago duk jikina a mace .
Babu mutumin nanne da farida tabani labari.
Inkuwa hakane hakika ina kan hadari.
Sai na kudure azuciyata bazan bawa farida labari ba.
Domin hakan zai iya tashin hankalinta harta fara hangen
kin yiwuwar aurenmu.
Ni kuwa bazanso hakaba. Sannan kuma na kudiri aniyar
bazan shaidawa yayana ba.
Domin kuwa shaidamasa kamar cinna ma takardar
alkawarinmu aurenmu da farida wutane,
Domin babu makawa zai rabani da’ita
Nikuwa ahalin yuanzu duka biyun sakamako daya zasu
bayar, tamkar shida atara da uku ne,da kuma uku atara
dashida,kowanne tara kenan
To hakama in har kaunar farida zata jamin mutuwa to
hakama barinta zaijamin.
Domin ahalin yanzu inna rasata ma zuciyata na iya
bugawa to kaga da wuya ya kasheka gara dadi ya kasheka
to waima da yake cewa zai yi wasa dani…..
@mr:-Shuraih 99%
Zan cigaba

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.