TARAR ARADU littafi na daya page 5

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 5
Ni kuwa gani da farinjini.
Aka rinka zuwa wajena naki fita don saboda ina ganin
hanani karatu za’ayi. Don babu abinda irin da daddare
narinka nazari , ahankali na kammala digirina akan
mathematics .
Nakuma yi bautar kasa, sai maganar aure . Nan muka
fara soyayya da wani matashi habib , dan kasuwar kwari
ina mutuwar sonsa ana kokarin samana rana .
Watarana yazo tsallakawa titi dominisa wajen motarsa
wani mai mota yazo ya bankeshi.ko shurawa baiyiba .
Mai motar kuma yagudu”
Sai naga hawaye nazuba daga idonta .
Tacigaba
“Naci kuka har na gode Allah bayan komai yalafa sai
muka kulla da wani ma’aikacin savannah bank mai suna
isma’il soyayyar dayake nuna min hartamantar dani na
habib.
Asheshima ba rabonane ba.
Babbar motace tabi takan motarsa starlet.
Da kyar akaringa banbaro namarsa gashi kuma cikin
darene abin ya afku.
Ba’asan inda mai motar yayiba.
Hankalina yayi mugun tashi yanda kasan nayi hauka
sabida yanda nakeson isma’I’ll banso habib ba,
nakasance cikin damuwa yanda samarina ke mutuwa
haka , sai natina zancen mutuminnan shkekaru biyu dasu
ka gabata.
Babu shakka shirinsane anan na shidawa mahaifiyata.
Tace saidai Addu’a tunda ba’asan inda yake ba .kuma ni
kaina tundaga ranar bansake jin duriyarasa ba.
Aifa wannan abubuwa dasuka faru suka sanya akafara
yimin son rakumin yara.
Sai dai mutum yabar kaunar dayakeyimin azuciyarsa
amma babu damar ya baiyana.
Na nesa kuwa ko mutum yafara zuwa sai naga ya janye
narasa dalili.
San dade ana haka sai wani dan’uwana yace yaji yagani
babu wani mamaci sai wanda kwanakinsa suka kare.
Saboda haka yace mahaukaci yahau kura
Sabida haka muka cigaba da soyayya abin gwanin
birgewa har ya mantar dani duk nabaya aka samana
rana.
Sai da abin yarage sati daya kawai akka tsinci gawarsa a
tsakiyar titi.
Aifa daganan sai zamto mujiya ma tafini farinjini.
Babu wani saurayi da yake fuskan tata”
Saita fashe da kuka har nayi zaton bazatayi shiruba.
Nima saida kwalla tazubo min don tausayawa taci gaba
“Wannan shine dalilin dayasa kaga naki amasa maka,
domin kuwa duk wanda ya kulla alakar soyayya dani
sunansa matacce, nikuma banso wani abu ya sameka.
Na dauki kaddara akan cewa Allah bai yi zanyi aure ba.
Domin kuwa har sai na sami wani ya dan kaunace ni
sannan zan ji sarai. Wanda ahalin yanzu abune mara
yiwuwa”
Nadaga mata hannu
“Dakata farida ni ina kaunarki”
Ta girgiza kai
“Bazai yiwuba umar banaso ka mutu sabida kaunar
danakeyi maka”
Na dubeta
“Don Allah farida da gaskene kina kaunata?”
Ta gyada kai
“Wallahi umar inayi maka kaunar da bantabayi ma wani
kamar taba”
Na mike tsaye
“To in hakane farida na daura damarar neman aurenki
koda zan mutu”
Na sun kuyo kusa da fuskarta.
“Wallahi farida babu wata wuya dazatasa na dakata”
Ta girgiza kai kuma alokacin data kirawo sunana ahankali
“Umar ,zaifi kyau kaje kasami. Wata domin samawa
kanka kwanciyar hankali”
Na bata fuska
“To ba kya kunata kenan”
Ta girgiza kai
“Bahaka bane”
“To kice kina kaunata da aure”
Tayi shiru kawai tana dubana
“To shikenan farida barinatafi tunda bakya klaunata”
Najuya cikin hanzari ,ta tare kofar na kalleta babu alamar
fara’a a fuskata
“Way or reply”
Nace da ita , murmushine yafara sauka akan lebenta
,sannan tafara fadin wasu kalmomimasu tsada
“Ina kaunarka da aure umar”
Sai wani farinciki ya mamayeni, kaunarta ya kara shiga
raina murmushi ya kubuce min.
Akuma lokaci guda dana sula le akan kujera.
Ban kula da hadarin dana ke akai ba.
“Za kiga abinda ake kira tsantsar kauna farida”
Shine abinda bakina yafara fada.
******* ********** ********
Tun daga ranar danaje gidan su farida sai ya zamo a
kowane lokaci in ina tafiya akan babur nakantafine cikin
taka tsantsan.
Kai kace mai keken daya doro ciyawa gaba da baya kuma
ya debi garke tumaki,badon komaiba kuwa saidon samun
garkuwa daga mutumin da farida tace min shine
sanadiyyar mutuwar masi neman arenta har mutum uku
Na kirga adadin makwanni cikin tafi daya.
Amma har yanzu banga abinda ya sameni ba nida farida.
Munyi matukar shiga ran juna.
Soyayya agida sannan wani salon dabn a makaranta.
Mahaifiyarta tayi matukar faribciki da soyayyarmu, baka
da baka ta fadamin
Duk samarin farinda dasuka shede bataga wabda suka
dace da juna kamar niba.
Allah yabar ku tare har abada naji dadin maganar.
Yau ranace ta lahadi da kuma muka shirya zuwa yawon
bude ido dabi da masoyiyata.
Sabbabin jacket nasiyo musamman don tafiyar ta kara
armashi
Nahadu iya haduwa. Ga wanda bai sanniba zai dauka dan
wani ne daga yayan jiga jigan garinnan nan kuwa ba haka
lamarin yakeba.
Na iso gidan su farida da misalin karfe hudu, ahalin yanzu
nazama dan gidan salllama kawai nayinashiga,
Na tarar da mahaifiyarta tana karanta wat mujallar Africa
banyi mamaki ba
Sakamakon cewa na dade da sanin cewa tan jin har shen
nasara sakamakon zama a kasar ingla na tsuguna na
gaisheta ta amasa da fara’a bisa dukkanin alamu shigar
tawa ta burgeta.
Ta nuna min dakin farida……
@mr shuraih 99%
Tobe con….

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.