Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

TARAR ARADU littafi na daya page 4

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 4
Na Jin jina kai taci gaba
“To kuma matarsa biyu hajiya halima uwargidan da
kuma hajiya safiyya wato mahaifiyata, kuma ita
uwargidan yayanta hudu uku maza daya mace.
Mazan kuma sune manya kuma abokanan harkar
mahifinmu wato masu taimaksa,ni kuma ni kadiace
awajen mahaifiyata.
Ina da shekara biyu Allah ya karbi abinsa kuma yayyen
namu sune suka san kudaden mahaifinmu na banki
hakanan kadarorinsa.
Wannan yabasu damar yin rubda ciki akan
kudin,hakazalika kadarorin, gidajenma cewa sukayi uku
kawai yabari duk sauran ya sayar dasu yabiya bashin
kamfaninnuwa.
Sai suka bamu wannan gida dakuma naira miliyan daya”
Nakar kada harshe game da jijjiga kai
Taci gaba ‘yanuwan mahaifiyata sunta bata shawara akan
takai kara amma tace sam wanda yatara dinma yau ina
yake? Saboda haka ta hakura
Arzikin dake tsakanin suma na ‘ya ai ya isa tayi ta renona
ta sanyani a nursery kai har zuwa lokacin dana sami shiga
jami’a nai ta fama da takardu daga samari.
An kuma sha tareni fuska da fuska.
To amma ban kula ba domin alokacin burina nayi digri
na kuma sami damar tallafawa kaina da mahaifiyata.
Kamar kullum na tsaya abakin titi don samun mota
akokarina na dawowa daga makaranata.
Wata honda hala tayi fakin agabana, ahankali bakin
gilashin na kofar direba ta fara janyewa ahankali, yana
gama janyewa sai naga ashe wani matashine jibgege
bakikkirin mai jajayen idanu.
Koda acikin dodanni na tabbata baza akirashi mai
kyawuba
Ya yaye fuskarsa yazuwa abinda yake murmushine,
nikuma aganina abinda yayi yafi kama da hammar jaki
“Yan mata shigo na rage miki hanya mana”
Yafada awta muryarsa mai kama da kukan balamar
tunkiya, na kau dakai daga kallonsa domin tsoratani yake
Akuma lokaci guda nakecew
@mr:- Shuraih 99%
“Jeka abinka na gode”
Sai ya leko da kansa waje wanda ke tsugune akan
wuyansa mai guru guru
Kamar gurun diro.yaci gaba da dubana da idanunsa
wanda suke zurma zurma kamar ramin tanda ,wayanda
suka sa war ga jejen hancinsa atsakiya.
Yaci gaba da magana da bakinsa irin na kada .
“Don Allah ‘yan mata kishigo mana”
Nafara matsawa
“Nagode nace dakai”
Ya biyoni yaci gaba da nacinsa. Ana hakane mota tazo
natare na shiga.
Mummunar mutumin yabini da kallo.har muka bace
masa bai motsaba , akayi tafiya har akazo inda zan sauka
nabiya kudi dana fioto.
Nakama hanya zuwa gida bayan na tako kofat gidanmu
sai naji horn din mota.
Ina waiwayawa sai naga katon mutuminnanne
“Zan dawo da daddare”
Yafada cikin daga murya kamar kwamandan sojan daya
ke bada umarni.
Bancemasa komai ba nashige gida,
Banma sake yin tinaninshi ba da daddare kuwa sai gashi
an aiko.
“Wai farida tazo inji wanda sukayi alkawari”
Na dade ina kokarin tuno waye wannan bantuna ba sai
daga baya mutuminnan yafado min a rai.
Babu shakka shine nayi tsaki na dubi dan aiken
“Kace mata waidon Allah yayi hakurin anyimata miji”
Yayi ta maido dan aiken nace masa kar ya sake shigowa.
Nama tsahi nasa sakata akofar gidanmu ganin haka sai
yatafi yayi ta zuwa gidanmu jefi jefi na ki fita har watrana
mahaifiyata tace min ya wajaba na fita banda zabi dole
hakan akayi.
Yayi ta suratansa bance masa komaiba
Sai da yagama hayaniyarsa. Wadda take bayani akancewa
wai yana kaunata ni kuwwa banga abin da zaisa na’auri
mutumin wanda yafi kama da naman daji koda kuwa
maza sun kare.
Wannan yasanya ni cewa dashi
“A gaskiya karatu nake kuma bana zaton zanyi aure sai
sama da shekaru goma”
“Indon wannanne zanyi jiranki”
Raina yabaci yanda mutumin ke kokarin likemin tamkar
kaska
“Kai kaga kaje kawai kanemi wata “
“Kece kikayi min”
Yaci gaba dafada nayi tsaki sannan nayi tahowata gida.
Washe gari yasake dawowa naki fita.
Wata washe garin sai yatareni an taso daga makaranta
yafara yimin shirme.
Nikuma kiyayyar danakeyimasa takai intaha.
Wannan yasa na kalleshi afusace
“Mallam bari infada ma gaskiyama ni dai bana kaunarka
bakuma zan kaunaceka ba , zai fima sauki kaje kanemi
daidai da kai”
Ya fashe dawata irin dariya wadda take bada amo tamkar
ana tuttule ruwa daga jarka.
Yadade yanayi har ya tsoratani ,tamkar kuma dauke
wutan nepa sai yayi shiru gaba daya.
Nan danan fuskarsa takara muni sakamakon bata rai
dayayi.
“Yarinya kinyi shirme kintafka babban kuskuren
dayakamata aganar dake”
Ya nunani da dan yatsansa mai kama da busasshen itace,
Yayi kasa kasa da murya.
“Babu duka babu zagi saidai zaki mutu babu miji”
Raina ta baci na watsa masa kasa
“Aniyarka tabika saidai kai kamutu babu mata “
Yayimin wani kallo sannan yahau motarsa yatafi.
Da ganan muka rabu da mummunan mutumin.
Baisake zuwa gidanmu bako kuma ya tareni.
Ni kuwa gani da farinjini.
Aka rinka zuwa wajena naki fita don saboda ina ganin
hanani karatu za’ayi. Don babu abinda irin da daddare
narinka nazari , ahankali na.
@mr:-shuraih 99%
Tobe conti…….
Tobe cont……
@mr:- Shuraih 99%

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.