Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

TARAR ARADU littafi na daya page 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 3
Adai dai junnction din bariki yellow fifi ya tsaida mu.
Raina yabaci domin kuwa shine abin dana tsana
sakamakon rashin wadataccen burki,nayi iya yina domin
ya tsaya amma ina ,har nakaiwa yellow fifan sura .yayi
tsalle gefe guda .
Da kyar babur din ya tsaya bayan daya tungudi ginin
express, na juyo domin bawa yallaban hakuri, sai naga
ashe bai dauka da zafiba ,daomin ma dan unguwar ne.
Ba’ajima ba akabamu hannu nafara kokarin sa giya ina
takawa da kafa da kyar na samu ta shiga,
Wata rana ma kin shiga takeyi sai nagaji da shan zagi da
horn daga masu ababen hawa .
Kai har akwai kwandastan daya taba rankwashina wai
tare musu hanya .
Haka naci gaba da taifya rakakai raka kai kamar wanda
yake tafiya akan jaki, sauda yawa mai keke yakan wuceni
tinma ba idan na hadu da sabon jini ba.
Aje ba’ajeba sai gani a goron dutse na dudduba hakika
farida tayi mantuwa wajen kwatantamin gidansu.
Domin kuwa gidan daya kamata yazama nasun sam
banasu bane ba.
Saboda yadda naga tsarin gidan ko yar wanke wankensu
tafi karfun tayi koyarwa amakaranta.
Sai nafara tunanin yadda ya amata nayi daga karshe na
yanke shawarar in sami yaro na tambayeshi.
Haka kuwa akayi ,
Nayafito wani yaro
“Dan Allah zo mana kanina”
“Gani”
Yafada okacin daya iso gareni
“Don Allah kasan wata farida malamar makaranta”
Ya gyada kai lokacin daya ke nuna min
kerarren gidan
@mr:-shuraih 99%
“Ga gidan sunan”
Nacika da mamaki badon ita tace nazo ba da juyawa
zanyi domin kuwa nakaraya lallai farida tafi karfina .
Wata kila tayimin hakanne domin innaga gidansu sai in
hankalta.
Har zan juya sai natuna yakamata tasan nazo don
kartakamni da laifin saba Alkawari.
Na dubi yaron
“Don Allah jeka ka kirawomin ita”
Ya zura min ido kamar maisan yafada min wani abu, da
na dauka bazashi ba
Sai naga ya kada kai yace
“Amma dai”
Sai yatafi nabi yaron da kallo shin me hakan yake nufine?
Kokuwa shima yagane cika kainane?
Bai jima ba sai gashi yafito tana biye dashi tana biye dashi
abaya fuskarta cike da murmushi.
Ta tsaya abakin kofa , naga ashe farida kyawunta ya wuce
yadda nake gani amakaranta, yaron yazo wucewa kusa
dani
“Mallam Allah yaji kanka”
Yafada yakuma zura aguje bansa abinda yake nufiba .
Na kafe babur dina na kuma nufi wajenta
“Sannu da zuwa umar”
Tace dani idanunta akaina na amsa da
“Yauwa”
“Bismillah”
Tafada sa’arda take juyawa na bita abaya ta cikin soron
wanda aka shimfideshi da tayil mai kayatarwa ,
Araina ina ta sake saken abin daysa farida koyarwa.
Shin sha’awar koyarwar take ko kuma me ?.
Nidai nasan ba’ace dan tasami kudiba.
Banyi aune ba sai na ganni atsakiyar gidan aifa sai na ne
mi kidimewa saboda tsabon tsari da kayatarwa.
Ta nufi wani daki dani tasa hannu ta tura kyauren na
gilashi,
Ta tura kai ciki sa’arda ta kecemin shigo,
Nasa kafata nayi mamaki danaji sanyi ya dokoni alhali
lokacin zafine, sai na tuna A.C babu shakka itace aka
kunna ,
Na ratsa ta wani kilishi daya mamaye ilahirin dakin da a
gidan nake to da babu ruwana da katifa kansa kawai zan
rinka zuwa ina yin baccina.
Na dubi wasu maka makan kujerun dasuka mamaye
dakin tai min nuni da daya
“Zauna umar”
Na juya nazauna sai naji nayi kasa zan nutse ,nan nafra
zargin farida da laifin zaunar dani a bulalliyar kujera –
kome yasa tayi min haka?
Kawai sai naji nadakata nan nagane ahe ba bulewa tayiba
duk laushin soso ne.
Na jinjina kai lallai masu mura suke da tari.
Ta nufi kofa loakcin da takecewa
“Ina zuwa”
Bata dadeba ta dawo rike da farantin silverm
@mr:-shuraih 99%
Ta ajiyeshi akan wani karamin table sai naga kofa tabude
wata matace ta leko.
Ita da farida tamkar an tsaga kara.
Sai nagane mahaifiyartane na sauka har kasa na gaidata
tayimin kyakkywan maraba, sannan tafita na dubi farida
“Mai yasa baki kirani naje nagaishta acan ba sai ki
wahalar da’ita kisa tazo nan”
Ta waiwayo gareni cike da murmushi
“Lallai bakasan momi ba umar, wani irin haline da’ita da
kayi wahala dominta gwara ita ta wahalar da kanta
yanzuma babu yadda banyiba akan tabari zamuzo ku
gaisa tace a’a zan wahalar dakai”
Nayi murumushi gami da fadin
“Allah sarki”
Na gane mahaifyar farida irin mutanenane masu saukin
kai,ta zauna akan kujerar dake kusa da tawa bayan ta
gama bude tan garayen,
Dan kalin turawane wanda akahadashi da kwai aka soya
sai kuma wani hadadden kosan doya.
Ta tsiya ya ruwan tatacciyar abarba akofuna sannan ta
dubeni sa’arda ta ajiyemini cokali mai yatsu.
“Bismillah umar”
Muka fara gabatarwa harzuwa lokacin danaga ya kamata
na dakata sannan na kora ruwar abarbar nayiwa Allah
godiya.
Ta kawar da kayan gefe sannan ta fuskanceni
“To umar naga kana nema kadamu akan rashin baka
amsar tambayarka ,to dayardar Allah ayanzunnan zan
warwaremaka zare da abawa”
Tacigaba
“Ni da ka ganni yar wani hamashakin mai ar zikice mai
suna. Alh Hashim.jigon dan kasuwane maiyin harkokinsa
akasashen turai,kuma nan dakake gani dayane daga jerin
gidajensa guda goma,kuma shine mafi kankanta dakuma
muni”
Nakame baki jin abinda take fada
“Kwarai kuwa”
Ta tabbatar mini
“Yana da gidaje a Kaduna ,legas,Abuja kai harma da
birnin london”
Zan cigaba
@mr:-shuraih 99%

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.