Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

TARAR ARADU littafi na daya page 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tarar Aradu
Littafi na daya
Page 2
Written by: Shuraih 99%
“Yau narigaki zuwa “
Nace da ita tadan kwatar da kanta
“Nadan ragewa mummy aikine saboda batajin dadi”
Ashsha Allah ya sauwake”
Nadan gyara tsayuwata “don Allah farida idan an tashi
tara ina son magana dake’
Ta kalleni da fararen idanunta sa’ar da take cewa
“Lafya dai ko umar”
Na kauda kaina domin bana jurewa kuramata ido saboda
wani kwarjini da take dashi.
“Lafya kalau akan dai maganar nan ne”
Ta sun kuyuyar da kanta kas daga bisani ta dago
“To Allah ya kaimu”
Muka juya muka tafi.
@mr:-Shuraih 99%
Tunda farida tafara aiki amakarantarnan Allah yasanya
min tsabar kaunarta , nayi kokari in yakice amma ina.
Abin yaki yiwuwa .
Wannan yasa nafara yi mata isharori amma tayi biris
kmar bta gane ba , ga misali nasha sai mata sabulai da
mayuka .
Amma sai dai tayi godiya ta kuma bini da Addu’ar Allah
yabar mutunci.
Wannan yasa nafito fili na shai da mata amma sai tace na
saurara zata tun tubeni .
Kuma shiru kakeji haryanzu taki tuntubata .
Dana tina mata saita kama noke-noke shine yau nayi
kunar bakin wake domin nasan wacce akeciki.
Ana tashi tara na nemi karkashin wata bishiya na hakimce
can jimawa sai ga farida tana isowa
“Mai yafaru ne umar?”
Ta tambayeni bayan data zauna ,nakara jingina sosai
ajikin kujerar danake kai.
Sannan na dubeta na fara dacewa
“Wai dan Allah farida mai yasa har yanzu kika ki bani
cikakkiyar amsa ?
Nidai idan kina ganin babu dama gwanda ki gayamun
insan yanda nayi.mai makon ki kyaleni kullum ina
azabtuwa da tsabar sonki, kuma ina hada ki da Allah ki
shaudamin hakikanin gaskiya “
Na dade ina sauraronta taki tace uffan .sai kawai ta
tokare habarta da hannu,
Babu tsammani kuma sai naga tafara kwalla .
Hakan ya rikitani ,cikin rudewa na fara cewa
“Maganata rai ya bata miki”
Don Allah kiyi hhakuri”
Batace komai ba taci gba da kukanta kawai
“Don Allah farida kiyi hakuri bazan sake tambayarkiba”
Ta girgiza kai lokacin da take share hawaye “umar ba
tambayr kabane ta bata min rai illa iyala wani al’amari
dabam , zan amsamaka tambayarka umar,amma saidai
in antashi kasameni agida “
Nadubeta
“Inane gidanku
Tadanyi jim sannan tacigaba ‘goron dutse bayan gidan
isiyaka rabi’u gida mai kallon kudu, na biyu ahannun
dama”
*** *** ** ** ** ***
Dayin sallar la’asar na shiga wankka , nadade ina shekawa
domin kuwa awa guda na karar cur, nakarar da ruwa ya
kai jarka uku, ba’a batun sabulu wanda nakarar da fakiti
guda badon komaiba sai don na kara haske.
Aranan sabon man shafawa nasiyo saboda ji nayi nawa
nada yana wari, alhalin kuma dukranda nashafashi har
tambata ake wannan wane maine?.
Saoda tsabar kamshi, na bude kwaba nayi ta zaro kaya
ina ajiyewa gefe guda ,har nazo kan na cin yewar
,dukranda na sanyasu ka tabbatar zani muhimmiyar
ungwa ko kayataccen fati.
Nan da nan nafara jikasu da tirarena.
Na makala farin gilkashi.
Ban nufi ko’inaba sai gindin dressin mirror don duba
haduwar tawa,
Hakika nafito kamar yadda nayi tsammani, nakalli
takalmana cali-cali wayanda tuni na baiwa shushaina ya
wankeminsu harda karin kudi nayimasa domin yayi mani
wanki na musamman nan danan na zura kafata nafara
takawa cikin takama ,
Kai kace wani dokin dan sarki,
@mr shuraih 99%
Na kulle shagon nanufi cikin gida anan na sami matar
yayana tana kokarin dora girki.
“Kai umar ina zakne haka kaci kwalliya ?”
Nagoge fuskata da hankici
“Wallahi zani unguwne ,yaya kika ganni,nafito?”
Ta kalleni daga sama har kasa
“Wallahi ka fito”
Kaga yanda kake kyalli kamar sabon kwabo”
Wata dariya ta kwacemin .
“Toh madalla dama haka nakesopn ji”
“Zanyi miki karin kudin cefane tunda kin yaba “
Tayi shewa .
“To mai gida, godiya nake,ince dai ba kishiya zakayiminba
ko?”
Na duba agogona
“Ke dai wallahi kin cika tsoron kishiya kimin Addu’a Allah
yabada sa’a”
Ta kwantar da kai
“To Allah ya taimaka “
“Amin”
Nafito nabarta .
Raina yabaci yayinda na iso soro,baodn komaiba sai don
bata min lokacin da mashin zaiyi.
Na turashi har muka zo waje.
Nakafeshi nafara bugawa nayi tayi amma ina ko amsawa
bayayi kamar wanda na cika tankinsa da ruwa .
Yara kuwa sukazo suka yanyameni,kullum haka sukemin
in har nazo fita da yamma ,sukanyi ta dariya sa’arda nake
bugawa.
Wani lokaci nakanji kaman nasa duka amma sai na daure
na rabu dasu.
Har ina shirin hakura sai naji yafara amsawa.
Wannan yasa nacigaba banfi bugu ashirin ba kuwa
yatashi.
Yara suka kaure da shewa ye !yatashi yatashi!
Nan fa suka da baya yayinda suka ga dare,badon komai
ba saidon sun san in yayi wata zabura zai iya bi takan
yaro.
Raina yakara baci dana tuna yadda zanyi fama da giya
,amma cikin ikon Allah murdawata sau uku sai fada, na
murza totur sai tafiya ahaka na ringa tuki cikin hkima da
dabara.wai ance inkana da abin hawa dolene kazama
makaryaci saboda takurawar yan aro mai zuwa yau
dabam mai zuwa gobe dabam.
To nidai nakaryata domin kuwa babur dina saudaya wani
abokin aikina yataba aronsa da uzurin gaggawa ya
kamashi,daga ranar shima bai kara araba.
CABDI WANNAN BABUR KO WAHALA DA RAI
Tobe con……
By @mr:- Shuraih 99%

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.