TARAR ARADU littafi na daya page 1

 TARAR ARADU littafi na daya page 1
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 14 Aug, 2018
Upload Time 1:17 pm
Hits 339 Hits
Comment No Comments

Description

TARAR. ARADU
Littafina daya
Page 1
Written & post by shuraih 99%
Na yayi mo takarduna bayan na cika tumbina da
waina.nan da nan nafara angizo babur dina Vespa
zabuwa .zuciyata na mai dari darin dadewar da zan yi ina
bugu kafin ta tashi.
Bayan dana hada waya sakamakon gidan makullin
(ignition)da ya dade da lalacewa.
Abin mamaki yau bugu shabiyar kawai nayi ta tashi .anan
da nan wata kara ta cika wajan kamar an kunna injin
markade sabon washi, saudadama idan ina sabis acikin
gida in har na tasheta yara kanyi sallama .”Ga markade”.
Ni kaina duk sanda ta tashi nakan toshe kunnena .
Lokacin kwanciyar zafi yan unguwar mu har basa so nayo
dare .
Darana kuwa matan aure basa son wuce wata wai nakan
tayar masu rigimammun ‘yayansu daga barci,kuma na
kan hansu bin sallar jam’I.
Dama gababur babu gudu,kuma nakara kasheshi da kaya
.
Domin kuwa idan nabudema wajen adana kayayyakinsa ,
babu komai illa tulin fulogi wanda nikain nasan suna
ragemin gudu.
Amma inkaduba body ,mai motama sai yayi zaton zan iya
wuceshi har yagaza kamoni.
Nan da nan na dare sama mukafara kokoyi da giya na
dade ina shammatarta kafin tafada .
Aifa shigar giyar kedawuya na murdashi sai tyafiya ,kar
kaso kaga yanda nake doro ina kwambarewa .
Kullum nahau haka nake fankama naketakama kamar
sarki akan doki.
Idan na raina majalisama ko sallama banayi ahaka naita
wuta har makarantar dangiwa commercial secondry
school.
Inda anan nake koyarwa amatsayin malamin English.
Da malam sule mai gadi muka fara gaisawa “har an fito”
“Allah yayi”
Nabashi amsa .
Nakafe babur dina a inda aka tanada domin yin fakin.
@mr:-shuraih 99%
Na nufi ofishin principle. Ko ba’a fada maka sunansa ba
zaka iya ganewa da kanka.
Domin kuwa yafi dacewa da malam Abba .akwai kwazon
aiki akwai kuma mugun son kudi na gaisheshi muka
kuma taba yar hira wadda zolaya acikinta tafi yawa .
Da fitowata na nufi wani abokin aikina kabir sabi’u. Muka
caccake na dubeshi “naga sai kyalli kake kodai kanasan ka
angoncene ban saniba?”
Yayi dariya” kaifa tsiyarka kenan baka kyale mutum haka”
Muka zauna na shiga dube dube wani lokacin har nakan
mike tsaye “wai kai me kake dubawane”
Na dawo na zauna bayan na gaza hango abin danake
nema “don Allah bakaga shigowar farida ba ?”
Na tambayeshi . Ya tintsire da dariya . “Kai mallam tunda
farida tafara aiki anan naga sai wani kankajeri Kake kana
kara kwalliya ,kodai da watane akasa?”Nace babu komai ,
don mutum ya tambayi abokin aikinsasai yazama laifi”
Ya girgiza kai
“To me isa baka tambayar su hafiz?
Kosu ba abokan aikin kabane”?
Na gyara takarduna sa’arda nake cewa
“Kaga mungama hirar ne ban tambayekasuba”
“To shikenan tunda boye-boye kake ,amma indai kuka
shirya kanku kayi sa’ar mata UMAR”
Bancemasa komaiba ,duk dacewa maganar tasa ta
kayatar dani . Bada jimawa ba na hangota tana shigowa
tana rungume da jakar takardunta .
Mace ce mai matukar tsari da kyau tana da yawan kuya
da kulawa da Addini,kai ni tunda nakke ban taba ganin
kamartaba .
Na mike tsaye kabir yabini da kallo
“To mallam ka hangota zaka gujeni ko?”
Na harareshi
“Ai kaine kake yimin wulakanci,ba gara na tafi inda inda
za’a karramani ba ” ban tsaya wata wata ba nanufi inda
take da ganina ta fara murmushi ,
Murmushin da kullum in tayimin sai nadan rikice .
Na dubeta cikin sarkewar murya
“Ina kwana hajiya farida “
“Lafiya lau umar”
Tra amsa cikin daddar muryarta
To be conti……
Via:- mr:-shuraih 99%

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: