Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

RANA DA WATA littafi na daya 1 part G

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part G

“Yake zaitunal-abidina ,ina mai matukar godya a gareki a bisa wannan taimako da kika yi min , bazan taba mantawa da ke a agaba dayan tarihin rayuwata ba.
.
Kuma zan kasance tare da ke har izuwa lokacin da zan samu sauki na dada samun kwarin jikina sannan”
.
Zaitunal-abidina ta kasance ita kadaice zaune a wannan kasaitaccen gida gaba dayan iyayenta da duk danginta sun rasu,
Asalin zaitunal-abidina da mahaifanta yan asalin kasar zargayunu ne,
.
Yaki yaci kasar su aka kashe gaba dayan mutanen kasar,sai mahaifinta ne da mahaifiyarta da kuma ita a wannan lokacin tana karama bata iya sanin komai game da lamarin duniya
.
Tun daga wannan lokacin ne wargis ya kasance tare da zaitunal abidina har [shuraih 99% ke typingg
Tsawon shekara daya wanda wannan lokaci wargis ya wartsake garau, sai ya bukaci zaitunal-abidina da ta aure shi kasancewar ita kadaice yanzu tayi saura a gaba dayan danginsu
.
Haka kuwa wannan lamari ya kasance,wargis ya auri zaitunal-abidina, wanda a wannan lokacin wargis ya musulunta, sai da suka sake shafe shekaru biyu sannan wargis hankalinsa ya karkata ya zuwa tunanin mahaifinsa
.
Da dan uwansa Dawwara, shin ko a wane hali suke yanzu?,amsar daya kasa samu kenan a duk lokacin daya tuno da kasarsu zayyar,
.
Bisa dole, wargis ya bukaci zaitunal-abidina da suyi shiri suje kasarsa ta haihuwa domin yaga a wane hali mahaifinsa yake ciki da yan uwanda sa suke da babban abokinsa kuma dan uwansa suke
.
Shuraih usman inkiya 99% jagoran typing
.
Wata rana sarki dawwara yana zaune akan karagarsa ta mulki yana tafiyar da sha’anainsa yadda yaso,kwatsam! Sai ga wargis ya shigo a wannan fada koda ganinsa sai sarki dawwara yai saurin mikewa tsaye hankalinsa ya dugunzuma ,
.
Take jikinsa ya kama karkarwa wata zufa ta karyo masa. Amma sai ya wayance ya tari wargis yana mai nuna tsananin farin cikinsa game da dawowarsa a wannan lokaci da suke nemansa ruwa ajallo
.
Dukkanin mutanen gari babu wanda bai nuna farinciki da dawowarsa ba, sai ma aka balle da wata kwarya kwaryar liyafa ta murnar dawowar wargis gida a bisa jagorancin sarki dawwara,
.
Sai da aka share kwanaki hudu ana wannan liyafa ta karramawa, sannan aka lafa, kuma a wannan rana ne duk yan majalisar tsohon sarki suka hadu tare da cire sarki dawwara suka dora wargis kasancewar shine shuraih usman inkiya 99% dan sarki dakiru daya kamata ace ya gaji mahaifinsa
.
Daga cikin wadanda suka dage ala dole sai an cire sarki dawwara akwai wani matashi wanda suka dade tare da wargis wanda ake kira da Suna mudahir ibini muhutaru
.
Mudahir ya kasance masani ne sosai akan ilimim taurari, yana buga kasa yayi bincike akan kowane irin al’amari idan ya damu al’ummar kasarsu, kasancewar ya gaji mahaifinsa ne ta wannan fanni
.
Kuma dama tun kafin sarki dakiru ya mutu ya dade yana sanar da wargis cewa ya rike mudahir hannu biyu, kuma duk abinda ya sanar da shi yayi gaugawar amincewa da shi, sakamakon mahaifin mudahir ya rasa rayuwarsa.
.
Tun daga wannan lokacin wargis ya dada janyo mudahir ajikinsa yana mai tsananin kula da shi baya son wani abun da zai dameshi shuraih usman inkiya 99%
.
Mudahir shi ya zake akan lallai sai ancire dawwara daga sarki cikin dan kankanin lokaci haka, sannan ya bukaci sarki wargis da su kebe yana son su gana su biyu kawai. Mudahir ya dubi sarki wargis ya fara magana cikin nutsuwa yana mai cewa
.
“Ya sarki wargis, ka sani tunda nake da kai ban taba sanar da kai wani labari da zai tayar da hankalinka ba a gaba dayan tarayyarmu saboda haka nake so kayi nazari a kan abinda zan sanar dakai.
.
Dan uwanka dawwara yana da sa hannu wajen batanka na tsawon dogon lokaci, sannan yana da sa hannu cikin rasuwar mahaifinka sarki dakiru”
.
Yayin da sarki wargis yaji wannan batu , sai ya rikice ya dimauce,hankalinsa ya dugunzuma ba don mudahir ya kasance baya sa baki akan kowanne al’amari akasar ba, da to sai sarki wargis yace yayi masa karya a wannan shuraih usman inkiya shuraih 99% karon don haka sai sarki wargis ya tsananta bincike ya kuma gano lallai dawwara bashi da gaskiya , har ma sai da ya turke kansa
.
Al’amarin daya daurewa sarki wargis kai kenan , hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe , anan take ya tsinewa dawwara ya kuma fada masa cewa babu wata dangantaka da zata sake hada su har abada, amma ba zai taba daukar wani mataki akansa ba
.
Lokacin da dawwara ya isa gida sai ya tattara dukkanin kayansa da iyalinsa ya bar kasar ba tare da sanin kowa ba yana fitowa daga kasar zayyar , sai ya tarar da boka gayyar yana jiran fitowansa ,
.
Koda boka gayyar yaga dawwara awannan lokaci sai ya tunstire da dariya yana mai kyakyatawa, sannan ya dubi dawwara ya ce dashi shuraih usman inkiya 99%
“Mugu shi ya san makwantar mugu”
Nan take boka gayyar ya kurma wani uban ihu, al’amarin daya matukar girgiza dawwara kenan ya dubi boka gayyar ya ce dahsi
.
“Ya boka gayyar shin ina dalilin wannan ihu naka da akayi a wannan lokaci?” Sa’adda boka gayyar yaji wannan tambaya daga bakin dawwara sai ya dube shi yace da shi.
.
“Hakika ya kai dawwara, ka sani akwai wata hanya ita kadaice zaka bi wannan bukata taka zata biya , kuma wannan hanya ta kasance mai tsananin wahalar gaske wadda zaka iya rasa rayuwarka ma akokarin ganin ka mallaki kasar zayyar ka zama sarki
.
Koda boka gayyar yazo nan a zancen sa sai dawwara yace da shi
“Wacce hanya ce wannan , shuraih usman inkiya 99% maza ka fada min ita na rantse da iyayena ba zan gaza ba wajen yin ko menene ake bukata ba”
Boka gayyar ya girgiza kai yace dahsi
.
“Muddin kana so ka zama kasaitaccem sarki da babu kamarsa a wannan nahiya , sai kaje can kogon darul yamzin dake acan karshen birnin sin,ka dauko wani hatsabibin zoben zinari da ke ajiye a dakin baccin dodanniya hujarnun-majnun

Koda dawwara yaji wannan batu sai ya kidime ,hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe, sai kawai ya dubi boka gayyar yace da shi
.
“Koda na tsaya ban amince da zuwa dauko wannan zoben ba, nasan halaka zanyiabanza saboda bakin ciki da takaicin abinda sarki wargis yai min, yakai boka gayyar maza ka ka tsumani da tsumi irin naku na manyan bokaye,
.
Na rantse da iyayena sai naje kogon darul yamzin na dauko wannan zobe dyk rintsi da tsanani shuraih usman inkiya 99%

HATSABIBIN ZOBEN ZINARI

A can saman wani katon dutse dake bayan kasar yamfisu akwai wani katon gida akan wannan dutse, tun sama da shekaru ashirin wannan gida yana nan kamar yadda yake a yanzu
.
Boka daulakaki shi ya gina wannan gida da karfin tsafinsa, yana zaune ne shi kadai, amma yana da mata da wani dansamai suna ihimuzussam ma yaro ne dan shekara goma da haihuwa
.
Babban dalilin daya sa boka daulakaki ya baro cikin kasar yamzin ya dawo kan wannan dutse shi ne .
Akwai wata rana da sarki badalaki yasa boka daulakaki yayi amfani da karfin bokancinsa ya tara masa wata dukiya mai tsananin yawa,
.
Shi kuwa boka daulakaki yaya nunar wa sarki cewar hakan ba zata taba yiwuwa ba, sai kuwa sa’insa ta shuraih Usman inkiya 99% kuduru a tsakaninsu har daga karshe sarki badalaki ya kori boka daulakaki daga cikin kasarsa
.
Ya kuma yi masa gargadi akan cewa bashi ba sake shigo masa kasa muddin bazai biya masa wannan bukata tasa ba, haka kuwa akayi, boka daulakaki yabar kasar yamzin , amma kafin yabar kasar ya dawo asaman wannan dutse daya gida wannan gida
.
Ya nemi alfarma a wurin sarki badalaki akan yabar iyalinsa suci gaba da rayuwa acikin kasarsa kasancewar shi kadai ne ya aikata masa wannan laifi, haka kuwa akayi
.
Bayan wasu yan shekaru sai sarki badalaki ya tsokano wani babban sarki mai girman sha’ani, wanda ake kira da suna sarki dawur ibni zaujainun.
.
Sarki dawur ya kasance tsara a cikin sarakunan duniya ,babu wanda bai san irin tsananin zalunci da rashin imaninsa ba , yana da runduna mai tsananin yawa masu zafin shuraih Usman inkiya shuraih 99% zafin nama da juriya a fagen yaki, sannan yana da eundunar bokaye wadanda suka shahara a duniya, atarihinsa ma ance duk inda yaje labarin wani hatsabibin boka daya gagara
Sai yaje wurinsa yabashi dukiya mai tarin yawa yazo ya zauna tare da shi.
.
Ran sarki dawur ya matukar baci ganin cewa yafi karfin sarki badalaki a kowanne fanni, don haka sai ya taho da rundunar yakinsa ya sauka a bayan kasar yamzin suka kacame da wani azababben yaki mai matukar tayar da hankali.
.
Wannan kazamin yaki da aka buga tsakanin sarki dawur da sarki badalaki sai ya kasance darki badalaki yayi dana sanin tsokano sarki dawur dayayi, akarshe sai da aka kashe shi da gaba dayan dakarunsa.
.
A karshe ma sai da sarki dawur ya shiga har kasar yamzin yana ta kashe mata da ka nanan yara sai ya zamo babu sauran mai numfashi a kasar face Shuraih Usman inkiya 99% ihimuzassam daya boye a wanin sako da basu ganshi ba.
.
Alokacin da wannan yaki ya kaure boka daulakaki baya nan yayi wata gagarumar tafiya lokacin daya dawoo ya tarar da cewa an rusa kasar yamzin kuma an kashe matarsa sai dan ne yayi saura , sai ransa ya yi matukar baci,
.
Take ya shirya ya tafi ga sarki dawur suka gwabza yaki mai tsanani, inda a karshe da kyar ya kwaci kansa, bayan kwanaki uku sai ya mutu agaban dansa ihimuzussam
.
Amma kafin ya mutu sai daya damkawa wa dansa jakar bokancinsa ya umarcesa daya gudu yabar kasar
Haka kuwa akayi , bayan shekaru shida ihumuzussam ya wanzu yana mai karanta duk wata takarda daya gani a cikin jakar bokancin mahaifinsa,
.
Daya kalleta sau daya sai kawai yaji ya hardace gaba dayanta, sannu a hankali, sai ihimuzzassam , ya zamo shuraih Usman inkiya 99% kasurgumin matsafi mai girman sha’anin da babu kamarsa a gaba dayan nahiyarsu
.
Da ihumuzussam ya fahimci ya samu wannan matsayi da daukak, sai ya kulla gaba da duk wani mahulukin dake zaluntar na kasa dashi,
Yana mai matukar jin haushi, da tafiya tayi tafiya sai ihimuzussum ya rika bi kasa kasa yana yakar azzalumai yahar sai da ya zamo cewa duk bokaye da matsafa suna boye kansu da fadar cewa su ba bokaye bane, izan su kayi gaba da gaba da ihumuzussam, shi kuwa sai yai wani tsafi duk inda ma’abocin tsafi yake kawai sai dai yaga ihumuzussam a gabansa, sannan ya halaka shi
.
Har ta kai babu wani mai ilimin bokanci da yai saura sai shi kawai a duniya
.
Tun daga ranar da ihimuzussam ya gama da bokaye da manyan sarakuna da takurawa na kasa da su, sai gaba dayan Shuraih Usman inkiya 99% mutane suka samu saukin zaluncin dara shin imani da ake nuna masu
.
Har ya zuwa lokacin da ihimuzzusam tsufa ya kamashi ya kasance baya iya zaga duniya domin ya kai agaji ga marasa karfi da ake zalunta
.
Saboda haka ne sai ihimuzzassum ya tattara gaba daya duk ilimin bokancinsa ya sana’anta wannan hatsabibin zobe na zinari yakai shi kogon darul yamzin anda ya riga ya san cewar koda bayan ransa babu wanda ya isa ya tunkari kogon bare yayi yunkurin mallakarsa komai hatsabibancinsa da shahararsa a duniya
.
Lokacin ihimuzussam ya mutu sai gaba dayan sarakunan duniya suka rika kokarin ganin sun mallake shi ya zama nasu saboda sanin cewa, duk wanda yake rike da wannan zoben dukkan mutane da aljanun duniya zasu zamo a karkashin ikonsa sai yadda yace za’yi
.
Hakika da yawa daga manyan sarakuna sun salwanta shuraih Usman inkiya 99% an gwabza kazamin yaki milyoyin mutane sun rasa rayuwarsu akan wannan hatsabibin zobe na zinari
.
Lokacin da zabbabu yazo nan a zancensa ,sai ya dubi huzainu yace da shi.
“Ya huzainu ka sani cewa kafin dawwara ya tafin yayi shirin zuwa kogon darul yamzin daukoo wannan zobe, sai da yahada wani tuggun da yayi sanadiyar rasa rayuwar mahaifina.
.
Wanda a wannan lokacin ina da shekaru goma sha biyar saboda haka sai aka danka min sarauta na ci gaba da kula da kasarmu har izuwa wannan lokaci da boka gayyar ya aiko da wayannan dakaru suka sato ni da niyyar su halaka ni,
.
Ka sani yakai huzainu a dai dai wannan lokacin dawwara yana kan hanyarsa ta zuwa kogon darul yamzin domin ya samu sa’ar dauko hatsabibin zoben zinari a kokarinsa na ya halaka duk wanda yake sarauta a kasar zayyar
.
Shuraih usman inkiya 99%. Koda zabbabu yazo nan a zancensa, sai gaba dayan kasar wurin ta dauki raurawa ta girgiza kamar zata kife, daga bisani kuma sai kasa taci gana da darewa wata guguwa mai tsananin karfin gaske ta ci daukar abu marar nauyi tana mai yin wurgi da dashi,
.
Bayan kamar kimanin dakika hamsin, sai komai ya daidaita , kawai sai ganin zuhaisa sukayi agabansu.
Zuhaisa ta kyalkyale da dariya tace da huzainu
.
“Hakika yakai huzainu kasani gani nazo a gareka cikin yanayi na ba zato da shammata. Kamar yadda na sha fada maka a baya, bani da wani makiyi a duniyan nan daya wuce kai, na tsani duk wani cigaban rayuwarka, kuma na dade da cin alwashin ganin ka daina numfashi.
.
Na zamo ni ce nayi sanadiyar mutuwarka, saboda haka ne nazo a ………….
Toh jama’a sai fa anyi hakuri don fallen littafin na karke ya balle
.
Anan muka kawo karshen littafin RANA da WATA na daya sai kunjini a littafi na Biyu nan da kwana biyu
Marubucin yace
.
SHIN TSOHUWA SHAFHILA ZATA SAMU NASAR ISA KOGON DARUL YAMZIN KUWA?
.
A TSAKANIN ZUHAISA DA HUZAINU SHIN WAYE ZAI SAMU NASARAR KASHE DAN UWANSA
.
SHIN DAWWAR ZAI SAMU NASARAR DAUKO ZOBEN ZINARI A KOGON DARUL YAMZIN KUWA
.
INA LABARIN DAJIN MAYUN DA SU TSOHUWA SHAFHILA sUKA ShIGA?
.
SHIN ZASU TSIRA DA RANSU KUWA??
.
Domin jin karshen wannan littafi sai mu hadu a littafi na biyu,
Tare dani Shuraih Usman
Inkiya Shuraih 99%
Jagoran Typing
Mamallakin shafin hausaebooks
Da keffians News Teller
.
Kar dai ku sha’afa zaku iya download na wannan littafi zuwa kan wayoyinku ta hanyar ziyartarmu a shafinmu na yanar gizo gizo Hausaebooks
.
Sai kunzo

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.