Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

RANA DA WATA littafi na daya 1 part F

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part F

Bisa ga rashi sa’a sai huzainu ya taka gawar wani sadauki da aka kashe
Ya zame ya subuce tare da faduwa a kas takobinsa ta subuce daga hannunsa
.
Koda ganin haka sai jarumin yayi dariya irinta mugunta da zalunci, sai kawai ya daka wani uban tsalle da niyyar ya taushe huzainu yasa takobin dake hannunsa ya sare masa kai ya halaka shi
.
Huzainu yayi saurin yin alkafura da barin wannan waje , aikuwa sai wannan jarumin ya fada akan wannan gawa mashin da yakashe sadaukin , shima yayi ajalinsa
.
Koda sauran mayakan da suka rage suka ga huzainu ya samu nasarar kashe shugabansu sai kowannensu ya ranta ana kare
.
Suka tsere faruwar wannan al’amari ke da wuya sai waannan saurayi ya rugo a guke ya rungume huzainu yana mai masa jinjiana da bisa ga wannan nasara da ya samu . Ya kuma yi masa godiya bisa ga taimaka masa da yayi huzainu ya dubi saurayin yace da shi
.
[Ni dinne dai shuraih 99% ke cewa daku
“Yakai wannnan saurayi maza ka sanar dani labarinka da abinda yasa wadannan mayaka suka taru akanka da niyyar suyi maka kwab daya su halaka ka”
.
Koda wannan saurayi yaji wannan batu sai ya fara magana yana mai cewa .
.
“Su nana zabbabu ibini wargis, ni dan asalin kasar zayyar ne na gaji sarauta a wajen mahaifina sarki wargis . Wadannan mayaka da ka gani dawwara da boka gayyar ne suka turo su , suka sato ni bisa yaudara suka kawo ni wannan waje da nniyyar su halakani
.
Tsananin gaba da kiyayyar dake tsakani na da dawwara ya samo asaline tun mahaifina sarki wargis suna kanana shi da dawwara,
.
Wanda a wannan lokacin kakana sarki dakiru shine sarki a kasar zayyar , dawwara ya kasance dan riko ne ga sarki dakiru ya rikeshi amana yadda har da yawa daga mutanen kasar sun dauka cewa sarki dakiru shi ya haifeshi saboda tsananin soyayyar da ya nuna masa, ko wargis baya nuna mawa
.
Shuraih 99% ke cewa
Wata rana mahaifina wargis wata gagarumar tafiya ta kamashi , yai shirinsa tsaf ya gabata a gaban sarki dakiru bayan yayi gaisuwa ya fara magana da cewa
.
“Ya abbana ina mai neman izni a gareka daka amince min na ziyarci babban aminina jarumi abasul-saidanu da zaune acan kasar turkiyya , kasancewar ya dade yana zuwa har wannan kasa tamu yana ziyara ta,
.
Amma ni ko saau daya ban taba zuwa naga mahaifansa ba. Akan wannan daliline nake neman izininka ya mahaifina”
.
Koda sarki dakiru yaji wannan batu sai yayi murmushi yace da shi.
.
Kuna tare ne dai da shuraih 99%
“Maza ka shirya nayi maka izni kaje ka gano shi, har ma kace ina gaida shi.
Sannan kaje bital malika debi dukiya mai tsananin yawan gaske wanda zaya isheka sa’annan ka tafi da dakaru dari biyu suyi maka rakiya a wannan tafiya taka
.
Amma kuma shin ba da danuwanka dawwara zakuyi wannan tafiya ba ne?”
.
Yayin da wargis yaji wannan batu sai ya sake dukawa a gaban sarki yana cewa
.
“Ka sani ya kai abbana, lokacin dana tuntubi dawwara daa zancen tafiyar nan sai ya ke shaidamin cewa , bashi da lafiya baza ya iya raka ni ba a wannan tafiya tawa,
.
Sai dai yana maiyimani fatan alkhairi har naje na dawo
“Koda sarki dakiru yaji haka sai ya mike tsaye batare daya shirya ba jikinsa ya dauki kakkarwa gashin jikinsa ya mimmike ya dubi wargis yace dashi.
.
Shuraih 99% ke typing
.
“Kasan da cewa dawwara bashi da lafiya kayi shiru baka sanar dani ba tun farko?”
Batare da ya saurari komai daga bakin wargis ba ya fita daga fadar ya shige cikin gidan sarauta,
.
Da shigarsa bai zame ko’ina ba sai dakin dawwara ya tarar dashi kwance magashiyyan rai a hannun Allah
.
Tun daga wannan rana ne sarki dakiru ya kasnace yana makale da dawwara har ya kwashe kwanaki arba’in yana jiyyarsa.
.
Lokacin da aka sake kwashe wata daya ba tare da wargis ya dawo gida ba al’amarin da ya dami sarki da dawwara da duk mutanen kasar kenan
.
Sarki dakiru ya ya tashi yan aike suka je har kasar turkiyya suka samu jarumi abbasul-saidanu suka sanar dashi abunda yake faruwa. Jarumi abasul saidanu ya tabbatar musu da cear Wargis fa baizo wannan kasar ba.
.
Lokacin da wannan sako yazo kunnen sarki dakiru [shuraih 99% nedai har wayau]sai hankalinsa ya dada dugunzuma fiye da farko , sai kawai ya baza yan aike a dukkanin wannan nahiya tasu da sauran kasashen dake nesa dasu domin samo wani labari game da dansa wargis
.
Bayan watanni uku sai dakiru ya kwanta ciwon ajali , a haka sai da sake share kwanaki tara ciwo na cinsa , sannan ya mutu
.
Al’amarin daya jefa dawwara cikin tashin hankali da matsananciyar damuwa kenan, har ma akwai lokacin da dawwara yake yin ihu da kururuwa yana mai cewa “na bani na lalace , ayau na rasa gatana, shi kenan nayi sallama da duk wani jin dadi a duniya kaicona!!!”
.
Daga nan sai ya kama buga kansa da bango yana mai yin ihu da iface iface
.
Bayan mutuwar sarki dakiru sai manyan yan majalisar sarki dakiru suka yanke shawarar nada dawwara daya zamo sarki a garesu
.[Karfa ku manta kuna tare ne da shuraih 99%]
Tun da waragis haryanzu bai dawo gida ba, kuma sunga dawwara shi yafi kusanci da sarki tunda har a wani lokaci yafi nuna soyayyarsa akansa fiye da dansa waragis,
.
Haka kuwa akayi aka nada dawwara ya zama sarkin kasar zayyar
.
Kashe gari tunda safe fada ta cika ana ta fadanci sai ga wani mutum ya shigo fadar ya dika gaban sarki ya kwashi gaisuwa, sannan ya fara magana yana mai cewa
“Yakai sarki dawwara ina mai neman izni damu kebe ina da magana”
Nan take wani dokari ya daka masa tsawa da niyyar ya dakatar da shi bisa ga aniyarsa
.
Sai sarki dawwara ya umarci wannan mutum da su kebe din
Bayan sarki dawwara da wannan mutum sun koma inda babu wanda zai jiyo abinda zasu tattauna akai sai mutumin ya bushe [har ila yanzu dai nine nan Shuraih 99%] da dariya ya dade yanayi kamar bazai daina ba.
.
Sai dayayi mai isarsa sannan yayi tsagaita har ya dubi sarki dawwara yace dashi
“Hakika yakai sarki dawwara bukatarka ta biya , saura tawa bukatar ya rage, shin yanzu menene abunyi?”
Lokacin da sarki dawwara yaji wannan batu sai ya dubi mutumin yace da shi
“Ya boka gayyar , ka sani na riga na tanadar maka duk dukiyar da kake bukata, sannan zan nada ka daka zamo wazirina ” koda boka gayyar yaji wannan batu sai ya sake kyalkyalewa da dariya yana mai kyakyatawa har zuwa wani lokaci mai dan tsawo.
.
Al’amarin wargis da dakarun dake tare dashi kuwa lokacin da suka yi nisa sosai suna tafiya ba dare ba rana kwatsam sai ga wata guguwa mai tsananin karfin gaske ta mamayesu,
.
Bayan [nidinn e dai Shuraih Usman inkiya shuraih 99%] wannan guguwa ta wuce sai kuwa wargis ya duba sama ko kasa babu abokan tafiyarsa, wannan al’amari ya daure masa kai zuwa can kuma sai boka gayyay ya bayyana kafin wargis ya zare takobi kawai sai boka gayyar ya huro masa wani farin haske bayyana tare da shiggewa a cikin hancin wargis.
.
Take sai wargis ya some sai boka gayyar ya bace yana mai kyakyata dariya
.
Daga nan wargis bai kara sanin halin da yake ciki ba , sai bayan shudewar dakika dari da hamsin , sai kawai ya samu kansa a wani katon gida na alfarma, yayi niyar tashi zaune ,sai yaji ya kasa koda motsa hannunsa,
.
Al’amarin daya sa hankalinsa ya dugunzuma kenan sai ya kasance yana mai sauraron abinda zai faru da shi
.
Bayan kimanin shudewar sa’a daya sai wargis ya rika jiyo wani kamshi yana dada kusantowa inda yake zuwa [shuraih usman A K A 99%] wani dan gajeren lokaci sai wata kyakkyawar budurwa ta bayyana gareshi cikin shiga ta kaya na alfarma, bayan ta samu wuri ta zauna sai ta dubeshi da murmushi sannan tace da shi
.
“Su nana zaitunal-abidina ka sani yakai wannan kyakkywar saurayi na tsintoka ne a cikin daji kana a halin galabita kuma ga dukkan alamu kana are da mutane ma’abota tsafi,
.
Wadanda sune suka yi maka mugun tanadi a kokarinsu na son su halaka ka , bisa ga kiyayewar ubangiji sai gani na bayyana a lokacin da kake neman taimako ta kowacce hanya .
Yakai wannan saurayi ka godewa Allah kasancewar yanzu ka dan fara samun sauki kana da dada warwarewa”
.
Yayin da wannan zaitunal- abidina tazo nan a zancenta sai wargis yaji wannan batu sai yai karfin halin ya fara magana yana mai cewa
.
Toh friends anan
Zan tsaya sai mun hadu bayan kwana biyu
Dafatan kuna jin dadin littafin
.
Shuraih Usman
Inkiya 99% mamallakin shafin hausaebooks da Keffians News Teller

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.