Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

RANA DA WATA littafi na daya 1 part E

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part E

Koda ahakamul bainun yazo nan a zancensa sai ya nuna zuhaisa da sandar da ke hannunsa wani haske mai kamar walkiya ya fito da matsanancin gudu kamar an harba shi akwari da baka
.
Zuhaisa ta zare garkuwarta daga damararta ta yaki ta kare , amma saboda karfin tsafi ahakamu-bainun sai da zuhaisa ta gwaru da bangon dake kogon take kanta ya fashe har ta shafa ta ji jini
.
Al’amarin daya dugunzuma hankalinta kenan , kawai sai ta zare takobi ta tunkari boka ahakamul-bainun a cikin tsananin bacin rai da kunar zuciya , tana zuwa kusa dashi ta daka wani uban tsalle tare da kai masa wani gawurtaccen sara a saitin dokin wuyansa da niyyar ta sare masa kai ta halaka shi.
.
Lokacin da ta sare shi sai taji tamkar dutse ta sara ,amma saboda karfin saran sai da yayi baya taga-taga amma ya turje bai kai kasaba .
.
Ita kuwa zuhaisa sai da takobinta ta subuce ta fadi can nesa da ita boka ahakamul bainun ya bushe da dariya ya dade yana yi kamar bazai daina ba har tsawon dakika sittin sannan ya daure fuska kamar bai aba fara’a ba .
Take ya nuna ta da dan yatsansa manuniya, sai ya kuma nuna wani sashi na kogon dutsen
.
Nan take sai zuhaisa taji kawai ana gwarata aka’ina a cikin kogon ta sume
Boka ahakamaul bainun ya sake bushewa da dariya a karo nabiyu
.
Lokacin da zuhaisa ta farfado daga suman da tayi sai ya kasance ko hannunta bata iya dagawa ,
Al’amarin daya matukar tayar mata da hankali kenan, take sai tay duba zuwa ga boka ahakamul bainun tace da shi “hakika yakai wannan takadarin boka ahakamul bainun wannan al’amari da kayi gareni baya nuna kayi galaba da rinye a akaina saboda ka kasnace boka mai dogaro da bokanci,
.
Ni kuwa na kasance ina mai tsananin takama da karfin damtse . Ka sani cewa muddin muka gwabza yaki da takobi tsakani na dakai tabbas nasan ba zaka wanzu tsawon dakika sittin a gabana ba face nasa takobi na daddatsa ka Ia dai kaman yadda duk wanda yasanka a baya bazan shaida ka ba”
.
Yayin da boka ahakamul bainun yaji wannan batu sai ya sake bushewa da dariya irinta mugunta da zalunci, sannan yace da zuhaisa ido cikin ido “hakika na kasance boka mara tausayi,mugu kuma azzalumi, bana tausayawa kowa hatta mata da yara kana na muddin suka fado a hannuna, tabbas duk mahalukin daya raboni ni nake zama ajalinsa amma a bisa ga tsananin mamakina sai gashi na kin zamo mutum na farko dana kasa hallakawa farat daya
.
Kar dai ku manta kuna tare ne da Shuraih 99%
.
Haka nan sai naji a jiki na ba zan iya kasheki ba na kasnace ina jin wani abu yana min yawo a zuciyata, wannan dalili ne yasa na tsananta bincike a gareki,
.
Sai daga karshe na gano na kamu da tsananin sonki da kaunarki a zuciyata saboda tunda nake arayuwa ta ban taba gani ko jin labarin mace mai tsananin kyau da cikar halitta sama da ke ba .
.
Al’amarin daya hanani kashe ki farat daya a lokacin dana fara ganinki wannan dajin tun sa’adda kika fara kusanto inda nake
.
Koda boka ahakamul bainun yazo nan a zancensa sai ya nuna zuhaisa da dan yatsa, take sai dukkanin karfin jikinta ya dawo gareta har ta mike tsaye tayi taku biyu daga inda take .
.
Kuma a sannan ne ta dubi boka ahakamul bainun tana nazarinsa boka ahakamul bainun ya kasance kato ne gajere mummuna yana da katon kai kamar wani dutse, fuskarsa cike da take da farin gashi, kuma ya kasance baki ne sidik
.
Zuhaisa ta kuduri yaudara acikin zuciyarta muddin zata samu nasarar biyan bukatarta a gareshi, take sai ta dubeshi cikin kisisina tana mai cewa dashi “ya kai boka ahakamul-bainun ka sani cewa na samu labarinka acan baya wurin wasu mutane, suka sanar dani al’amarinka na yadda ka gagari manyan sadaukai da jaruman wannan nahiya , lamarin daya kwataitar dani kenan naci alwashin sai na kawo kaina a gareka, mu kasance tare domin biyan wata muhimmiyar buka tata”
.
Sa’adda zuhaisa tazo nan azancenta sai tayi murmushi irin wanda ke janye hankalin duk wanda yake kallonta .
.
Boka ahakamul bainun ya dada kwadaituwa da zuhaisa anan take ma sai ya bude baki galala yana kallonta ita kuwa ta fahimci haka sai ta matsa kusa da shi tana karairaya har tasa hannu ta shafa krjins.
.
Al’amarin daya sa boka ahakamul bainun kenan ya kurma ihu don dadi da shagaltuwa da wannan al’amari anan take ma sa ya budi baki yace da zuhaisa
.
“Yake wannan yarinya ma’abociyar kyawu da cikar halitta , maza sanar dani wace ce ke, daga ina kika fito da har kike neman hadin kaina akan wata bukata ta ki?”
.
Yayin da zuhaisa taji wannan batu sai ta sake kallon boka ahakamul bainun sannan ta soma da cewa ” sunana zuhaisa bin zubgainu, mun kasance mu biyu ne ga mahaifiyarmu , un kafin a haifemu babanmu ya mutu, lokacin da aka haifemu ni da dan uwana mai suna huzainu sai ya kasance duk duniya bani da wani buri face naga na hallaka shi da kaina
.
Tun sa’addda muka girma nake ta faman farautar rayuwarsa domin ganin na
[Jama’a ayi hakuri don kuwa fallen wajen ya yage Shuraih 99%]
.
Bayan huzainu ya gama shiryawa sai kawai ya dane kan wani ingarmar dokinsa ya zabureshi ya faa tafiya har ya fito daga cikin kasarsu zaibalatu.
.
Yaci gana da tafiya yana wanda shi da kansa bai ma san inda ya nufa ba duk kauyuka da kananan garuwan dayake haduwa da akan hanyarsa sai ya shiga yana mai tambayar mutanen koda za’a sami wani wanda yasan inda take ko jin labari game da ita ,
.
Sannu a hankali har ya fita daga wannan nahiya tasu gaba daya ba tare daya samu wanda yasan komai akan mahaifiyarsa shafhila ba
.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai huzainu yaga wani matashin saurayi yana yakar wata rundunar yaki da wani gawurtaccen jarumi yake jagoranta
.
Mayakan suna kokarin halaka wannan saurayi a halin gajiya saboda tsananin yawan mayakan da suka taru suna yakarsa shi kadai
.
Koda ganin haka sai huzaini ya kwadaitu daya taimaka ma wannan saurayi dake yakar wannan runduna . Nan take huzainu ya dakawa rundunar yakin wata tsawa da dukkanin karfinsa muryarsa
.
Lamarin daya sa kowa ya karkato da hankalinsa zuwa gareshi sai kawai huzainu ya zare takobinsa tare da kutsawa tsakiyar mayakan yana saransu da tsananin zuciya mai karfin gaske .
.
Koda ganin haka sai shima wananna saurayi yaji wani sabon karfi ya shige shi , take yaji kamar a sannan ne aka fara wannan yaki suka hadu su biyu suna masu farauce rayuwar duk mai tsautsayin daya fado a agabansu
.
Wohoho! Masu iya magana suna cewa mai son yayi kuka ne aka jefeshi da kashin awaki ,
Nan take wani sabon azababben yaki ya kacame a tsakaninsu huzainu ya wanzu yana mai tsananin farauce rayuwar wadannan mayaka , duk inda ya juya sai dai kaga yana tsarge mutane gida biyu haka nan shima wannan saurayi ya kasance sadauki ne mai karfin damtse da juriya , yana aikata mummunana kisa ga wadannan mayaka kamar yadda yaga huzainu yana aikatawa gare su
.
Cikin sa’a daya sai gashi sun halaka fiye da kaso biyu daga cikin kaso biyar na wadannan mayaka lokacin da wannan jarumi mai jagorantar runudunar ya fahimci wannan ta’asa ta huzainu da kuma wannan saurayi , sai ya fusata , nan take ya zare takobi tun ma daga nan inda yake zaune akan dokinsa yayi wata alkafura sai gashi yana juyi a sama sai gashi ya dira a bayan huzainu yasa takobinsa dake hannusa ya saro huzainu da dukkanin karfisa
.
Sai da kaifin takobi ya samu nasarar keta karfen dake bayan huzzainu yaji masa ciwo , har ya shige shi, jini yai tsartuwa a inda aka sareshi,
.
Take sai huzainu ya fado daga saman dokinsa saboda tsananin karfin saran da akayi masa bayan ya mike tsaye ne sai kawai ya juyo da baya da nufin yaga wanene yayi masa wannan sara haka cikin shammata da bazato lokacin da huzainu yaga ashe jarumin dake jagorantar wannan runduna ne
.
Take sai ransa ya baci fiye da sa’adda aka fara wannan gumurzu
.

Suka kurawa juna, idanu cikin nazari da jin motsin juna, lokaci daya suka yi kukan kura suka afkawa juna da sara da suka cikin tsananin zafin nama da jarumta
.
Sai da suka shafe fiye da rabin sa’a suna wannan azababben gumurzu ba tare da dayansu ya samu sa’ar raunata daya ba
.
Yauwa anan zan tsaya
Kuyi hakuri da yanayin posting din wlh bana samun lokaci ne
.
Naku akullum shuraih 99%
Friends kui hakrui yau ban yi posting da wuri ba
Wallahi bani da lafiyane
Yanzu ma na dan ji sauki ne shi isa na shigo
Ii

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.