Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

RANA DA WATA littafi na daya 1 part D

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part D

.
Sa’adda wannan sadauki yazo na a zancensa sai zuhaisa tace da shin cikin zafin zuciya ” kada kayi zato ko tsammanin kasancewata mace kuma ni kadai ki hudun nan zaku iya razana ni.
.
Yakai wannan karamin sadauki ma’abocin shisshigi da kokarin haikewa ajalinsa, kayi sani cewa a yadda kuke din nan izan za’a ninka ku sau goma ba zaku sa naji dar a zuciyata ba.
.
Ina mai ja maka kunne akan wadannan munanan kalamai daka ambata zuwa gareni.
.
Maza ka tuba ko ka samawa kanka afuwa da sassauci akan fushin da zai afko zuwa gare ka kai da mutanenka”
.
Yayin da wannan sadauki yaji wannan batu, sai ya dada harzuka fiye da farko.
.ni dinne dai Shuraih 99%
Nan take ya dakawa daya daga cikin yaransa tsawa akan ya saro masa kan zuhaisa .
.
Koda ganin haka sai ran zuhaisa ya baci ita a ganinta ya za’ayi kamarta za’a turowa wani karamin sadauki tare da umartarsa daya saro kanta
.
Ai kuwa sai ta zare takobi tun ma kafin sadaukin ya karaso zuwa gareta ta tareshi a kai masa wani gawurtaccen sara ta halaka shi, sannan karkata linzamin dokinta ta afkawa ragowar da sara da suka cikin tsananin bacin rai da jarumta ,
.
Anan take wani sabon azababben yaki ya kacame a tsakanin su cikin kankanin lokaci zuhaisa ta zabtarewa biyu hannayensu wadanda ke dauke da makamansu. Sannan ta juya ga babbansu tana kai masa sara ba kakkautawa.
.
Acikin dakika sittin ta galabaitar da shi, kawai ya zubar da makamansa ya mika wuya ga zuhaisa
.
Ita kuwa ganin haka sai tayi kururuwa ta daki kirji da hannun hagu sannan tasa takobi ta sare masa kunnen daya.
.
Take ya fado daga kan dokinsa ,jini yai tsartuwa a inda ta cire masa kunnen. Zuhaisa ta diro daga kan dokinta ta cakume shi ta kuma tuntsirewa da dariya a karo nabiyu sannan da shi “wannan zamo misali a gareka da sauran masu hali irin naka . Maza ka sanar dani izan nabar nan ina zan dosa?”
.ni dinne dai Shuraih 99%
Koda sadaukinnan yaji wannan tambaya ta zuhaisa saiya amsa mata da cewa
“Yake wannan matashiyar basadaukiya kiyi sani cewa zai fi miki abu mai sauki da ki koma inda ki ka fito domin kuwa hadarin da zaki tarar akan hanyar nan yafi gaban tunaninki.
.
Ko mu din nan da kike gani nan ,idan muka yi fashi bama kusantar hanyar nan.
.
Kiyi sani cewa akwai wani hatsabibin boka kuma takadari mai suna AHAKAMUL-BAINUN yana da tsananin karfin tsafi, yana da hatsarin gaske kasnacewar manyan jarumai da hatsabiban bokaye komai yawansu sai ya gagare su ya addabesu a karshe kuma ya hallaka su gaba daya .
Yake wannan basadaukiya ina mai shawartarki da ki juya da baya , ki canja hanya domin yafi maki sauki “
.
Koda zuhaisa taji wannan bayani na wannnan dan fashi sai tace da shi ” kada ka damu, tunda ka sanar dani komai to lallai sai na shiga dajin nan ,koda kuwa zamuyi arangama da fito-na-fito dashi wannan hatsabibin bokan nan”
.ni dinne dai Shuraih 99%
Batare da bata wani dogon lokaci ba ,zuhaisa ta dare akan dokinta ta zabureshi sannan ta kutsa kai a cikin daji ba tare da fargaba ko shayin komai ba .
.
Ai kuwa zuhaisa ba tayi nisa ba sai hango wani katon dutse agabanta , ajikin dutsen akwai wani kogo mai zurfi wannan ya tabbatar mata da cewa wannan boka yana a cikin wannan kogon dutsen ne .
.
Zuhaisa ta sauka daga kan dokinta kai tsaye ta danna kana cikin kogon dutse ba tare da fargabar komai ba .
.
Kogon dutse ne mai tsananin girma da fadin gaske babu komai a ciki face kasusuwa na sassan jikin mutane sai kuma kayayyakin irin na bokanci a ko’ina , yayinda zuhaisa ta gama nazari a cikin kogon dutsen sai ta fara tafiya acikinsa tana lura tare da sauraren wani motsi dake dada karuwa sannu sannu
.
Daga bisani ma sai kofar shigowa kogon ta shafe kuma asannan ne wani bakin duhu ya mamaye kogon .bayan kaman dakika sittin kuwa sai aka fara girgiiza kogon, sautin kukan yara kana na. Yana amsa kuwa a cikin kogon.
.
Zuhaisa tayi alkafura tana juyi a sama ta dira a wani guri can daban, sakamakon jin sautin tahowar wani a gareta . Wato wani katon dutse ne ya mirgino yana niyyar taushe ta.
.
koda zuhaisa taga matsawar tayi wasa zata iya rasa rayuwarta a cikin wannan kogon dutse, sai ta bude baki ta fara magana cikin madaukakyira murya ,tace” hakika wannan al’amari naka yakai wannan ma’aboci bokanci, yana nuni da cewa ka tsorata da al’amarina , saboda ka ki bayyanarr da kanka gareni , ka labe kana kokarin cutar da ni. Ka sani baya daga dabi’un manyan mutane madaukaka suyi yaudara ga dukkan Al’amurransu”
.
Koda jin wannan batu sai ya harzuka boka ahakamul-bainun, hankalinsa ya dugunzuma ,kasnacewar tun da yake zaune a cikin wannan daji babu wani mutum da ya taba kwatanta fada masa wata magana ,mai daci da muni irin wannan saboda sanin matsayinsa da daukakarsa a duniyar tsafi.
.ni dinne dai Shuraih 99%
Nan take sai yayi kururuwa da karfin muryarsa , gaba daya kogon ya amsa kuwwarsa,sai kawai ya bayyanna gareta .kuma a wannan lokacin ne duhun ya yaye, haske ya maye gurbinsa.
Koda boka ahakamul-bainun ya dubi zuhaisa cikin tsananin bacin rai ya daka mata tsawa
.
“Hakika yake wannan yarinya kin aikata manyan laifuka biyu a gareni. Na farko kin shigo wannan daji ba tare da izini na ba har kika shigo cikin turakata bata re da fargabar komai ba.
Na biyu kkuwa kin furta munanan kalamai masu nuna rauni da gazawa gareni. Lallai zaki dandana tsananin zalunci da ukubata ,
.
Kafin daga karshe na halakaki
……….
Anan zan dakata sai mun hadu a part e
ni dinne dai Shuraih Usman
In kiya shuraih 99%

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.