RANA DA WATA littafi na daya 1 part C

 RANA DA WATA littafi na daya 1 part C
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Aug, 2018
Upload Time 2:59 am
Hits 277 Hits
Comment No Comments

Description

RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
PART:- C

*********
Al’amarin huzainu da zuhaisa kuwa arana da suka fahimci mahaifiyarsu bata na duk kuwa da cewa basu san inda ta tafi ba ha tsawon wata guda cur , sai zuhaisa ta hada kayanta tsaf tayi shigar kayan yaki, tayi tsalle ta dare akan ingarman dokinta a dai-dai wannan lokacin huzainu ya karaso a gurin
.
Zuhaisa ta dubeshi da tsana cikin tsananin kiyayya, sannan ta zare takobi tareda nuna shi da tsinin takobin tace “na fahimci mahaifiyamu tayi wata tafiya daba dta son mu san inda ta tafi, kama yadda kasani a duk fadin duniya babu wani mahaluki dana tsana da tsananin kiyayya sama da kai.
.
Kamar yadda na daukarwa kaina alkawarin da karfin damtsena sai na sanya takobi na datse jijiyar wuyanka, da iyakance numfashinka [ its shuraih 99%] a doron kasa .
.
Hakika bani da wani buri daya wuce na ga na shafe babin rayuwarka. Don haka na yanke shawarar barin mahaifata a yanzu , zanje na dada yin shiri da mummunan tanadi a akanka
.
Inasi ka sani daga ranar da muka sake haduwa da kai ,to ka sani a wannan ranar ne mala’ikan mutuwa zai gabata zuwa gareka, na rantse da iyayena ba zaka kubucewa kaifin takobina ba face na halaka ka”
.
Koda huzainu yaji wannan batu sai ya tuntsire da dariya, ya dade yana yi tamkar bazai daina ba, al’amarin daya harzuka zuhaisa kenan ranta ya baci jijiyoyin jikinta suka motsa sai kawai ta diro daga kan dokinta ta nufi huzainu da bakar zuciya tana gurnani kai kace zaki ne yayin da zaluncinsa ya motsa masa a lokacin daya ga wata karamar dabba
.[shuraih Usman nake inkiya 99]
Zuhaisa tana kusanto huzainu sai ta kawo masa wani gawurtaccen sara a saitin dokin wuyansa da niyyar ta sare masa kai cikin tsananin zafin nama, kwarewa da jarumta huzainu ya goce takobin ta wuce ta saman kansa ta kara kawo masa wani mummunan sara a anan ma ya kauce
.
Da huzainu yaga da gaske fa zuhaima take sai shima ya zare nashi takobin nan ne fa suka fara wani azababben yaki, suka kasance cikin kai ma juna sara da suka suna masu zafin nama, juria da jarumta
.
Sai da suka shafe sa’a uku babu wanda ya samu nasarar yiwa daya koda sara daya ne har sai da takubbansu suka dakushe saboda tsananin kai sara ga junansu
.
Sannan suka zubar da makaman nasu suka kacame da kokawa da naushe-naushe.
.
Babu jimawa kowannensu ya hada gumi woho ho mai karfi sai Allah ya isa nan fa tsagwaron karfin damtse ya soma amfani sai gashi su duka biyun kwanjin jikinsu ya dada kumbura , jijiyoyin suka tashi sukayi burdinburdum.
.
Can gabannin faduwar rana kowannensu kamar an yi masa umarni sai suka turje suna masu kallon juna kamar zakaru [shuraih Usman nake inkiya 99]
.
Zuhaisa ta nuna huzainu da dan yatsa ta ce da shi ” kamar yadda na fada da farko ka saurari haduwarmu anan gaba kadan. Ka sanni bana afuwa , kuma bana mance gaba komai kankantarta”
.
Lokacin data zo nan a zancenta sai tayi tsalle ta dare akan dokinta taci gana da tafiya . Huzainu yai tsaye yana kallonta kawai ba tare da yace da ita ci kanki ba.
.
A haka har ta bace masa ya daina ganinta
.
Da farko Zuhaisa tayi niyyar shiga duniya domin ta dada samun horo da jarumtaka fiye da huzainu yadda da zarar ta sake haduwa da shi tayi masa kwab daya ta gama da shi
.
Sai kuma ta sauya ra’ayinta akan ta fara neman ilimin bokanci wanda tana ganin ta wannan hanyar ne yafi sauki, kafin ta hallaka shi ta kashe shi.
.
Sannu a hankali har zuwa zuhaisa ta bar nahiyar kasarsu ta danna kai cikin daji
.
Lokacin da zuhaisa ta shafe wata daya tana tafiya ba tare da ta hadu da wani abu na cutarwa ba , sai ta zo inda hanya ta kasu gida uku nan take sai ta karkata linzamin dokinta ta dauki hanyar da ta nufi arewa.
.[shuraih Usman nake inkiya 99]
Bata dade tana tafiyaba sai kuwa taci karo da wadansu mahaya dawai har su hudu dauke da makamansu
.
Daya daga cikinsu wanda yafi sauran zafin zuciya da karfin hali ya dakawa zuhaisa tsawa yana mai cewa da ita “yake wannan kyakkyawar yarinya ma’abociyar kyawun fuska, maza ko gaggauta miko kanki zuwa garemu da dukkanin abinda kike dauke da shi, ko kuwa fushinmu ya sauka a kanki ba zamu lura tsananin kyawun fuska da cikar zatinki ba”
…….Wai lallai wannan ya tsokano tsuliyar dodo
Mai shirin kuka an jefeshi da kashin a waki
.
Anan zan tsaya sai Gobe
Kar ku manta dai kuna tare ne da Shuraih Usman
Inkiya 99%

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: