Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

RANA DA WATA littafi na daya 1 part B

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

BRANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part B

Shuraih 99% nake cewa daku Lokcin da boka sharanu yazo nan a zancensa sai tsohuwa shafhila tayi doguwar ajiyar zuciya , sannan ta dubeshi a cikin nutsuwa tace ” yakai wannan boka mai yawan daraja ka dubeni ka gani , nifa na tsufa banida wani buri da yai mini saura a wannan duniya face ganin cewar bayana tayi kyau. Ina mai tabbatar maka cewa raina da duk abinda na mallaka ba’a bakin komai suke ba, muddin wadannan yayan nawa zau hada kansu su zauna lafiya a matsayin yan uwan juna na jini ba abokan gaba ba .
.
Yanzu zan koma gida naje na sayar da duk abunda na mallaka domin nayi guzurin wannan tafiya .
.
Abinda na ke so naji daga gareka kawai shine yaushene abokan tafiyar tawa zasu hallara anan mu gamu mu dunguma gaba daya mu tafi birnin sin(abokan tafiyarmu zakice don kuwa har dani acikin wanga tafiya ehm shuraih 99%)
.
Yayinda tsohuwa shafhila ta zo nan a zancenta sao boka sharanu ya kura mata idanu cikin natsuwa da mamaki, sannan yace ” na rantse da darajar iyayena da kakannina da kuma darajar tsafina ke ce mutum ta farko data taba cin alwashin zuwa kogon darul yamzin ba tare data girgiza ba, hakika yake wannan tsohuwa shafhila , ina ji ajikina cewa zaki samu nasarar zuwa wannan kogon koda kuwa wannan bukata taki zata zamo ajali a gareki.
.
Saboda haka maza ki gaggauta kammala shirin tafiya nan da kwanaki uku”
.
Lokacin da boka shuranu ya zo nan azancensa , sai ya taba hannayensa a take ya bace a gurin , Tsohuwa shafhila ta daina ganinsa.
.
Kar dai ku shagala kuna tare da Shuraih 99% ne
.
Yayin da tsohuwa shafhila ta samu kwanaki uku. Daidai lokacin data karasa duk wani shiri nata tsaf .
.
Sai shafhila ta gabata a gaban boka sharanu zuciyarta ta kekashe a yanzu bata da wani buri a rayuwarta face taga yayanta huazainu da zuhaisa sun hada kansu wuri daya sun daina tsananin gaba da kiyayya da junansu .
.
Lokacin da boka sharanu ya dube ta sai ya tuntsire da dariya kamar bazai daina ba. Al’amarin daya dada karfafawa shafhila guiwar zage damtse kenan akan wannan tafiya kuma a
.
Lokacin ne fataken da zau tafi tare suka karaso. Daga cikinsu akwai manyan attajirai da jarumai masu tsananin kafiya da dakakkiyar zuciya. Yawan fataken duk su dari uku ne.
.
Boka sharanu ya dubi tsohuwa shafhila sannan ya mika mata fatar barewa yace da ita “ki rike wannan a duk lokacin da kike bukatar sanin wani abu a yayin wannan tafiya taku ki shimfida wannan fatar barewan sannan ki kirayi sunana sau uku fuskata zata bayyana a kai ki fada mini matsalarki”
.
Sa’adda boka sharanu yazo nan a zancesa sai tsohuwa shafhila tayi godiya a gareshi , sannan ta shige cikin a yarin fataken nan ba tare da bata lokaci ba suka kama tafiya cikin azama a wannan gagarumar tafiya tasu mai cike da hadarurruka.
.
Kwanci tashi har suka shafe kwanaki goma suna tafiya ba tare da sun sami wata matsala ba.
.
Dukkana fataken nan sun cika da tsananin mamaki akan tsohuwa shafhila domin tafi kowa doki da tsananin kuzari a wannan tafiya, sai ya zamana a yanzu tsohuwa shafhila ce ke jagorancin tafiyar duk da cewa akwai manyan sadaukai da jarumai a ciki.
.
Lokacin da suka sake shafe kwanaki uku a wannan lokacin sun zo wani daji mai tsananin duhuwa da dogayen itatuwa masu tsayin gaske . Daga cikin ayarin fataken akwai wani sadaiki mai suna sabitul-agadawur ibni ihwas.
.
Ya dubi tsohuwa shafhiila yace da ita .
“Hakika yake wannan tsohuwa ki sani cewa a yanzu munzo dajin mutane ma’abota cin naman mutane.
.
Ki sani a wannan daji duk girmansa babu ko dabba daya dake rayuwa a cikinsa.
Saboda tsananin shawagi irin na wadannan mutane shi yasa ko tsuntsaye basu kusanto wannan daji .
.
A tarihi ba’a taba samun wani ayarin fataken da suka taba ratsa wannan daji suka fita lafiya ba , face wasu da yawa daga cikinsu sun halaka
.
Sannan suna da yawa ,kuma suna da tsananin kafiya da naci, ance saboda maitarsu idan suka asa mutanen da zasu halaka su cinye, sai babbansu yasa ayi kuri’a duk wanda tsautsayi ya afkama to a wannnan ana sune kalacinsu.
.
koda sadauki sabitul-agadawur ya zo nan azancensa , sai ya dubi sauran abokan tafiyarsa ya kara da cewa “saboda haka ya zama wajibi mu yi taka tsantsan wasun mu su rika lua da bayanmu wasu kuma su rinka lura da gefen dama da gefen hauninmu”
.
Daga nan babu wanda ya kaa cewa komai suka ci gaba da ratsa dogayen itatuwan dake a wannan daji
.
Anan zan dakata , Kar dai ku manta kuna tare da
Shuraih Usman
Inkiya 99%

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.