RANA DA WATA littafi na daya 1 part A

 RANA DA WATA littafi na daya 1 part A
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Aug, 2018
Upload Time 2:57 am
Hits 589 Hits
Comment No Comments

Description

RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
PART:- A

Masu karatu ayimin afuwa don kuwa farkon fallen littafin ya yage amma ga abunda ya kunsa
.
Acan cikin wani kauyene wata mata mai suna shafhila sai faman naku da ta ke tayi yayin da sararin samaniya kuwa sai amsawa yake, ba’a bata lokaci ba matar ta haifo yaranta guda biyu
.
Babu abun da zai baka mamaki da wayannan yara face sam basa kaunar junansu, don kuwa koda yaran suka fara girma sai ya kasance suna matukar GABA da juna tamkar RANA DA WATA ,
A kowani lokaci kuwa babu abunda suke yi face fada da junansu wanda wannan abu yana matukar damun mahaifiyarsu shafhila
Shekaru suna ta ja har takai sun girma sun mallaki hankulansu amma basu daina wannan gaba da fada ce fadace ba
Macen mai suna zuhaisa zuciyarta bakine sam babu ko digon tausayi ko imani a tattare da ita
Shi kuwa namjin mai suna huzainu babu abun da ya tsana face zalunci , kuma shi kadai ne acikin wannan gari wanda yake hana Zuhaisa ai kata zaluncinta don kuwa aduk lokacin da zata aikata zalunci sai ya bayyana, sannan su cigaba da bakin yaki tamkar ba ciki daya suka fito ba
.
Hakan shi yasa mahaifiyarsu ta nufi wajen boka wani shahararren boka mai suna sharanu koda isarta wajensa har ta budi baki zatace wani abu sai boka shuranu ya dakatar da ita sannan yace” yake wannan tsohuwa kiyi sani cewa nasan abun da ke tafe dake ,”koda jin haka sai shafhila tace
Shin boka yaya za’ai su hada kansu su daina wannan gaba da fadace fadace

Koda jin bukatar shafhila sai boka sharanu ya tuntsire da dariya
Al’amarin da yai matukar firgita shafhila kenan
Lokaci guda boka sharanu ya murtuke fuska ya dubeta yace “yake wannan uwar jarumai ki sani cewa har abada yayanki ba zasu taba kaunar juna ba , kuma ba zasu taba zama ba a waje daya domin tamkar RANA DA WATA suke .
.
Sai aranar da dayansu ya kashe daya sannan nadama da takaici zasu zo masa.
Ki sani cewa kin haifi yayanki ne a ranar da aka samu kisfewar rana.
Ita macen kin haifeta ne a dai dai lokacin da rana zata kisfe , don haka ta zamo mai bakar zuciya da bakin rai . Saboda rana aba ce mai zafi,
.
Shi kuwa namijin kin haifeshi ne a dai dai lokacin da wata ya kisfe, shi yasa ya zamo mai tausayi da sanyin rai (kaman ni kenan, kar dai ku shagala Alkalamin shuraih 99% ne]
.
Wadannan yaya naki zasu daukaka a duniya irin wacce babu kamarta a wannan zamani.
.
Macen zata zamo gagarumar matsafiyar sarauniya .shi kuwa namijin zai zamo gawurtaccen sarki ma’abocin wani bakon Addini,
.
Zasu yi ta yakar junan har izuwa lokaci mai tsawo, yayansu ma sai sun gaji wannan gaba kuma a karshe sai dayansu ya kashe daya”
.
Koda jin wannan labari sai tsohuwa shafhila ta dafe kai tana mai fashewa da matsanancin kuka na bakin ciki tamkar ba zata daina ba .
.
Da kyar boka sharanu ya lallasheta tayi shiru snnan ta dube shi tace da shi.
“Yakai wannan boka mai daraja , yanzu wace hanya zan bi na sauya wannan al’amari ya zamana cewa wadannan yaya nawa sun hada kansu sun daina gaba?”
.koda jin wannan tambaya sai boka shuranu ya sake tuntsirewa da dariya a karo nabiyu , daga san ya takarkare ya kwarara uban ihu mai firgitarwa , har yana birgima a kas,
.
Al’amarin daya firgita tsohuwa shafhila kenan har ta ja da baya .
Ta takure jikinta ajikin bangon dakin kamar zata saki fitsari saboda tsananin tsoro daga can kuma sai taga boka shuranu yayi doguwar ajiyar zuciya a lokacin daya jike sharkaf da gumi sannan ya dubeta yace “yake wannan tsohuwa, kiyi sani cewa babu wani abu da zai iya canza wannan al’amari face ki sallama rayuwarki don inganta tasu.
Kuma yin hakan ma ba abu bane mai sauki ba domin dole kije har can kogon darul yazmin dake can karshen birnin sin ki yanka jijiyar hannunki na hagu a cikin kokon dodonniya HUJUMU-MAJNUN har sai kokon ya cika ta zo ta shanye jinin duka , nan take rana zata kisfe .
.
Idan da rana ne abin ya faru. Haka kuwa wata zai kisfe, idan a lokacin da abin ya faru dare ne ki sani cewa a tarihin kogon darul yazmin tun daga wanzuwarsa kawo izuwa yanzu, babu wani bil’adama ko aljani daya taba shiga cikinsa ya fito a raye sai dai a mace aciki har ya rube, ya zama kwarangwal.
.
Duk abin da mutum yake nema na duniya in dai ya shiga cikin darul yazmin sai ya sameshi walau dukiya ko maganin wata cuta data gagara . Matsalar dai itace koda mutum ya sami biyan bukatarsa bai isa ya iya fitowa ba araye daga cikin kogon saboda hujranul-majnun ce take gadin duk abin daya ke cikinsa
(Lallai dole nayi shiri na ttunkari kogonnan saboda wata bukata tawa ehm shuraih 99%)
.
Dodonniya hujranul majnun ta kasance gabjejiyar dodonniya mai tsawon gaske gami da kauri da fadi. Idan ta tsaya a gaban mutane komai yawansu sai su ga kamar a gaban tsauni suke.
Ta kasance basadaukiya mai tsananin karfin damtse domin komai girman dutse da kwarinsa
.
Idan ta dokeshi da hannunta sai yayi bindiga ya tarwatse, kuma tana iya kwakule duwatsu da kaifin faratan hannayenta ko ta yanka karafa da su ta sarrafa karafunan wajen kera abubuwa da yawa kamar kofunan zinare,gadaje,kujeru,da saurran kawa irinsu lu’u lu’u jauhar da sauransu wanda Aljanu suke zuwa su siya a wajenta
.
Masana da masu bincike sun tabbatar da cewar a duk fadin duniya babu wani makeri wanda yafi dodonniya hujranul-majnun iya kira da sanin karfe kuma babu wani boka wanda yafita karfin sihiri, babu wani sadauki wanda ya fita karfin damtse gami da zafin nama.
.
Kaifi da tsini basa tasiri a jikinta
.
Dukiyar data tara kuwa a kaf duniya babu wani Attajiri daya tara kamarta komai karfin arzikinsa da karfin mulkinsa.
Dodonniya hujranul-majnun tana iya tarwatsa runudunar mayaka ita kadai komai yawansu, sai dai su tsere su gudu su barta
.
A halin yanzu dodonniya hujranul-majnun tana da shekaru dari da talatin da uku a duniya.
.
Yake wannan tsohuwa isan har zaki iya siyar da rayuwarki kije har can dajin inda kogon darul-yamzin yake a karshen birnin sin to sai kiyi shiri ki zo nan akwai fataken da zan hada ki dasu su kai ki har birnin sin daga can kuma akwai aljanu wadanda za’a hada dasu su kai ki har bakin kogon darul-yamzin
.
Ammafa ki sani cewar wannan tafiya zata daukeki a kallah shekara shida, kafin ki isa birnin sin kuma zaku ketare ta cikin mugayen dazuzzuka masu dauke da mugayen aljannu, dodonni da mugayen dabbobin daji wadanda zasu iya zama sanadin ajalinku , sai mai cikakken rabo da matukar sa’ane zai iya kaiwa har can a raye kuma cikin koashin lafiya
.
Toh ana zan dakata sai kuma gobe in Allah ya kaimu da rai da lafiya
Daga shuraih Usman
Inkiya 99%
Sai kunjini da part

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: