Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

RANA DA WATA littafi na biyu 2 part D

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RANA DA WATA
Littafi na biyu 2
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part D
.
.
“Ai duk wanda ya saba shiga cikin manyan dazuzzuka , ba zai taba firgita da ganin irin wadannan ramuka ba, babu ruwanmu da duk abun daya ke cikinsa face idan ya bayyana garemu da nufin ya cutar wa”
.
Yayin da zahakim yazo nan a zancensa sai ya kishingida domin ya huta, hankalinsa a kwance babu abinda yake damunsa, koda ganin haka sai sauran abokan tafiyar ma suka sami nutsuwa da kwanciyar hankali,
.
Batare da wani bata lokaci ba , sai suka shiga aikin kafa tantuna sai da suka shafe tsawon sa’a uku sannan suka kammala kafa tantunan, wani sadauki daga cikin ayarin ya zagaya can baya da niyyar yin bawali,
.
Bisa ga tsautsayi sai ya tsaya a dai dai daya daaga cikin wadannan ramuka ya zage mazagin wandonsa sannan ya fara fitsari yana mai jin dadi har yana lumshe idanu da wani murmushi, har takai ya fara wata yar waka saboda jin dadin wannan bawali dayake Gabatarwa (ayya har na tausaya masa Shuraih Usman inkiya 99%
.
Ashe wannan fitsari daya keyi, yana kwararawane akan idanun wata shirgegiyar macijiya mai tsananin kauri da tsawon gaske, koda taji ruwan fitsari yana sauka akanta kuma tajiyo sautin muryar wannan sadauki, sai tta sadado a hankali har ta iso dab da bakin ramin
.
Tana yin arba da shu tayi fitar burgu ta wangame baki ta cabi kugunsa gaba daya tana zuba mar hakora ta raba shi gida biyu, sadaukin ya kwarara uban ihu, alokacin da rabin jikinsa ya fadi can gefe daya jini yai feshi a sama sannan ya malala a kasa
.
Cikin tsananin firgici su jarumi zahakim sukayi zumbur suka rugo izuwa wajen suna zuwa wajen suka iske macijiyar bata gama hadiye rabin jikin wannan sadauki ba,
Al’amarin daya daure masu kai kenan, suka yi niyyar su gudu amma sai jaruman cikinsu suka tsaya tare da zare takobi, suka tunkari macijiyar da nufin su kare iya numfashinta su halakata acikinsu har da Shuraih Usman inkiya 99% wannnan maridi shi ya fara daka tsalle ya cafi wuyanta sannan suka kama kokowa, tana danneshi yana danneta, yana matse mata kai koda ta ga zai hallakata sai ta kannannadeshi da gaba dayan jikinta ta matseshi ainun take kasusuwan jikinsa suka kakkarye gaba daya tayi jifa da gawarsa
.
Jarumi zahakim ya daga takobinsa ya girgizata sannan ya tunkari wannan maciya. Da zuciya mai tsananin karfin gaske haka nan ma sadauki sabiyul-agadawur koda ganin zahakim ya tari macijiyar nan take shima ya tunkareta a fusace yakai mata sara koda takobinsa ta hadu da jikin macijiyar sai ta lauye kafin sabitul agadawur yai wani motsi tuni macijiyar tasa jelarta ta make shi yai sama yana katan tanwa ya gwaru da wani katon dutse dake can nesa ya fadi a matukar galabaice
.
Koda zahakim yaga haka sai yai wani tsalle da yana juyi a sama ya Shuraih Usman inkiya 99% cakawa macijiyar takobin dake hannunsa da dukkanin karfinsa, nan take sai yaji kamar ya soki karfe, kafin yakai kasa macijiyar tasa jelarta, ta kara masa gudu ya fadi can nesa da ita, bakinsa ya bugi wani karamin dutse ya fashe, jini yai tsartuwa daga bakin nasa
Lokacin da zahakim ya shafa bakinsa yaga jini, sai hankalinsa ya dugunzuma yai saurin mikewa tsaye ya sake fuskantar macijiyar yana mai nazarinta, kuma adai dai wannan lokacin ne, dukkanin dakarun da ke cikin ayarinsu suka dawo a wannan waje domin suma ayi ta kare tare da su,
Suka hadu dayansu suaka yi wa maciyar kawanya kowannensu dauke da makamin daya iya sarrafawa a filin yaki
.
Macijiyar tayi wani ruri da gunji ma tsananin karfi, gaba dayan dajin ya amsa amon kuwwarta, sannan tayi wani juyi da zabura da tana gurnani, bakinta yana mai fitar da wani farin hayaki, maciyar ta afka Shuraih Usman inkiya 99% a tsakiyar ayarin tana mai kai sara da zago zagon hakoranta, ta sari da yawa daga cikinsu, tayi amfani da jelarta ta make da yawa daga cikinsu wasu sun kakkarye, wasu kuwa sunji raunika da sama daga cikinsu, har ta kaima wasu da jan ciki suke kokarin guduwa domin su tsira da rayuwarsu, sai ya kasance gaba daya ta watsar da su ta daidaita su, masu taurin rai ne daga cikinsu , suka mike tare da sake tunkararta suna kai mata sara duk da sanin cewa ko sun sare ta ma bata ji
.
Zahakim ya harzuka matuka ya ruga a guje iuwa kan wannan maciya yana sararta tako ina idan ta kawo masa duka da jelarta, cikin zafin nama gami kwarewa da sanin makama yake saurin gocewa haka nan idan tayi masa tsartuwa sai yasa garkuwa ya kare batare da wani ya cutar da shiba, sai da suka shafe dakika dari da arba’in suna wannan bakin artabu, dayansu bai samu nasarar cutar da daya ba, kawai sai macijiyar ta shammaci Shuraih Usman inkiya 99% zahakim ta maka masa jelarta a kirjinsa take kirjinsa ya dare jini yai tsartuwa zahakim ya kwarara wani uban ihu yai tsalle ya fadi can gefe daya
.
Koda ganin haka sai macijiyar ta juya iuwa sauran sadaukan da suka rage tayi wani ruri da tsananin karfi ta jijjiga jikinta tana mai dada kumbura, ta nufi inda suke domin ta hallakasu anan fa dakarun suka dimauce hankalinsu ya dugunzuma suka dimauce bisa ganin mutuwa miraran, saboda babu abinda zasu iya yi a wannan lokaci, kasancewar sun nakasa ainun
Koda jarumi zahakim ya hango abinda yake shirin faruwa ga abokan tafiyarsa sai ya fusata ya mike tsaye cikin tsananin juriya da jarumta ya yage rigarsa ya daure raunin dake kirjinsa ya falfalo da gudu ta bayana maciyar ya daka tsalle ya haye bisa jelarta kuma ya cigaba da gudu akan jelar kamar mai hawa matattakalar bene har sai dayazo tsakiyar kan macijiyar
.Shurai Usman inkiya 99%
.
Kawai sai ya daga takobinsa ya soka mata a tsakiyar kanta ai kuwa sai takobin ta lume gaba daya, yana zare takobin jini ya kama feshi yana tsiri a sama a lokacin da macijiyar ta kama ruri da gunji, wanda ya haddasa girgizar kasa a gaba dayan dajin
Babu shiri jarumi zahakim ya daka tsalle yado a kasa can gefe daya ya baje kasa sumamme
.
Ita kuwa maciyar sai ta kama mirgina akas,tana mata gunugun kuma tani ci gaba da ruri har saida karfinta a kare , jikinta ya sandare gaba daya, ta zama gawa,
A wannan lokacin ne sauran abokan tafiyar suka rugo izuwa gareshi sabitul agadawur ya shiga aikin ceto shi daga halaka
.
Bayan andinke raunin dake kirjinsa an sa masa magani, sai suka ga ko motsi bayayi, kuma babu alamar numfashi a tare da shi, al’amarin daya dugunzuma hankalinsu kenan suka fara tunanin koya mutu nan fa jikin kowa yai sanyi, ganin cewa ya zama kamar shine Shuraih Usman inkiya 99%. Jagoran wannan tafiya tasu ba zato ba tsammani sai sukaga yayi wani gwauron numfashi, nan take suka cika da tsananin farinciki suna murmushi da dariya
.
Duk wayanda suka kakkarye aka gyara masu karayarsu, wadanda suka ji rauni aka sa masu magani, sabitul agadauwur yabada umarnin akwana a wannan wuri sai gobe. Kashe gari da sassafe suka ci gaba da tafiya, har ya kasance a wannan karon sun shafe kwana ashirin batare da sun hadu da wani abu na cutarwa ba, kuma a wannan lokacin ne duk guzurinsu ya kare ga shi sun nemi abun da zasu ci amman babu, kuma duk dawakansu sun gaji da yawa daga cikin dawakan suna sassarfa kamar zasu fadi
.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka hango wadansu bukkoki a gabansu alamar cewa wani karamin kauye ne a gabansu
Al’amarin daya jefa kowa cikin tsananin farin ciki kenan cikin hanzari suka ruga izuwa wannan dan karamin kauye Shuraih Usman inkiya 99% suna shiga sai suka ga ba kowa kuma babu wani abu mai rai dake kai kawo acikin garin a tsakiyar garin suka ga wadansu manya manyan tukwane kimanin guda bakwai bisa murhun wuta ana dahuwa a cikin shi ruwan cikin tukwanen ya zabalbala yana fitar da tiririn hayaki
.
Nan fa wasu daga cikin abokan tafiyar suka fara hadiyar yawu, suna waige waige da dube dube ko zasu ga wadan da ke da wadannan tukwane, amma basu ga kowa ba wani wanda yafi koowa karambani ana kiransa da suna ruhaisu kawai sai ya tafi izuwa ga tukunya guda yasa hannu ya bude murfinta, koda kamshin abincin ya daki hancinsa, sai ya kama dariyar murna, kawai sai yaga wani katon ludayi a gefen tukunyar nan take ya dauki wannan ludayi ya tsoma a cikin wannan katuwar tukunya izuwa kasanta koda ya dago ludayin sama yayi arba da abunda ke cikinsa sai ya Shuraih Usman inkiya 99% kurma wani uban ihu yai jifa da wannan ludayin
.
Ba wani abu bane yai arba da shi ba face kunne da idanuwan bil’adama nan fa kowannensu ya fara ja da baya, suna kokarin ficewa daga cikin kauyen, jarumi zahakim da sabitul agadawur su kadai ne basu tsorata ba sai kawai suka zare takubbansu suna waige waige domin ganin koda wani abu zai kawo masu hari
.
Kawai sai sukaji wani irin iska mai sanyi ta soma kadawa a wurin nan take suka rika yanke jiki suna bingirewa kasa da bacci,
Daya bayan daya sai da kowannensu ya baje a kasa ya kama bacci a daidai wannan lokaci ne wadansu irin mata na bil’adama suka rika saukowa daga sama tamkar tsuntsaye masu fika fikai, komai nasu irin na bil’adama ne amma sun kasance mayu masu cin naman bil’adama kuma masha huran matsafa babbar cikinsu Shuraih Usman inkiya 99% ke magana yaufa zakusha karatu
Babbar cikinsu na goye da wata karamar yarinya wacce bazata wuce shekaru tara ba aduniya
.
Ita dai wannan yarinya ta kasance kyakkyawar gaske kuma abar kwatance domin suffofinta ma iri daban ne dana wadannan mayu, tunda aka haifeta sai ya zamana cewa bata iya cin komai daga abincinsu, abincinta kawai shine ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki dai kuma kifi bata taba cin nama ba arayuwarta koda kuwa na kifi ne, ana kiran wannan yarinya da suna darisat
.
Gaba dayan mazajen wadannan mayi sun mutu sakamakon yakin cikin gida daya barke tsakaninsu da matayen nasu, bayan an gama yakin ne matan suka kashe dukkan wani da namiji komai kankantarsa, daga wannan rana ne mahaifiyar darisat ta karbii shugabancin kauyen gaba daya alokacin tana dauke da tsohon cikin darisat, don haka ana jira aga abinda zata haifa idan namijine a kashe shi, Shuraih Usman inkiya 99% idan kuwa macece sai a taya ta murnar mai gadonta
.
Tuna a ranar da aka haifi darisat aka dunga ganin abubuwa na al’ajabi a tattare da ita domin aljanu ne suka yi hidimar ta har izuwa ranan sunanta, bata taba shan nonon mahaifiyarta ba aljanu suke kawo mata wata madara ta musamman suna shayar da ita , tun uwar darisat tana jintsoron wadannan aljanun har ta daina ta saki jiki da su , lokacin da darisat ta cika shekara shida sai wadannan aljanu suka ce da mahaifiyanta
.
“Duk abinda kuke nema a duniya zaku samu albarkacin wannan yarinya, daba don ita be da gaba dayanku ba zaku taba samun nasarar zama a wannan dajin ba, kuma duk abun da take bukata a rayuwarta ayi mata shi komai tsananin wahakarsa, kuma kada ku kuskura ku bata mata rai kasancewar wannan yarinya an haifeta da wata irin baiwa wadda bazata musaltu ba” yayin da Shuraih Usman inkiya 99% mahaifiyar darisat taji wannan batu sai ta kasance mai tsananin lura da duk abunda darisat take so da wanda bata so, kuma ta sanarwa da gabadayan mayun dake wannan kauyen, kowannensu ya zamo mai tsananin kiyayewa da lura game da al’amarin darisat
.
Daga wannan rana darisat ta samu karfin sihirin tsafi ajikinta mai yawan gaske, kuma ta rinka shigar dashi a jikin mahaifiyarta wanda shine abu na karshe da tayi nadamar yi arayuwarta saboda halayensu ya banbanta, saboda ita sarauniyar mayun wato mahaifiyar darisat ta kasance azzaluma kuma maketaciya sabanin darisat wadda ta kasance mai tausayi da jinkai don babu abinda ta tsana a arayuwarta sama da al’adar su ta cin naman bil’adama
.
Lokacin da sarauniyar mayu da makarrabanta suka yo kasa tare da yiwa su jarumi zahakim kawanya sai sarauniyar mayu tayi nuni da hannunta izuwa Shuraih Usman inkiya 99% garesu nan take sarkar tsafi ta daddaure su duka tamau faruwar haka keda wuya sai gaba daya matan mayun suka kama shewa da murna, don sun san sun samu lagwada zasu sha romo da farfesu na bil’adama ita kuwa darisat sai ta kamu da tsananin bakin ciki musamman data dubi su jarumi zahaki na yadda suka jigata suka sha wahala
.
Take sai tausayinsu ya kama ta har kwalla ya ciko idanunta kawai sai ta ruga izuwa cikin dakin mahaifiyarta ta zauna tana kuka, a wannan lokaci ne sarauniyar mayu ta dubi dukkan mayun dake wannan kauyen tace
“Tunda dai muna da abunda zamuci a yau mu adana wadannan mutane da muka kama sai gobe mu tsakuro wasu daga cikinsu mu dafa muyi kalaci da su” tana gama fadar haka sai ta dubi wadannsu mayu su ashirin wadanda suke gadin wannan kauyen masu kama da mazaje, tace dasu “ku zuba ido akan yata darisat, Shuraih Usman inkiya 99% domin kuwa zata iya yin yunkurin salwantar da wannan abincin da muka samu” tana gama fadar haka sai ta tafi can wata katuwar bukka wadda acan ne fadarta , fadawanta suna take mata baya
.
Al’amarin darisat kuwa lokacin da ta zauna a cikin daki tana kuka har izuwa wani lokaci mai tsawo sai wani bakin aljani ya bayyana agabanta ya duka ya kwashi gaisuwa sannan yace “ya shugabata akan wanne dalili zaki rika zubda hawayenki mai daraja haka, alhalin muna nan kewaye dake?”
Yayin da darisat taji wannan batu sai ta dago kai ta dubeshi a lokacin hawaye ke shatata a idanunta, tace “ya ra’asul-nauwasu ka sani cewa babu abin da na tsana sama da wannan muguwar halayya ta iyayena wato cin naman bil’adama, tunda suke kama mutane ban taba ganin wayanda na taba tausaya mawa ba sama da wadannan mutane da suka kama, kuma na kudiri Shuraih Usman inkiya 99% aniyar sai na ceci rayuwarsu duka da nasan cewa bani da tabba shin samun nasara”
.
Lokacin da aljani Ra’asul Nauwasu yaji wannan batu sai ya jinjina kai yana mai ajiyar zuciya yace “ya shugabata kin sani cewa akwai ka’ida da sharadi tsakaninmu da mahaifiyarki da jama’arta kuma duk sun cika wannan sharadi da ka’idar abinda kike so kiyi yanzu zai sabawa al’adarmu da kuma addinunmu na tsafi domin kuwa babu yadda za’ayi ki kubutar da su face kin hallaka mahaifiyarki da kanki, shin zaki zabi baki ne akan mahaifiyarki wadanda baki san su ba kuma baki da wata alaka da su? Ki sani izan kika aikata wannan abu zamu juya maki baya mu ya keki, domin kaman kin hallakamu ne” koda aljani ra’asul nauwas yazo nan a zancensa sai ya bace tamkar bai taba wanzuwa ba awurin Al’amarin daya dugunzuma hankalin darisat kenan ta fada cikin kokonto da wasi wasi kuma ta dada fashewa da matsanancin kuka
Shuraih Usman inkiya 99%
.
Bayan su sarauniyar mayu sun gama yin walima da wannan abincin na naman bil’adama da suka dafa afadarta sai kowa ya watse ya tafi iuzwa bukkarsa,
.
Lokacin da sarauniyar mayu ta isa cikin bukkarta dare ya raab,kawai sai ta iske darisat a zaune tayi tagumi tana shishikar kuka,cikin fushi sarauniyar mayu ta daka mata tsawa,”yanzu ke ashe bazaki sauya wannan halin banzan naki ba, ta yaya kike tsammmanin zaki hanamu gabatar da Al’adarmu da muka gada tun iyaye da kakanni, to ki sani akan hakane muka kashe gaba dayan mazajenmu,kema badan kinci darajar aljanun damuke bautawa ba da tuni na hallakaki, duk da cewa ke yata ce da cikina,ina mai gargadinki da kada ki kuskura kice zakiyi wani abu da ba dai dai ba,kisani nasa dakaru su zuba idanu akanki” koda jin haka sai sarauniyar mayu ta tafi izuwa kan gadonta ta kwanta, bata dauki wani dogon Shuraih Usman inkiya 99% lokaci ba sai wani bacci mai nauyin gaske yai awon gaba da ita har tana wani irin munshari tamkar ana gigarawa wani bajimin sa wuka
.
Al’amarin su jarumi zahakim kuwa tun sa’adda wannan iska mai sanyi ta kada suka bingire kasa suna bacci, basu farkaba sai da gari ya waye, koda suka bude idanunsu suka tsinci kansu a daure cikin sarkoki sai hankalinsu ya dugunzuma ainun nan fa suka kama kokarin kwance sarkar dake jikinsu sai suka kasa, jarumi zahakim ya budi baki da nufin yayi addu’a sai yaji bakinshi ta kulle, nan fa shi ya diamauce ya tabbatar da cewa babu abun da zai kubutar dashi a wannan wuri face ikon Allah, a dai dai wannan lokaci ne sarauniyar mayu suka fir fito daga cikin bukkokinsu suka nufo inda su jarumi zahakim suke da zuwansu sai sarauniyar mayun ta kama zagaya su tana lallatsa su domin taji wanda Shuraih Usman inkiya 99% yafi tsoka da mai, wani lokacin har tsikarinsu take da tsinin farcenta tana laso jini ta tsotsa, nan take ta zabo mutum goma daga cikinsu har da sabitul agadawur nan take suna ji suna gani aka dandanne su aka fara yi musu yankan rago
.
Kaico mutuwa bata da dadi, tashin hankali ba’a samasa rana koda su jarumi zahakim sukaga anayiwa yan uwansu irin wannan kisan gilla sai suka dimauce wasu suka kama kuka wasu kuwa take suka some, shi kuwa jarumi zahakim wanda yayi imani da Allah da mutuwa sai ya rungumi kaddara, a lokacinne ya hada idanu da darisat bisa ga mamakinsa kawai sai yaga hawaye yana malala daga idanunta, Al’amarin dayai matukar bashi mamaki kenan ya kura mata idanu itama haka hakika idan ajali yai kira ko babu ciwo aje haka dai aka gama yanka su sabitul agadawur aka daddatsasu aka watsa cikin tukunyar girki, har izuwa wannan lokaci su jarumi Shuraih Usman inkiya 99% zahakim na cikin fama da yunwa da kishirwa kuma babu wanda ya dubesu da idon rahama bare a basu koda ruwan sha makurwa daya, haka dai aka gama duka abunda za’ayi agurin aka watse ya rage saura darisat ita kadai a tsugunne a wajen tana kallonsu cikin tausayawa, koda taga babu sarauniya awajen kuma babu sauran fadawanta sai ta mike tsaye ta dauki wani karton tulun ruwa taje ta fara baiwa jarumi zahakim ya tara hannayensa biyu yana sha
.
Koda dakaru masu tsaro suka hango abinda ke faruwa sai suka taso da sauri da nufin su kwace tulun ai kuwa sai darisat ta nuna su da hannunta na hagu, take wata irin iska mai karfi ta daga su sama ta rinka katan tanwa da su suna masu kurma ihu koda saraunyar mayu da sauran fadawanta suka jiyo wannan ihu sai suka rugo da gudu izuwa waje suka hango abinda yake faruwa
Shuraih Usman inkiya 99%
Nan take zuciyar sarauniyar mayu ta kama tafarfasa tamkar zata kone cikin tsananin fushi ta dubi dakarun nata tace “ku dauko wannan wanda ta baiwa ruwan ku kawoshi dakina na da kaina zanyi gadinsa kuma gobe da safe shine mutum na farko da za’afara yankawa
.
Wannan shine abun daya faru gasu jarumi zahaki da tsohuwa shafhila wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa kogon darul yamzin
.
Al’amarin zuhaisa kuwa bayan ta bace daga inda ta bar su huzainu da zabbabu, bata bayyana ako’ina ba sai dakin tsafin boka ahakamul bainun ta same shi yana zaune akan wani katon buzu na fatar damisa yana gabatar da wani aikin sihiri, don haka sai ta nemi wuri ta zauna tana jiran ya gama wannan hallarar Zuhaisa ta dauli wani dogon lokaci tana jiransa amma yaki ya tsinke abinda yake yi ya saurareta Shuraih Usman inkiya 99% ana cikin haka sai taji zuciyarta tana tashi alamar kamar zata yi amai, sai kawai ta ruga izuwa wani sako ta ci gaba da kwara ra amai baji ba gani, bayan ta idar da wannan amai ta nutsu sai ta koma gefe daya wanda a wannan lokacin wata kasala ta kama gaba dayan jikinta, al’amarin da yai matukar dugunzuma hankalinta kenan nan take taji gabanta ya fadi data ayyana a ranta cewa “ta samu juna biyu” domin kuwa duk wasu alamomin dake bayyana ga mace wacce take dauke da ciki sun bayyana a gareta
.
Yayin da zuhaisa taga wannan zancen zucin ya addabi zuciyarta sai ta shiga bangarenta ta kama bincike babu ji babu gani zuhaisa ta kwarara wani uban ihu da kururwa ta fara iface iface ba wani abu da gani ba face anbunda zuciyarta take ayyana mata ya zamo gaskiya, tabbas ta samu ciki da boka ahakamul bainun nan take ta taji ta tsani Shuraih Usman inkiya 99% bafa ni ba Boka ahakamul bainun nake nufi kawai sai zuhaisa ta mike tsaye zumbur ranta abace ta tunkari boka ahakamul bainun wanda har a wannan lokacin yana nan kamar yadda ta barshi zaune akan wannan buzu na fatar damisa
.
Zuhaisa ta zare takobinta ta dagata sama ta sare kan boka ahakamul bainun nan take kan boka ahakamul bainun ya cire fit daga jikin wuya, jini yai tsartuwa da feshi a bango, sannan gangar jikin ta sulale kasa, zuhaisa ta goge jinin takobinta ajikin gawar boka ahakamul bainun, ta maida takobin cikin kufenta, nan dai ta shiga shirye shirye ta hada nata ya nata, ta kwashe duk wasu abubuwa masu amfani na tsafi dana dukiya tayi awon gaba dasu tana mai nausawa izuwa cikin daji
.
Hakannan taci gaba da tafiya tana tunani da sakar zuci, innda ta ayyana aranta lokaci yayi wanda yakamata ta kafa daula ta kanta, domin ta sami nutsuwa da Shuraih Usman inkiya 99% kwanciyar hankali ta fara dandanar jindadin duniya, lokacin da zuhaisa ta shafe kwanaki arba’in da hudu tana tafiya cikin alkaluman rage nisan tafiya sai ta hango wani babban birni gabanta wanda tun daga nesa ya burgeta, ita kanta kofar shiga birnin ta isa abar kallo domin an yi tane da zallar karfen lu’u lu’u
.
Zuhaisa ta cigaba da tunkarar wannan birni fuskarta cike da annuri, koda ta iso bakin kofar ta iski masu gadi, wadansu girda girdan samari su shida sai sukayi mata kallon raini, babban cikinsu ya dubeta awulakance yace
“Ke kuma wace ce, shin baki san dokar wannan birni bane har da zaki zo mana a irin wannan lokaci?” Koda jin wannan tambaya sai zuhaisa tayi murmushi kuma ta turbune fuska tace ba’ayi mini doka kuma ba’ayi mini ka’ida akan dukkan al’amari kawai ku bude mani kofa ko kuma yanzunnan na gama da ku”.
.
Koda wadannan dakaru sukaji wannan batu Shuraih Usman inkiya 99% sai suka bushe da dariya kafin daya daga cikinsu ya kara fadin wani abu sai zuhaisa ta daka tsalle ta sa takobinta su duka ta sare musu kawuna alokaci guda, suka zube kasa matattu, kawai sai tasa kafa ta banke kofar shiga birnin, take kofar ta tun buko daga cikin kasa ta fadu akas, zuhaisa ta kunna kai cikin birnin tana tafiya cikin takama da izza
.
Ashe akwai dakaru dayawa asaman ganuwa suna kallon abunda ya faru bata sani ba kawai sai suka jehi mata raga ta lullubeta, kafin tayi wani yunkurin fita daga wannan raga, sai suka diro sukayi mata rubdugu suka tumurmusheta da karfin tsiya,
Suka zuba mata sarka ahannu da kafa, sannan aka tasa keyarta izuwa fada
.
Fada ce kasaitacciya wadda ta kawatu ainun da kayan kawa iri iri, komai isar mutum da ikonsa idan ya shigo cikin wannan fada sai an tafi da imaninsa, wani kyakkyawan saurayine zaune akan karagar mulki yayi shigar tufafi na alfarma fadawa da dakaru sun kewayeshi ana tafiyar da harkar mulki, (anya ba Shuraih Usman inkiya 99% bane). Kwatsam sai aka shigo da zuhaisa daure cikin sarkoki, nan take sai kowa ya zuba mata idanu wasu tsananin kyawunta ne ya rudesu wasu kuwa mamaki suke bisa irin laifin da wannan kyakkyawar budurwa tayi da har aka kamota dasa mata wadannan irin sarkoki hannu da kafafuwanta
.
Da zuwa sai aka gurfanar da ita a gaban sarki himali bini auzal aka sanar da shi irin laifin data aikata, nakashe dakaru masu gadin kofa, da kuma karya kofar garin ta shigo batare da izni ba, koda sarki himal yaji wannan batu sai ya dubi zuhaisa cikin mamaki yace “yake wannan budurwa ma’abociyar kyawu da kwarjini mai nene dalilin ki na aikata wannan babban laifi” sa’adda zuhaisa taji wannan tambaya sai ta dago kai ta dubi sarki himal tana mai yi masa wani guntun murmushi tace “Ni ba ayi mini umarni kuma bana bin doka ” koda jin haka sai sarki himal ya fusata ya dubi dakarun da suka zo da ita yace “ku kawar da wannan budurwa mai tsaurin ido daga gabana ku kaita kurkuku ku kulleta, lallai ne gobe da safe zata fuskanci hukunci daidai da abinda ta aikata” nan take dakarun suka dauke zuhaisa suka tafi da ita don cika umarnin sarki
.
.
SHIN ZUHAISA ZATA SAMI NASARAR KUBUTA DAGA CIKIN WANNAN KURKUKU?
.
MENE NE DALILIN DA YASA ZUHAISA BATAYI AMFANI DA KARFIN SIHIRIN TSAFINTA BA A CIKIN BIRNIN SARKI IMHAL
.
SHIN IDAN GARI YA WAYE ZA’A YANKA JARUMI ZAhAKIM A BIRNIN MAYU KUWA?
.
YA LABARIN TSOHUWA SHAFHILA,SHIN ZATA CIKA BURINTA NA TSAYAR DA GABAN YAYANTA KUWA?
.
INA BATUN DAWWARA DA YA TAHO DA NIYYAR ZUWA KOGON DARUL YAMZIN DA NUFIN DAUKO HATSABIBIN ZOBEN ZINARI
.
Maribucin yace muhadu a littafi na Uku 3
Toh jama’a littafi na uku dai bai fito bako imma ya fito toh nidai bana da shi, dun haka sai kuyi hakri mu dan ajjiye wannan littafi a gefe kafin Allah ya kawo wani Da zarar na samu na ukunshi zan cigaba da mazgo maku shi ba kakkautawa bissalam Shuraih Usman inkiya 99%
.
Daga:- ABDULAZIZ S MADAKI
.
Rana da wata
Firgita maza
Kare dangi
Zuciyar jarumta
Rai da ajali
Daren mutuwa
Farautar bayi

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.