Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

RANA DA WATA littafi na biyu 2 part C

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RANA DA WATA
Littafi na biyu 2
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part C
.
.
Koda boka barbushe yaji wannan batu sai ya aika aka kira masa boka kailanu yazo a gabansa sarki barbushe ya dubi boka kailanu yace dashi
.
“Yakai babban boka kailanu, ka sani cewa yan majalisa ta sun shawatce ni da na sanar da kai abinda yake damuna, wanda ina da masaniyan zaka sama mamni mafita akan abinda ya addabeni”
.
Yayin da sarki barbushe yazo nan a zancensa sai boka kailanu ya bushe da dariya ya dade yanayi har sai da yayi mai isarsa, sannan ya daure fuska kamar bai taba fara’a ba a rayuwarsa ba al’amarin daya matukar kidima sarki barbushe kenan ya dubi boka kailanu yace da shi
.
Ina dalilin wannan dariya taka alhalin muna cikin tsaka mai wuya?” Koda boka kailanu yaji wannan batu sai ya sake bushewa da dariya a karo na biyu, sannan Shuraih Usman inkiya 99% ya dubi sarki barbushe yafara da cewa
.
Hakika yakai sarki barbushe ka aikata wani babban kuskure wanda duk wannan wahalhalu da masifu da suke addabarka , sun samo asaline daga sakamakon wani mutum dayazo wannan kasa kayi wa matarsa fyade , wanda saboda haka ne matar tasa ta hadiyi zuciya ta mutu
.
Shi kuma ka koreshi, kasani yakai barbushe wannan mutum yakasance ma’abocin wani bakon Addini ne wanda a duk lokacin da suka roki ubangijinsu yana amsa musu
.
Kuma duk wanda ya kasance daya daga cikin masu wannan addini baya tsoron mutuwa, sun kasance masu tsananin taurin rai da karfin zuciya
Duk lokacin da suka tunkari wani al’amari sai sun cimma burinsu ne a akansa koda kuwa zasu rasa raywarsu ne akan wannan al’amari
.
Ina mai tabbatar maka da cewa idan duk duniya mutane da aljanu zasu hadu, babu wanda yake da ikon fidda kai daga wannan masifa daka shiga , har sai ranar da ka nemo Shuraih Usman inkiya 99% wannan mutum ka bashi hakuri ya yafe maka wannan zalunci da kayi masa, sannan zaka samu nutsuwa da kwanciyar hankali
.
Idan kuwa ba hakaba , to har abada zuciyarka zuriarka sun gama yin sarauta a wannan kasa tamu”
Yayin da sarki barbushe yaji wannan batu sai ya kamu da tsananin tsoro da fargaba , hankalinsa ya dugunzuma ,
.
Nan take ya sulalae kasa a sume, bai farfado ba sai da boka kailanu ya yayyafa masa ruwa sannan, koda sarki barbushe ya sake hada idanu da boka kailanu sai ya fashe da kukan takaici, sai a wannan lokacin ne yayi nadamar al’amarin daya aikata da kansa
.
Yana mai yin danansanin kasancewarsa azzalumi mara tausayi, da boka kailanu ya fahimci sarki barbushe, sai yai duba zuwa gareshi yana mai cewa da shi
.
“Ya kai sarki barbushe hakika na tanadar maka mafita kan wannan lamari abisa Shuraih Usman inkiya 99% sharadi guda, “
Sa’adda sarki barbushe yaji wannan batu cikin tsananin kagauta ya dubi boka kailanu yace
“Maza ka sanr dani wannan sharadi, komai wahalansa ina mai rantsuwa da karagar mulkina zan kiyaye koma me ake bukata”
Boka kailanu yace da shi
.
Muddin kana so danka zaftalarutu ya gajeka da dukkan jikokin ka su cigaba da sa da sarautar kasar nan har abada, dole sai ka dauko sandar tsafin da kakanka marutun-asmar ya sana’anta ya ajjiye a cikin wannan dogon daki tsafinsa daake cikin gidan sarautar nan koda sarki darbuza yaji wannan batu take hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe, yai sunkui da kai kas yana nazari, zuwa can ya dago kai ya dubi boka kailanu yace da shi
.
“Ka riga kasani kakana ya fada cewa bayana mutuwarsa babu wanda zai samu nasarar dauko sandar nan dayin amfani da ita sai bayan shekara dari, kuma duk tsananin naci da kwadayin mallakar wannan sanda babu irin wanda Shuraih Usman inkiya 99^ mahaifina bai yiba har ya rasa rayuwarsa da ya matsa bisa dole sai ya mallaki wannan sanda da aka ajjiye a dogon dakin nan
.
Saboda haka ni na hakura ba zanyi wani yunkurin cewa lallai sai na mallaki wannan sanda ba , kuma zzan ci gaba da neman inda dakalansu ya shiga a duniya na bashi hakuri bisa zaluntarsa danayi, na kuma fadaa masa cewa nayi matukar nadama akan abun da na aikata masa”
.
Tun daga wannan rana sai ya kasance al’adar sarki darbuza itaxce duk sa’adda ya samu labarin wasu baki sun sauka a kasarsa, sai ya tambayesu ko suna da masaniya akan inda dakalansu yake a duniya
.
Sai da sarki barbushe ya share wata daya cif ya tabbatar wa kansa cewa tasa ta kare sai ya wanda a wannan lokaci ya kankance a kowace rana , har takai cewa har takai ramewarsa takai ya zama kamar yaro Shuraih Usman inkiya 99% dan shekara hudu,
.
A wannan lokacin kuwa baya gane duk mutanen dake zuwa kansa
A wata ranar lahadi aka wayi gari da safe sarki darbuza ya mutu, aka nada sarki zaftalarutu ya dare akan karagar mulkinsa
.
Ita dai wannan sanda ta sarki marutul asmar ya sana’anta, ta kasance hatsabibyar gaske, duk tsananin karfin tsafin kowane boka ya kasance ya na mai matukar shakka da jin tsoron duk wanda yake tare da ita, domin kuwa duk irin tsafin duk irin tsafin da akayiwa mutum da zarar an buga mai ita a take zai warke kamar babu abinda ya taba samunsa,
.
Haka kuma kowanne tsafi baya tasiri ga duk wanda yake tare da ita wannan shine dalilin dayasa sarki marutul asmar ya gallabi duk matsafan duniya , suka kasance masu shakkarsa da bin duk wani umarni nasa”
.
Lokacin da Shuraih Usman inkiya 99% da boka gayyar yazo nan a zancensa sai dawwara ya dubeshi ta cikin wannan masaki dake a gabansa yace
.
Yakai boka gayyar shin yanzu ya za’ayi na mallaki wannan sanda , alhalin shekaru dari da sarki marutul asmar sai sun cika za’a samu damar daukota lokacin bai zo ba?”
.
Koda jin wannan batu sai boga gayyar daga cikin wannan masaki ya fashe da dariya ya dade yanayi kamar ba zai dainaba, al’amarin da ya karfafawa dawwara karfin zuciya kenan kan ya dada zage dantse, duk rintsi da tsanani sai ya mallaki wannan sanda boka gayyar yace
“Yakai dawwara ka sani cewa kwanaki goma da suka gabata wannan wa’adi ya cika, zaka iya bin duk wata hanya da zaka yaudari sarki zaftalarutu ya baka dama ka shiga cikin wannan dogon daki
.
Zaka tarar tun a farkon wannan daki a kwai wani katon akwati wanda tsayinsa da Shuraih Usman inkiya 99% girmansa yakai wani katon dakin da za’a iya sa mutum dubu a ciki a kwai katuwar kofa da zaka gani a jikin akwatin ka sa hannu ka budeta, tun kafin ka shiga cikin wannan akwati sai ka dauke gaba dayan numfashinka har tsawon dakika dari da sittin kuma kada ka kuskura wannan lokaci yayi batare da ka samu nasarar dauko wannan sanda ba , domin kuwa mutuwa za kayi ba za’a sake tada labarin rayuwarka ba naka ta kare kenan
.
Duk irin abubuwan ban tsoro da al’ajabin da zaka gani kada ka tsorata ko kadan ka nutsu kana mai yunkurin aikata abunda ka shiga wannan akwati domin yi” koda dawwara yaji wannan batu take yai sallama da boka gayyar ya koma ga sarki zaftalarutu ,
Sarki zaftalarurtu yana ganin dawwara sai ya tareshi yana mai tambayarsa akan wannan bincike da yayi
“Ya shuraih Usman inkya 99% dawwara ya labarin wannan bincike naka, shin an dace ko kuwa dawwara yai murmushi sannan yace,
.
“Hakika al’amarin wannan dogon daki da kakanka yai hani da cewa kada a kuskura a shiga cikinsa sai bayan shekau dari da mutuwarsa, abisa bincikena na gano akwai wani babban al’amari a cikin wannan akwati wanda duk duniya ni kadai zan iya shiga wannan daki na gano maka ko menene mahaifinka bayao ka gani sai wannan wa’adi ya cika”
Yayinda sarki zaftalarutu yaji wannan batu take ya amince da duk bayanan dawwara kuma ya hakikance kan cewa zai iya duk abinda ya fada
.
Sarki zaftalarutu yaja hannun dawwara yakaishi har gaban wannan dogon dak, sarki zaftalarutu ya tsaua a bakin kofa batare daya kusanci akwatin ba. Shi kuwa dawwara sai ya danna kai ciki ba tare da fargabar komai ba, da farko sai da Shuraih Usman inkiya 99% ya shaki iska mai yawa kafin ya shiga sannan ya tinkari wannan katon akwati da boka gayyar ya labarta masa,
.
Dawwara ya sa hannu ya bude kofar shiga cikin akwatin mai kamar kofa ta wani katon gida, lokacin da dawwara ya shiga wannan akwati nan take ya samu kansa a wani katon fili daga can gabansa ya hango wani katon gida don haka ya tunkari gidan yana mai gaugawa da azama domin ya samu sa’ar dauko sandar kafin wa’adin daka diba masa ya cika
.
Dawwara yana fara tafiya sai yai arba da wata wuta ta nufo shi gadan gadan ata kona shi bai damu ba yaci gaba da tafiyarsa ya keta ta cikin wannan wuta ba tare data kona shi ba
.
Haka kuwa kafin yakai wannan gida wani katon zaki ya taso masa yana gurnani zakin ya bude zago zagon kaifunsa ya dako wani wawan tsalle da niyarra ya taushe dawwara ya halakashi, koda dawwar yaga wannan bajimin zakin sai ya kauda kai ga Shuraih Usman inkiya 99% ga barin kallonsa, yayin da wannan zakin yazo dab da shi batare da yaji tsoronsa ba, take zakin ya tarwatse ya zama kasa
.
Sa’add dawwara ya kusan zuwa wannan gida sai yaga wata kyakyawar yarinya tsirara ta nufo shi tana mai kiransa gareta, yayin da dawwara yakalle ta sau daya bai sake kula ta ba har ha kasara kofar wannan gida yasa hannu ya bude tare da shiga ciki
.
Lokacin da dawwara ya shiga wannan gida sai kawai yaga ana ta harbo masa ruwan kibiyoyi ta ko ina ba adadi, anan ma baiyu ko gezau ba , sai ma ya dada sauri yana mai kusantar hatsabibiyar sandar da yazo dauka, a lokacin daya gana rataye a jikin bangon wannan gida daya shigo
Duk kibiyar da tazo sai ta keta jikin dawwara ta fita ba tare da cutar da shi ba
.
Dawwara yasa hannu ya dauki wannan sanda gaba dayan wannan gida yadauki raurawa yana girgiza kamar zai Shuraih Usman inkiya 99%. Zai tsage gida biyu, kuma adai dai wannan lokaci ne dawwara ya soma galabaita sakamakon dadewar dayayi bai shaki numfashi ba,
.
Nan take ya soma tangadi kamar wanda yasha giya sai kawai ya ruga a guje yana mai tsala gudu da tsananin karfinsa domin ya samu ya tsira daga halaka, dawwara yana fara wannan gudu sai yaji wannan sanda tayi masa wani irin nauyi dayaji bazai iya cigaba da daukarta ba , don haka ya saketa,
.
Sandar tay wani haske, nan take ta rikide ta zama wata irin guguwa mai tsananin karfin gaske, ta dauki dawwara ta fito dashi daaga cikin wannan a gabasu sarki zaftalarutu, take wannan guguwa ta sake rikidewa a karo na biyu ta zama sanda, dawwara ya shaki numfashi sannan ya lura da sarki zaftalarutu dayake tsaye akansa yana kallonsa
.
Koda sarki zaftalarutu yaga dawwara tare da wannan sanda sai yasa hannu da niyar ya kwace wannan sanda, kamar anyi wa wannan sanda umarni take sai ta hannun sarki zaftalarutu da tsananin karfin gaske,sarki zafatalarutu yai ihu da kururuwa da karfi, kuma wannan ihu da yayi shi ya janyo hankalin dukkan dakarun da ke kusa suka yo ca domin ganin halin da sarkinsu yake ciki
.
Lokacin da dawwara yaga dakaru sunyi masa kawanya sai ya kyalkyale da dariya yasa hannu ya shafi wannan sanda dake hannunsa, nan take sai sandar ta rikide ta zama wata sharbebiyar takobi mai tsananin kaifi da tsini, kuma a wannan lokacin ne gana dayan dakarun sukayi kukan kura suka abkawa dawwara da niyyar suyi masa kwab daya su halaka shi
.
Wohoho! Masu iya magana sunce duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi’ dawwara ya kasanayana mai kai sara da wannan sharbebiyar takobi dake hannunsa yana tsarge dakarun sarki Shuraih Usman inkiya 99% zaftalaruti cikin dan kankanin lokaci sai ga dawwara ya kashe gaba dayan dakarun da suka taru akansa, shi kansa dawwara sai dayayi matukar mamakin yadda akayi wannan al’amari yake kasancewa a gareshi, aduk lokacin dayakai sara sau daya sai yaga dakaru fiye da dari sun fadi kasa ko ya saresu koma bai saresu ba
.
Koda dawwara yaga haka sai ya takure ya zabga wata tsawa mai karfi wadda ta kidima duk ilahirin mutanaen dake kasar nan
Sarki zaftalarutu ya zare takobinsa ya tari dawwara ya sare kansa, sa’adda dawwara yaga sarki yayo kansa sai ya jefe shi da wannan sanda , sandar ta tafi tana mai tsala gudu, tana matsewa sarki zaftalarutu, take taci da kai masa suka ba kakkautaw,
Tun sarki zaftalarutu yana karewa har takai ya gaza kare kansa, daga karshe sandar ta rikide ta zama wata doguwar takobi ta sare kan sarki zaftalarutu ya fadi kasa matacce,
Dawwara ya shafi wannan takobi take ta rikide ta koma wannan sanda , sannan ya jefa sandar a sama nan take sandar ta tsaya cak,
.
Shuraih Usman inkiya 99%
Dawwara yai tsalle daya tare da darewa saman sandar take suka bace daga shi har wannan sanda gaba daya
!!! ***
Yayin da jarumi zahakin da su tsohuwa shafhila suka tabbatar da sun kubuta daga sharrin wadannan maridai, sai suka ci gaba da tafiya suna masu tsananin sauri da azama , bayan sunyi nisa a wannan tafiya , sai suka yada zango a wani katon fili, abinda ya matukar daure masu kai shine wajen a cike yake da manyan ramuka birjik ba adadi,
.
Daya daga cikinsu ya dubi wadannan ramuka cikin tsananin frigici da tsorata yace da ragowar abokan tafiyarsa
“Anya kuwa wadannan ramukan ba za’a rasa wani mugun abu a cikinsu ba koda jin haka sai zahakim yai murmushi yace
!!!!!!!!!!!!!!!!!!
!!!!!!!!!!
!!!!!!!
!!!!!
!!!
!!
!
.
Shuraih usman

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.