Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

RANA DA WATA littafi na biyu 2 part B

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RANA DA WATA
Littafi na biyu 2
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part B
.
.
Lokacin da zuhaisa ta bace sai zabbabu ya dubi huzainu yace dashi,
“Yakai jarumi huzainu hakika ba karamar kiyayya ke tsakaninka da wannan yar uwa taka ba , kasancewar naga tana neman halakaka ta kowwace hanya .
.
Ina mai kyautata zaton ta hada kai da manyan bokaye hatsabiban gaske, saboda haka nake shawartarka daka biyoni izuwa kasata wadda can na tabbata zuhaisa bata da ikon shigowa har can da niyyar ta cutar da kai”
.
Koda huzainu yaji haka sai yace da zabbabu
“Yakai zabbabu ka sani bana shakka kojin tsoron duk irin makircin da zuhaisa zata shirya mani, ka sani zuhaisa ta kasance tun muna yara kanana bama ga maciji da ita, har izuwa lokacin da kowannenmu karfi yazo masa daga nan kuma sai muka shiga farautar juna da son hallaka juna
.
Hakika zuhaisa ta kasance azzaluma mara tausayi Shuraih Usman inkiya 99% ko kadan wannan shine dalilin daya sa ba ma shiri da ita sam, saboda na zamo mutum mai sanyin rai da taimako ga mutane mara gata a kasarmu, hatta mahaifiyarmu bata jin dadin irin wannan matsananciyar gaba dake tsakaninmu, amma na daukarwa kaina alkawarin duk lokacin da zuhaisa ta sake zuwa gare ni a bisa mummunar aniyarta a kaina , sai na halaka ta ba zan taba bari taci gaba da rayuwa ba muddin tana nan kan bakarta”
.
Daga nan suka kama tafiya cikin daji zabbabu yana mai yiwa huzainu jagora har suka dauki hanyar da zata sada su kasar gayyar inda a yanzu zabbabu yake sarauta
.
. *** .
Dawwara yana tafe kan wani ingarman doki yana mai tsananin tsala gudu kamar zai tashi sama , baya saurarawa komai a wannan muhimmiyar tafiya tasa,
.
Tun bayan da boka gayyar yaga ma shiryasa ya ba shi wata alkyabba ta tsafi yasa sannan SHurarih Usman inkiya 99% ya bashi wasu guraye ya daura su a dantsensa, sannan ya kama tafiya baji babu gani wanda ayanzu ya shafe kwanaki arba’in yana tafiya batare daya hadu da wani mugun abu ba kan hanyarsa
.
Dawwara ya daukarwa kansa alkawarin cewa duk rintsi da tsanani ba zasu taba hana shi yaje kogon darul yamzin ba, don dauko wannan hatsabibin zoben zinari da boka gayyar ya labarta masa ba
.
Lokacin dawwara ya fahimci yabar nahiyar kasarsu ya shiga wani yanki daban inda babu yadda za’ayi a samu wanda ya sanshi
Dawwara yana cikin tafiya akan hanyarsa sai yazo wucewa ta wata kasa mai girman gaske, take dawwara ya kayatu da wannan kasa nan da nan ya ayyana a ransa cewa bari ya shiga wannan kasa ya yada zango kafin wayewar gari ya dan huta yaci gaba da tafiyarsa,
.
Lokacin da dawwara ya shiga wannan kasa sai ya tarar dukkanin mutanen kasar sun taru a wani Shuraih Usman inkiya 99% katon fili daka shata layi, sarki zaftalaru ibini barbushe, yana zaune akan karagarsa ta mulki yana kallon duk abinda yake faruwa a wannan fili
.
Wasu karti ne majiya karfin dantse da murdewar jiki, wani kato daga cikinsu zai tsaya ya mike hannayensa sama , sannan sai wasu karti su ashirin suyi ta dukansa ta dukansa tsawon rabin sa’a batare da yayi koda gezau ba, sannan sarji zaftalarutu ya sa abashi dukiya nai tsananin yawan gaske ya koma gefe daya
.
Lokacin da dawwara yazo wannan waje sai masu gadi suka tare shi suka hana shi ya karasa wannan fili daa wadannan karti suke tada gwanjinsu ana basu dukiya mai tarin yawa, yayin da dawwara yaga haka sai ya fusata matuka, take ya sa dokinsa ya rika banke dakarun yana kusantar wannan fili,
.
Dawwara bai tsayay ba sai da kure a tsakiyar filin saboda karfin dokinsa daya Shuraih Usman inkiya 99% sakarwa linzami batare daya bukaci ya tsaya
.
Sarki zaftalarutu yaji hayaniya ta yawaita sai ya hango dawwara yana ta aikin bangaje masa dakaru , al’amarin daya fusata shi kenan, sai ya bada umarnin cewa a tsaya da wannan gasa ta fada da ake gabatarwa ya daka wa dawwara tsawa ya ce dashi
.
“Yakai wannan mahayi, daga ina ka ke kuma me ya kawoka cikin birni na da har kake bangake mini dakaru alhalin sun haka shigowa inda ake wannan gasa ta fada tsakanin karti majiya majiya karfi ga shi kuma ka kasance baka da siffa irinta jarumai ma’abota karfin damtse”
.
Sa’adda sarki zaftalarutu yazo nan a zancensa sai dawwara ya gyara zamansa akan doki hankalinsa a kwance yafara magana cikin takama da jin cewa shi wani ne
.
“Banzo wannan kasa taka da niyar nayi musayar kalamai da kai ba yakai Shuraih Usman inkiya 99% sarki ma’abocin zafin rai da shisshigi” yayinda dawarra yazo nan a zancensa sai kawai yaga wadannan karata majiya karfi sunyi masa kawanya kowannensu yana ta dukan kirjinsa suna tada kwanjinsu sarki zaftalarutu ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi dawwara yace dashi
.
“Tunda tsautsayi da karar kwana suka sa ka shigo wannan fili batare da an umarceka ba sai kayi fada da wadannan karata idan kayi nasara kansu shi kenan, izan kuwa ka kasa tabuka komai hakika yau sai dai uwarka ta haifi wani ba kaiba”
.
Sa’adda sarki zaftalarutu yazo nan a jawabinsa sai ya koma ya zauna akan karagarsa ta mulki ya harde kafafuwansa yana mai kallon yadda dawwara zai kare tsakaninsa da wadannan karata
.
Dawwara ya sauko daga kan dokinsa ya fuskance su yana mai nazarin wadannan karata da duk motsi na su, kamar an Shuraih Usman inkiya 99% umarci wadannan karti sai su duka saukayi kukan kura da wani mai zafin zuciya dake kan gaba , ya fara dunkule hannu da niyyar ya zabtarewa dawwara baki ya zubda masa dukkan hakoransa,
.
Koda dawwara yaga tahowar wannan hannu zuwa kan fuskarsa sai ya bari sai da hannunsa ya tsakumi wannan kato yai hajijiya da shi ya watsar dashi wani ya sake taso masa shi ma yayi saurin tararsa tun kafin ya iso gareshi ya daga shi gaba dayansa sannan yai wurgi da shi
.
Cikin dakika dari sai gashi dawwara ya watsar da fite da rabin wadannan karti, batare da sun samu sa’ar koda zunguransa ba, al’amarin da ya matukar burge sarki zzaftalarutu kenan, yaga dawwara ya kasance bashi da siffa irinta sadaukai, amma gashi ya kasance yana mai watsar da karata majiya karfin damtse wadanda daya daga cikinsu ma baya kwatanta aikata wannan aiki da wannan bako yazo daga wata kasa Shuraih Usman inkiya 99% ya aikata musu ba
.
Sai kawai sarki zaftarutu ya cika da tsananin mamakinn wannan lamari na dawwara nan take sai ya ga ai yanzu ne ya samu dama da zaiyi amfani da dawwar domin cikar burinsa da ya dade yana hada wannan gasa saboda dashi
.
Nan take sarki zaftarutu yai umarni ga dukkan mutanensa da dakarunsa cewa kowa yatafi abinsa wannan gasa ta kare kenan,
Dawwara ya cika da matukar al’ajabin faruwar wannan lamari, sai ya dubi sarki zaftalarutu da niyyar yayi magana
.
Sai sarki zaftalarutu ya daga masa hannu alamar su kebe akwai abunda zasu tattauna akansa, koda suka kebe sai sarki zaftalarutu ya sake duban dawwara dakyau yana mai sake nazarinsa ,
.
Lokaci da dawwara yaga irin wannan duba take sai ya aiyana aransa koda wannan sarki yayi niyyar ya cutar da shi, hakika sai yake shi ya kasheshi da gaba dayan jama’arsa
Toh nine dai Shuraih 99% ke typing umje zuwa wai …..
.
“Kasani yakai wannan bako mai girman sha’ani na dade ina hada wannan gasa daka tarar anayi anan kasar tawa ne saboda wata bukata ta dana dade daita a raina ban taba fadawa kowa ba, kuma ko su mutanen wannan kasa tawa basu san dalilin daya sa nake hada su fada da juna ba, wannan ni kadai ne na sani sai kuma kai yanzu da zan sanar dakai kasancewarka jarumi uban jaruman wannan kasa tawa
.
A cikin gidan sarauta ta akwai wani dogon daki da mahaifina yabar mani wanda tun mutuwarsa yabar wasiyya da gargadi agareni kan cewa kada na sake nace zan shiga wannan daki sai bayan mutuwarsa da shekaru goma
.
Hakika yau wata tara kenan da cikar shekaru gima da mutuwar mahaifina “sarki zaftalarutu ya gyara zamansa sannan yaci gaba da cewa
.
“Saboda haka nake so ka shiga wannan daki ka gano mani kome ne yake tsoratar dani aduk lookacin danayi yunkurin Shuraih Usman inkiya 99% sannan sai acigaba da hajijiya dani ana bugani adukkan bangwayen dake wannan dogon daki har na ga kawai an watsoni waje a sume sai bayan wani dogon lokaci sannan na farfado
.
Yakai wammam jarumi ina mai neman hadin kanka daka shiga cikin wannan daki tare da gano min meye mahaifina ya aajiye acikin wannan daki da har ya gargadeni da kada na fadawa kowa da kuma kar na sake na shiga har sai bayan cikar shekara goma”
.
Yayinda sarki zaftalarutu yazo nan a zancensa sai dawwara yace dashi,
“Kabani dakika dari zanje nayi bincike da gano yadda wannan al’amari sannan na warware maka komai game da wannan dogon daki
“Dawwara ya kebe can waje daya nesa da inda sarki zafatarutu yake tsaye ya dauko wani katon masaki yasa wani farin garin magani acikin ruwam da ke cikin wannan masaki sannan ya rufe idanuwansa ya soma kiran sunan Shuraih Usman inkiya 99% boka gayyar bayan dakika sittin sai ga fuskar boka gayyar ta bayyana a cikin wannan kaskon dake gaban dawwara
.
Boka gayyar ya fashe da dariya yana mai kyakyatawa ya tari numfashi dawwara yace da shi,
.
“Kasani yakai dawwara hakika zaka jefi tsuntsu biyu ne da dutsi daya, saboda wata ajiya ce acikin wannan daki da sarki zaftalarutu yake magana, kuma muddin ka mallaki wannan ajiya to zata matukar taimaka maka akan hanyar ka ta zuwa kogon darul yamzin tun can wani zamani mai tsawo daya wuce anyi wani kasaitacce kuma azzalumin sarki wanda sunansa ya watsu agaba dayan duniya kowa ya san da shi wanda ake kira da suna barbushe
.
Sarki barbushe ya kasance yana da karfin runduna da matsafa da suke akarkashin mulkinsa ance komai hatsabibancin bokayen wannan zamani ba’a taba samun wanda ya hada ido da sarki barbushe face idanunsa sun tsiyaye ba Shuraih Usman inkiya 99%
.
Wata rana sarki barbushe yana aune a fada ana fadanci kwatsam sai ga wani mtum da matarsa sun shigo fadar, koda sarki barbushe yaga wannan mata dake tare da wannan mutum sai yaga tunda yake a duniya bai taba ji ko ganin kyakkyawar mace mai cikar halitta sama da ita ba
.
Nan take sai ya kamu da tsananin sonta ya shagaltu da kallonta har sai data tsargu, bayan wannan mutum yayi gaisuwa gaban sarki barbushe sai ya sake dukawa yace,
.
Yakai wannan sarki mai daraja ni da matata mun sauka a wannan kasa takea ne da niyyar mu yada zango anan kafin gobe da safe muci gaba da tafiya zuwa inda muka nufa”
.
Yayinnda sarki barbushe yaji wannan batu sai ya sa aka basu masauki a cikin gidan sarauta, al’amarin daya daurewa duk mutanen dake fadar kai kenan suka cika da tsananin mamaki akan wannan al’amari, take sai sarki barbushe ya tashi ya shiga cikin gida, fada ta watse kowa Shuraih Usman inkiya 99% gabansa
.
Jama’a suna masu al’ajabi cewa yau gashi sarki barbushe ya sauki baki har acikin gidansa abinda tunda yake a arayuwarsa bai taba barin wani mutum ya shigo kasar sa da wani abu na dangin dukiya ba face ya amsheta, baya barin kowacce mace mai kyau muddin ya kyalla idanuwansa akanta sai ya biya bukatarsa da ita indai tayi masa, sannan hankalinsa zai kwanta
.
Sa’adda dare ya raba sai sarki barbushe yayi shiri ya tafi bangaren da wannan mutum yake suka kadaita sannan yace da bakon
“Ka fadi duk iya tarin dukiayr da kake bukata a gareni, ina mai rantsuwa da darajar iyayena zan baka ita muddin zaka bar mani wannan kyakkyawar mace da ka kira da sunan matarka”
.
Yayinda bako dakalansu yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma, ya dimauce jikinsa ya kama karkarwa wata gumi ya Shuraih Usman inkiya 99% karyo masa kawai sai ya kara dukawa a gaban sarki barbushe yace
.
“Yakai wannan sarki kayi sani cewa ni a addinina haramun ne wani abu ya shiga tsakaninka da matata ta sunna,
Ma’ana ba zan iya mallaka maka matata ba, wannan babban laifine awajen ubangijina”
.
Koda sarki barbushe yaji wannan batu sai ya bushe da dariya al’amarin daya matukar girgiza dakalansu kenan hankalinsa ya kara dugunzuma fiye da farko
.
Sarki barbushe ya juyo a fusace ya dubi wadansu dakarunsa dake tsaye a gefe day yace
“Ku kama shi ku daure shi, kuma kuje ku fito mini da matar tasa, nan take dakarin suka cika wannan umarni
.
Dakalansu yanaji yana gani agaban idanuwannsa yayi wa matsarsa fyade, al’amarin dayasa matar ta hadiyi zuciya ta sulale a kasa matacciya kenan, shi kuwa dakalansu sai ya fashe da matsanancin kuka na bakin ciki ya kama hailala yana mai kai Shuraih Usman inkiya 99% kukansa ga Allah
.
Sarki barbushe yasa dakarunsa suka tasa keyar dakalansu ana dukansa anayi masa korar kare har aka fitar dashi daga kasar
.
Tun daga ranar da aka kori dakalansu, sai masifu da bala’u iri iri daban daban suka addabi kasar taimara, sai masifu da bala’u iri daban daban suka addabi sarki barbushe cikin kwanaki shida sai daya kasance an rasa gane abinda yake damun sarki barbushe har takai cewa baya iya fita ko ina har takai cewa mutanen kasar sa suna tsananin tausaya masa abisa wannan al’amari
.
Lokacin da sarki barbushe ya fahimci ya shiga tsaka mai wuya , sai ya tara gabadayan yan majalisarsa domin su shawarce akan wannan lamari, daya addabeshi, koda sukaji haka, sai kowannensu ya fada cewa lallao sai ya aika a kirawo masa boka kailanu shi kadai zai iya gano dukkan abinda yake damunsa yayin da sarki barbushe……….
.
Kai wallahi nagaji bazanje nayi cajin wayata
.
Toh anan zan tsaya sai mun hada bayan kwana biyu
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99% ma shafin Hausaebooks da
Keffians News Teller

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.