Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

TASKU part 9

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


Upload : 25 Jul 2017 – 19:12
Size : 155 kb _______________________________________
— TASKU
————————————————————–
__kirkirarren labari_____________________
—-daga Shuraih 99%——————————
Part 9
.
.
Ina zaune bisa wani kujera, na yi zurfi cikin tunani
.
“Assalamu’alaikum” naji muryar Abbana
.
Umma ta ce ta amsa mai sallamar , ko kallon inda nake baiyi ba ya wuce izuwa dakinsa
.
Ina ganin haka nace a zuciyata yau dea zanje na ba Malam hakuri, inma wani laifin na mai a iya sanina ni dai nasan babu laifin dana aikata masa,
.
Na tashi na nufi cikin dakin nasa, sallama nayi na shiga na iske shi a zaune bisa kushin a tsakiyar falonsa,
Ya amsa sallamar amma kansa aduke yana danna waya,
.
Na durkusa bisa guiwowina a gabansa nace ” Malam kayi hakuri, bisa abin dana aikata, duk da bansan abin dana aikatan ba, tunda na taso a gidan nan baka taba fushi da ni ba sai wannan karon
Sannan kuma fushin iyaye masifa ce ga yayansu, don Allah malam ka yafeni, kaine komaina a rayuwa kamin komai”
.
Sai asannan ne yadago kai ya dubeni “ni baka batamin rai ba, illa dai kawai abu daya , malam shuraihu (sunan da babana ke kirana da shi kenan) shin me ya hadaka da wannan yarinya sannan kuma a cikin tsohon dare,
Ta yaya zaka nemi ka bata sunan wannan gida namu , dukkan mutanen wannan angwan suna ganina da kima da mutunci, “
Yadanyi ajiyar zuciya ,
Sai a sannan ne na fahimci inda maganan Malam ya nufa,
Yaci gaba da cewa” shin yaushe ka watsar da tarbiyar dana baka , shin yaushe rudin duniya ta fara debarka, kodai MUGAYEN ABOKAI ke maka hudubar shaidan, sam sam bazan yadda ka batamin suna a wajen mutane ba” yafada cikin bacin rai
.
Na dubeshi sannan nace”Malam ba abin da kake tunani bane , babu wani wanda ya’isa ya gurbata wannan tarbiyar daka bani sai Allah, dayar dar Allah bazan taba jawo maka zagi wajen mutane ba,

Nan na fede wa babana biri har wutsiya, sannan na kara da fadi mashi cewa ni ina Sonta da aure ne bawai da wani nufin ba
.
“Alhamdulillah Alhamdulillah dama mu abin da muke so kenan , tuntuntuni nake ta yi dakai akan kayi Aure amma sam kaki toh yau kam babu wanda ya kaini farin ciki bisa wannan zance daka sanar dani, yar gidan wacece”
Nan na dan susa keya ” bansan sunan mahaifinta ba amma zan…..”
Sallamar da mukaji ne ya dakatar da zancena,
Mahaifiyata ce ta shigo dauke da farantin abinci ta ajiye farantin mai dauke da kuloli biyu da kuma cokula a saman wani dan karamin gilashi mai kirar teburi, wanda akayi dama don hakan ,”
.
******** *********** ******
Ina tafe bisa mota ta kirar 406, wani sauti na saka , sai tashi yake yadda kasan wani club ,
,
Pakawa nayi a gefen titi sannan na kira wayan mjd,
.
Bayan ya dauka ne na sanar dashi yanzu haka ina kofar gidansu ina jiransa,
,
Baifi minti biyar ba da ajiye wayata, sai gashi nan ya fito, yana zuwa ya shige gidan baya ya zauna. Na duve shi” malam kasan ni ba direban kabane koh”
.
Murmushi yayi sannan yace” ok zaka basu labari badai ni ba ,muje zuwa…”
Ya fito ya dawo gidan gaba kusa dani, nan na tashi motar muka hau hanya,
,
“Ya baba ina muka nufa” yafada dai dai lokacin dana sharo wata kwana ta wani babban gareji,
“Ba saidaka zan ba,kaji don haka ka kwantar da hankalinka” na fada yayin da hankalina ke wajen tuki
.
Har muka iso gidan bai ce dani ufFan ba mun karisa ciki sannan na kira wayarta,
,
Bugu daya Tadauka anan na sanar da ita ina gidansu, inajin lokacin da ta sa shewa, sai kuma tace dani na kariso dama mahaifinta yana so yai magana dani,
,
******* ********** *******
Rantsatstsen falone wanda ya amsa sunansa , mahaifinta yana wani babbar kushin maicin mutane akalla goma , sai kuma ita Rufaidan tana gefensa
,
Nida mjd zaune bisa wani sofa mai cin mutum uku zuwa hudu, mun fuskanci juna da mahaifinta,
,
“Yaro tabbas ka ceto yata daga shiga wani hali na rayuwa, sannan ka ceto martabar wannan gida,ni nama rasa da wata kalma zan yi amfani da ita wajen yi maka godiya,na gode yaro, shuraihu kake ko shuraiha” mahaifinta yafada yayin daya ke dubana,
.
“Shuraih ne sunan baba, sannan basai kayi mini godiya,ai wannan ba wani abu bane tamkar kanwata haka take ,ka dai gode ma Allah mai kowa mai komai,”
,
Wayarsa ce tayi kara nan danan ya daga magana sukayi daganan yace damu shi zai tafi izuwa wani taro da aka kirashi na gaggawa,
.
Bayan tafiyarsa ne na dubi Rufaida wani zunzurutun sonta ne ke kara shiga cikin zuciyata,
,
Toh anan ne na tambayeta ya akayi har wayannan karti suka kawota cikin wannan kwarin da kuma dalili
.
Nayi mata wannan tambayar ne don kawai naji sautin muryarta wanda ya kasance mai zakine tamkar zuma,
,
Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dubemu ni da mjd tafara bada labarin kamar haka
“Mahaifina……..
Ku biyoni a part 10
Its Shuraih 99%
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч @Shuraih Usman

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.