Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

TASKU part 7

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


_______________________________________
— TASKU
————————————————————–
__kirkirarren labari_____________________
—-daga Shuraih 99%——————————
Part 7
.
.

Wasu murdamurdan karnukane su biyu, jikinsu sur gashi, girman kowani dayansu yakai girman kosashshen rago, baki bude suka nufo mu suna haushi,
,
Sam sam karka dauka wai ina jin tsoron karnuka ,
Toh ni da anguwarmu ma cike yake da karnuka
.
Toh amma da nai arba da wayannan kosasssun karnukan sai da hantata ta kada , domin ban saba ganinsu ba
.
A dai fina-finan indiya da america ina ganinsu, toh amma a zahiri dai yaune mukayi kicibis dasu
.
Koda wayannan karnuka suka fara kusanto mu
Sai rufaida ta rude ta tsuguna a kasa ta rufe fuskarta,
.
Haryanzu wukar dana cire a kugun katonnan yana hannuna ,
Nan na kara damkeshi da kyau tamau,
.
Karnukan suka daka tsalle a lokaci daya suka fado jikina , a sannan ne suka mangareni na fadi akasa,
.
Rufaida na ganin hakan sai ta taso daga tsugunen data ke ta dauki wani shirgimemen dutse,
Tayi nasarar jefar kare guda da wannan dutsen sai dai , dutsen bai jimata rauni ba,
.
Karnukan dukkansu suka juya izuwa kanta, na tabbata izan har suka, isa gareta , lamari ya baci
.
Cikin sauri na yi gudu na wawuri kare daya na yafa da kasa sannan na caka mai wuka a kafarsa daya, nan ya kwanta sai shureshure yake, dayan karen na ganin haka, sai ya dubeni sannan ya nufo ni cikin gudu
.
Koda ya rage baifi zira’I kadan muhadu ba sai ya daka tsalle ya fado jikina yasanya gaba daya farcensa a gefen wuyana bakinsa kuwa wadda take wangame tana saitin maqokwarona, nufinsa ya fasa makoshina da fikarsa
.
Koda na fahimci manufarsa, sai na yunkura don na yi cilli dashi amma naji na kasa sakamakon dannenin da wannan karen yayi,
.
Karfin tsiyane da shi, da kyar na tureshi daga jikina,
.
Sannan na bishi na kama bakinsa na caka mai wukar a tsakiyar ka har sai da ta fito ta cikin bakinsa nan take yafadi kasa matacce,
,
Na nufi wajen rufaida wacce tagama tsorata da wayannan karnukan
.
Nakama hannunta muka tashi tsaye,
Toh a daidae wannan lokacin ne al’amarin ya faru,
Wani radadine ya ziyarce kafata, na’zata ko zarto ne aka sa za’a yanke kafar, sai a sannanne idona yai arba da dayan karennan ya damfara wa kafata cizo,
.
Na janye kafata daga bakinsa, na dan rarrafa, ina cikin rarrafen ne naji hannuna ya taba wani abu ,
.
Bakomai bane illa guntun bulo, ji nayi saukar karennan a ruwan cikina,
.
Ai ban tsaya wata bata lokaci ba na rarumi wannan bulo din na maka masa aka,
Nan yayi gefe, ya bingire a kasa koda naga haka sai na tashi, na hau ruwam cikinsa, nai ta maka masa wannan bulo din aka har sai da bulo din ya juya izuwa gari,
,
Sai a sannan ne hankalina ya dawo jikina na yunkura na mike tsaye ,
,
******** *********** ********
,
Munyi tafiya mai nisa a cikin wannan daren,
Har muka iso daidai wajen wani gada wanda a akasar wannan gada ba komai bane illa wani katon kogi, shi wannan kogin ana mai lakani da mahannu,
.
Muna zuwa daidai gadan na turje sakamakon kafata data ke yimin wani mugun ra dadi,
.
Na dubi rufaida na ce da ita, “duk da mun kasance muna cikin halin tashin hankali, toh wannan bazai sa na gagari furta miki sakon zuciyata ba”
.
Ta dubeni cikin alamun rashin fahimtar inda zance na ya nufa
“Tun lokacin dana fara ganinki, lokacin da idanuwa sukai arba da wannan kyakyawar fuskar taki, tun a sannan wani mashi mai dauke da dafin sonki ya ca keni a kahon zuciyata,
Kece kawai maganin wannan dafin sam sam wannan lalurar dake jikina bai dameni ba,
Don muddin akan kine zan iya, sadaukar da rayuwata,
Kisani Rufaida I NA SONKI,
Bawai so na fatan baki ba sannan bawai so irin na mayaudara ba , ke wata ginshikice na a cikin rayuwata”
Ina gama fadin wannan kalmar na bingire kasa sumamme.
Daga nan bansan kome ya faru dani ba
,
.
Ku biyo ni a part 8 .
.
Its Shuraih 99%
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч @Shuraih Usman

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.