TASKU part 6

 TASKU part 6
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Nov, 2017
Upload Time 9:21 pm
Hits 137 Hits
Comment No Comments

Description


_____________________________________
— TASKU
—————————————————-kirkirarren labari________________
—-NA Shuraih 99%———————–
Part 6
.
.

Koda wayannan karti hudun suka ga abinda nayi wa dan’uwansu sai suka zaburomani tamkar zasu cinyeni danye
,
Zobe suka yi mani sannan muka fara kallon kallo tsakanina dasu,
,
Yadda kasan giwaye ne suka sa cinnaka a tsakiya haka sukaimani, wani garjejen kato daga cikinsu ya rarumeni yadaga sama sannan ya tika da kasa,
,
Ai nan naji tyamkar, kashin bayana ya karye, na kwala ihu ,
Koda ganin hakan sai daya daga cikin kartin ya dubi wanda ya kwada ni da kasa yace
“Yanzu sisini maza je ka duba lafiyar Gogo, “
Wanda aka kira da sisinin najin haka ya nufi wajen katon dana barar dazu da dutse
,
Ya dagashi daga kwancen dayake, sannan ya zaunar dashi,
.
Sukuwa cikon ukun sai suka fara dumfaro inda nake kwance , koda na farga da su sai na cika hannuwana da kasa,
Daidai wani kato ya kawomani naushi sai na tsuguna ya naushi iska, kafin yakai ga juyowa na watsa mai wannan kasar dana diba cikin hannuwana acikin idanunshi,
,
Nan ya tsaya turmus sai karkade idanu yake,
.
Nan take kuma idanuwana suka kai ga mararsa inda ya soke wata wuka irin na yan daban nan kafin yan’uwansa suyi wani yunkuri, tuni har na zare wukar a mararsa ,
A samam makoshinsa na sanya wukar sannan nayiwa yan’uwarsa barazanar, cewa in suka kariso gareni toh tabbas zan yan kashi,
.
Koda suka ga haka sai dukkansu suka fara ja da baya ,
.
Nima ina ganin hakan na dubi wannan budurwar da haryanzu take kwance gashin kanta a barbaje, sannan bakinta na fidda jini
,
Nace mata” tashi mu tafi”
.
Nan ta mike ko dankwalinta bata tsaya daurawa ta nufo bayana
.
“Kana jefa kanka a cikin matsanancin tashin hankali, lallai kasani muddin ka aikata, abin da kake yunkurin aikatawa toh lallai, sai kayi dana sani , alokacin da dana sanin bazai yi maka amfani ba
.
Murmushin karfin hali nayi sannan nai duba ga budurwarnan na ce mata ta fice daga cikin kogon
.
Shi kuwa katon dana sanya mai wuka a makoshinsa ko kwakkwarar motsi ba yayi , a tunaninsa a kowani loka ci zan iya danna hannuna wukar ya lume cikin maqokwaronsa,
.
Jansa nakeyi muna tafiya har muka kawo bakin kogon a sannan ne na juya na dubi yan’uwansa, “Lallai kada kuyi gangancin fitowa daga cikin wannan kogon , domin muddin kuka fito kuwa wannan dan’uwankun sai de wani ba shi ba”
Na fada cikin gargadi garesu.
.
Nan suka dakata sai muzurai suke,
,
Maimakon mu haura saman kwarin ta inda na gangaro wato ta bakin titi, sai muka haura ta dayan gefen inda zai bulla dani gidajen mutane,
,
Duk wannan tafiyar da mukayi ban yadda ko da wasa na kauce da hannuna daga saman makoshin wannan katon ba.
.
Muna haurowa saman kwarin sai na bankaje katon , nan take ya fada cikin kwarin da mirgine,
.
Ban tsaya wani bata lokaci ba na kama hannun wannan budurwar wacce bana iya , ganin fuskarta, muka ci gaba da gudu,
.
Gudu muke wanda ko waiga bayanmu ma ba mayi, nan wannan budurwar ta yi tuntube da wani gwangwani ta fadi,
.
Sai a sannan ne na tsaya na lura da wajen da muke, muna wani faffadan filine , wanda ciyayi suka dan tsiro kadan kadan a gefen mu na dama wani babban gidane na kece raini
.
Gaba daya jikin bangon wannan gida a lillike take da kwayakwayai lantarki, wayanda suka haske kofar gidan,
.
Hasken kofar gidan ne ma ya dan haska wannan faffadan filin da muke ciki,
.
Nan na duba a gogon wayata, 2:25,
Tun danake ban taba ganin musifa irin wadda naganta a yau ba ,
.
Danai duba izuwa wannan budurwar sai naga ita ma ta mike ,
.
Hasken nan ya haska mani fuskarta, Turus kawai nayi yayin da kaina ya kusa juyewa,
.
Na dan muntsili hannuna wai ko mafarki nake, tabbas a zahiri ne
.
Kamar ko yaushe fuskarta sai sheki yake a yayin da wasu siraren hawaye ke gangarowa ta saman kumatunta,
Sirara kebbanta sun rine da jan baki,
.
Ba wata bace face RUFAIDAH
Yarinyar dana Zuzuce akanta
,
Ita ma na fuskanci ta ganeni sabida yanayin da fuskarta ta nuna,
,
Hau hau hau hau
Naji daga gefena ina juyowa nai arba da su,
,
Wasu murdamurdan karnukane su biyu, jikinsu sur gashi, girman kowani dayansu yakai girman kosashshen rago, baki bude suka nufo mu suna haushi,
,
Tir kashi anyi gudun gara an………
Inji hausawa
,
Wai karya ta kare bori taci boka
Tobe continue
,
Its Shuraih 99%
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч @Shuraih Usman

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: