TASKU part 5

 TASKU part 5
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Nov, 2017
Upload Time 9:20 pm
Hits 165 Hits
Comment No Comments

Description

_____________________________________
— TASKU
—————————————————-kirkirarren labari________________
—-NA Shuraih 99%———————–
Part 5
.
.
Wannan shine tambayar dana yiwa zuciyata.
,
Toh ma mezai dameni koma dai wanene ke wannan kuka babu abinda ya shafeni
.
“Tai mako jama’a! Babu wani bane yazo ya taimakeni!” Naji wata murya na fadi, ta cikin surkukin kwarin dake gefena,
Tabbas wannan muryar mace ce , sannan kuma duk yadda akayi tana cikin wani haline
.
Ban tsaya wani dogon tunani ba na fada cikin kwarin ina fadawa na cigaba da gangarawa,
.
Nan na isa cikin wani surkukin ciyayi , toh anan ne Mafarin shigata cikin TASKU ya samo asali
.
Tabbas da nasan ko menene ke shirin faruwa da ni toh da banyi gangancin kara shiga cikin surkukin ba
.
Ina wuce ciyayin nan, na iske wani dan kogo,
batare da wata fargaba ko tsoro ba na danna kai cikin wannan kogon,
.
Na kunna tocila na wayana yayin dana kutsa kai cikin kogon ,
Wannan kogon dai irin ramukannan ne da ake tonawa don neman arziki ,
Babu komai acikin kogon in banda duwatsu da kuma rairayin ciyayi,
,
Ina kara gaba na ja tunga nayi turus sakamakon abinda idanuwana suka gane mani
.
Bakomai nagani ba face wata kyakkyawar budurwa, kwance a kasa, sannan wasu karti, su biyar sun zagayeta,
.
Biyu daga cikin kartin nan sun rike ma wannan yarinya hannu, yayin da wasu karti biyu suka rirrike mata kafafu , a sannan ne wani kato ke kokarin yi mata fyade ,
,
Ita ko babu abinda take illa ihu da karaji da neman taimako,
,
Sudai wayannan karti zasu kai shekaru talatin dukkansu, sannan gaba dayansu sun sanya bakaken kayane, jaket ce baka ajikinta anyi mata Ado da wasu duwatsu na karfe ,

.
Yayin da wayannan karti suka ganni cikin wannan kogon ,
Sai guda daga cikinsu wanda yake kokarin haike ma wannan yarinya ya dubeni sama da kasa sannan yace dani cikin wata murya mai kama dana jaki
“Kai dan tsako ,Ka kama gabanka tun kana numfashi “
.
Koda naji wannan zace nashi sai na juya da niyyar na fice daga cikin wannan kogo ,
Har na fara tafiya sai naji muryar budurwar tana cemani” Malam dan Allah ka taimaka mani, ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka”
.
Najuyo sannan nayi magana yadda zasu iya jina ” kiyi hakuri yar’uwa “
.
“Yanzu da kanwarka ko wata yar’uwarka kaga za aketa mata mutuncinta ,haka zaka juya ka tafi”
Tafada yayin da akarshen maganar tata ta kare da kuka
,
Ban iya mai da mata da amsa ba sakamakon yadda maganar ya shiga cikin zuciyata
.
Kawai sai najuya na fice daga cikin kogon
,
Ina ji tana kirana amma ya zanyi dole ce tasa , domin gaskiya ni ba jarumi bane kuma bana da kirar sadaukantaka a jikina,
.
Toh koma dae menene ai hausawa nacewa sarkin yawa yafi sarkin karfi
,
Ayayin danake wannan tunanin ne naji zuciyata ta fara tafasa, ni kaina bansan lokacin dana juya na koma cikin kogon nan ba
.
Ina zuwa naga wannan katon na kokarin cire mata kaya hakan ne yakara tunzura ni
,
Nan na nemi wani katon dutse na dauka ina zuwa na sami daidai saitin gadon bayansa , na mai dundu, da wannan dutsen, nan ya kife, ,
,
Koda wayannan karti hudun suka ga abinda nayi wa dan’uwansu sai suka zaburomani tamkar zasu cinyeni danye
,
Zobe suka yi mani sannann……

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: