Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

TASKU part 4

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

_______________________________________

— TASKU

————————————————————–

__kirkirarren labari_____________________

—-daga Shuraih 99%——————————

Part 4

.

.

Ai bansan lokacin dana saki baki Galala ina kallonta ba
.

Koda ta kariso gabanmu saita tsuguna ta gaishemu sannan ta fara magana yayin datake dubana
“Kuyi hakuri da abun da nai maku jiya”
Bakina na rawa na ce”ai babu komai ,”
.

“Wallahi jiyannan na rudene sosai shi yasa,kuma na zata Abba zai min fadane shi yasa” ta fadi cikin wata irin murya tamkar bata son fadin maganar,

.

Ta kara dubanmu tace”Sunana Rufaida “

.”Sunana shuraih, wannan koh m….”

Mjd ya katseni yayin daya ke fadin “malam barni na sanar da’ita sunana, “

Dariya kawai mukayi yayin daya cigaba”wai nine zai min lamuni,toh Allah yasa ina da baki “

Nanma murmushi kawai tayi,
“Mujahid ko kice mjd sunan kenan”

.

Na dan harereshi nace”sai kuma akace ka fadamana nickname ko”
.

*******************

Bayan mun yi musayar nombobi nida ita sabida zumunci, daga nan muka rankaya zuwa gidanmu ,sabida cikinmu dake kiran ciroma.

.

Zaune muke muna cin abinci nida mjd anan ne yake sanar dani wani wajen bikin Sallah da zamuje da la’asar wai shi minki,

.

***************

Muna isa bakin get din muka nausa kai ciki sakamakon get din dake bude, anan muka sami wajen parking muka paka motan

.

Samarine da ‘yan mata ke ta zirga zirga a cikin wajen ,yayin da wasu yanmata wayanda suke tare da samarinsu, zaka gansu tare suna hira.

.

Yaune zuwana na farko wannan waje ,dun haka sai na nufi bayan wani bishiya domin na dan huta ,

Wani makeken bencine dakure akusa da jikin bishiyar, saman bencin na dane,

Mjd kuwa muna shigowa cikin wajen naga ya nufi wajen wata yarinya daga nan suka ci gaba da tadin su,

.

Daga wajen danake zaune ina hangen samari da yanmata dake zirzirga a wajen ,wasu gungun samarine da yanmata naga sunyi da’ira a wani kebabban waje, daga inda nake zaune ina iya sauraron sautin gular dake tashi,

.

Na tashi daga inda nake zaune na nufi wajen, koda na isa sai naga ashema yan’mata ne da samari keta gwargwazon rawarsu, sai tika rawa ake, ayayin da Dj ya saki kidan Ado gwanja na asha ruwa
.

****************

Kwata-kwata. Wajen ya gundureni ,zaman wajen ya fita min arai,

Nan naje wajen dana bar mjd tare da budurwarsa suna zance,

Koda na isa wajen ban samesu ba na duba sama da kasa gaba daya cikin minki ban samesu ba.

.
Dana kira wayarsa ne yake sanarmani shi yanzu haka fa babansa ya kirasa, kuma ya nemeni mu tafi bai ganni ba,
.
karfe 11:24pm agogon wayana ya nuna mini, nan take na fito bakin titi ina neman acaba, duk da nasan da wuya na samu acaba saboda dare da yayi,
.
Nafi minti talatin ina tsaye a bakin titin amma ko alamar acaba ban gani ba,duk da wani sa’in mashina da motoci sukan wuce jefi jefi,
.
Nan na yanke shawarar na taka saiyadata har Allah yasa na sami dan acaba,
,
Nayi tafiya mai nisa sosai har na fara gajiya, a sannan ne na iso angwan lambu,daidai gaban gidan rediyon N B S
,na sami wani dakali na dan zauna don in huta daga nan na cigaba da tafiya,

Baccin na hutane na cigaba da tafiya, har na iso wani waje dana duba agogon wayata 1:54 Am

Na danyi tafiya kadan kenan sai naji hayaniyar mutane, sama sama dana dan kara gaba ne na fahimci kamar shishshikar kuka ne ke fitowa ta cikin wani sunkuru,

Karkaji nace sunkuru ka dauka ko acikin dokar daji nake, a bakin titi nake wani wawakeken kwari ne dogo tamkar kwalbet, shimfide a gefen titin
Shi wannan kwari hanyar ruwane idan ana ruwan sama ta ciki yake bi yai wuce warsa, kwarin din cike yake da ciyayi, sannan a saman kwarin gidajene da kuma gidan giya,
Dana dan lura da kyau na kasa kunne sai naji shishshikar kukan na fitowane ta wani restaurant, restaurant din yana saman kwarin ne,
.
Shishshikar kukan ya cigaba da kara hauhawa, nan da nan na fahimci muryar mace ce,
.
Toh shin wacece ke kuka acikin wannan tsohon daren
.
Kubiyoni a part 5
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.