TASKU part 2

 TASKU part 2
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Nov, 2017
Upload Time 9:15 pm
Hits 242 Hits
Comment No Comments

Description


_______________________________________

— TASKU

————————————————————–

__kirkirarren labari_____________________

—-daga Shuraih 99%——————————

Part 2

.

.

Nan ta fara magana tamkar bazata yi ba, ni kuwa babu abin danake sai kallon siraran lebbanta wayanda suka rinu da janbaki,

Wanda hakan ba karamin kyau ya kara masu ba ,

.

Chochulate color ce, doguwa wanda har taso ma ta fini tsayi, duk dana kasance ina da tsayi tamkar bishiyar kwakwa

.

Fuskarta faffadane , idanuwanta dara dara madaidaita, wayanda suka kara fitar da siffar kyauwun fuskar tata,

.

Ma tsakaicin karan hancinta wanda ya taimaka wajen fidda siraran lebbanta,

.
kai mai karatu duk yadda naso na baiyana maka ita saidai na fada amma tafi haka

.

Tana sanye ne da doguwar riga mai hade dankwali yayin data yafa gyalenta, a kafada ,

.

“Kai malam kaduba irin asarar da ka jamini kuma wannan motar batawa bace ta abbata ce , sai magana na ke tayi da kai amma kai sam hankalinka baya tare gareni” na tsinkayi daddadan sautin muryarta cikin kunnena ,

.

.

“Ehhhm ehhm, maganar ma ta gagareni furtawa sai in ina na ke”

.

Na dube ta dakyau sai naga wasu siraran hawaye suna zarya akan kyakyawar fuskannan tata,

.

“Kiyi hakuri , wannan duk laifina ne ” na ji muryar mjd na fadin haka dana duba sai na ganshi a gefena ashe ma ya kariso ni bansaniba

.

“Ni babu abin daya shafeni ko laifin wanene cikinku nidai damuwata a gyaran motata ,”

.

Ta fada cikin murya mai ban tausayi, ai tunima na manta da wani abu waishi yunwa.

muryarta kadai inzan ringa saurara toh ya isa ya gusar min da dukkan wani bacin raina ,

.

“Ok toh indai wannan ne baki da damuwa , yanzu ki shiga cikin motar mu je gun bakanikai na tabbata yanzu dai basu tashi ba”
Inji mjd yayin daya ke dubana

“Kwarai kuwa “nace dashi amma fuskana na duban fuskarta ita kuma tunda tai mani kallo daya ta kau da kanta , ga barin kallona

.

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤. ¤

Cikin wasu mintuna kalilan muka isa wajen bakaniken wanda yake zama a hayin waziri,

Nan dai ya ca jemu wasu kudade, mjd ya ciro ya biya ita kuma ta wuce gida , amma kafin ta wuce ta bamu Address din gidansu akan idan angyara mukai mata motar.

.

Hakan ba karamin dadi yai mini ba ,

Muna isa angwa nida mjd na fito na shige gida zuciyata cike da tunane tunane

**********************

Ina kwance a cikin daki fuskata yana kallon saman silif, zaka rantse da Allah cewa slif din nake kallo, toh Amma hankalina ya tafine ga tunano, wannan sirirriyar sautin muryar wadda da kuma wannan fuskar da bazata taba goguwa cikin idanuwana ba

.

“Shuraih! Shuraih!! Shuraih!!!”
Naji mruyar anas tsulum, nan na mike ina mai dubansa ,cikin mamaki

.

Bawai mamakin ganinsa nake ba a’a yadda akayi har ya shigo cikin dakin bansani ba alhalin ba bacci nakeba.

“Nayi sallama yafi baki goma amma kaki ka amsa mini” na tsinci muryarsa na mai fada mani,

“Kayi hakuri wallahi wani tunanine nake”

.

“Tunanin me”

.

“Tunaninta kake koh” naji muryar mjd , wai ashema tare suke da anas ,

Sam ban farga cewa yana cikin dakin ba sai daya fadi haka tukun

“Wacece ita” anas ya fada yayin daya ke duban mjd,

“Wata beuty ce muka ja mata asara, yau “

Nan ya labarta masa yadda mukai da ita

.

Ni dai sai jinsu kawai nake

Mjd yadan dukeni sannan yace”amma fa 99% kayi dace dun gaskiya yarinyar she is pretty,sai dai zakayi fama da’ita”

.

“Wani fama kuma zan da ita”

Na tambayeshi

.

“Zakayi fama da kuka mayena,dun yarinyar saurin kuka gareta sai kace wata …..”

.bai karisa maganar ba na kaimai dukan wasa,

Nan muka dara

.

.

Wannan labari Goron Sallah ne ga
dukkan Masoyana gaba ki daya

Hop kunyi Sallah lfy

Toh Allah ya maimaita mana

.

Ku biyoni zuwa par 3

Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: