TASKU part 1

 TASKU part 1
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Nov, 2017
Upload Time 9:13 pm
Hits 289 Hits
Comment No Comments

Description


_______________________________________

— TASKU

————————————————————–

__kirkirarren labari_____________________

—-daga Shuraih 99%——————————

Part 1

.

Zaune nake a kofar gidanmu na lankwame kai, kai kace wani sabon uztass ne

Sa’I sa’I nakan kalli danfareren titin dake gabana, da shike gidanmun a bakin titi yake

.

Wani karamin yarone yazo zai tsallaka titin, daidai zai tsallaka kenan sai ga wata mota kirar peugeut, karama ta sulalo titin ,

.

Daganin wannan mota kasan bata da niyayyar sassauta gudun data ke antoyawa,

Nan da nan jama’a suka maida hankalinsu ga wannan mota, shi ko wannan yaro ko da yaga mota ta dumfaro wannan titin gadan gadan, sai ya tsorata ya fada cikin kwalbet
.

Sai daya zo daf da inda nake zaune baki bude ko kwakwaran motsi bana iyayi .

Sannan ya taka birki, nan motar ta bada wata sauti kuuuttt, sannan taci taya akan titin ,

Tsayuwar motar keda wuya sai kofar gidan direba ta bude ,

Tsinin takalmin sane ta fara fitowa sannan shi, yana sanye da karamar riga t-shit a gaban rigar an rubuta da manyar haruffa, MY MONEY GROW LIKE GRASS

Jeans ne ajikinsa sai kafarsa kuwa tsokale duniya ce acikinsa,
,

Duba daya naimai sannan nadan yi wata murmushi wadda tafi kama da yake,

“Baba kunajin dadinku fa” yafada lokacin daya miko mani hannu muka tafa ,

“Amma kana karin magana ne koh, ae ko makaho yazo ya lalubani ya lalubaka toh wallahi sai yaji banbanci” na ce dashi yayin dana matsa mashi ya zauna kusa dani.

.

Na san yazone kawai ya tayani hira daga nan yai wucewarsa

“99% da alamu azumin yau na baka jiki”
.

“Kaman kasani, mjd shiyasa ma na dan fito nan ko zanji dan iska iska”

.

“Maza kazo yanzu muje yawan shan iska”

.

“Allah yasa yawon shan iskokai ne” namai gatse, dun shi mjd arayuwarsa babu abinda ke birgesa sama da yadau wanka ,sannan ya fito yai ta yawo da mota a gari,

.

“Maza damuwana da kai kenan haryanzu baka wayeba”

.

“Toh sannu wayayyu,”

.

Nan dai yata lallabani har Allah ya daura shi akaina na amince masa.

.

Na daga cikin abun daya sa na amince masa don yau kwata kwata jinake tamkar bani bane, tunda aka shiga watan ramadan wata mai albarka,watan da ake gafartawa masu rabo zunbansu, .
ban taba shan wuya naji najaki kamar Azumin yau ba,
. Wani sa’in ma bana sahur,amma haka zakaga nakai azumina batare da wani mishkila ba amma wai sai gashi yau datake ranar da za’mu idar da Azumin wato ranar jajibiri,
shine azumi ke azabtar dani

.

Abinma da zai sake baka mamaki shine yau, bakaramin lodi nayi ba wajen sahur, don sai danaji nakasa tashi daga zaunen danake sannan nabar tusa abincin izuwa cikina.

.

Tabbas naji ba dadi kwarai shi yasa ma na amince ma mjd muka rankaya izuwa cikin Gari

.

.

Sai sulala gudu mjd keyi tamkar zamu tashi a sama .

“Kagani malam muddin bazaka rage gudu ba toh ka tsaya na sauka”

Na fada yayin dana murtuke fuskata
.

Koda ya kalleni yaga babu alamar wasa a fuskata, sai yayi yar dariya sannan yace”kace dai kana tsoro kar na rage ma farashi a wajen yan’mata”
.

“Koma dai menene kace lokacinkane ko kuma nace laifinane dana shiga motarka”

.

KwakkwassssSssss!!!!, muka ji wata sauti ta fito daga gabanmu,

“Subhanallahi”
shine kawai abin dana samu damar furtawa
.

Ashe dai bamu sani ba a lokacin da muke magana , akwai wata farar mota a gabanmu kirar audi, toh itace muka ci karo da ita.

Wannan karar kuwa karar rugurgujewar fitilar baya na motar ne da kuma signa na ta.
.

“Subhanallahi” shine kawai abin dana furta sannan na bude kofar motar na fita dun naga asarar da muka tafka

.

Ina fita wani daddadan kamshin turare ya ziyarci hancina, ,sai dana lura da kyau sai naga tamkar shacin mutum agefena,

.

Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki daya halicci wannan aba , kai kace aljana ce,

,

Ta durkusa a gefen motan tana kuka harda shishsheka, ganina datayi na fito ne yasata mikewa , ta fuskance ni.

Ai anan ne ma naga ashe ni na mata kallon nisa ne
sai yanzu data ke gabana ne na kare mata kallo tsaf
.

.

Wannan labari Goron Sallah ne ga
dukkan Masoyana gaba ki daya

Hop kunyi Sallah lfy

Toh Allah ya maimaita mana

.

Ku biyoni zuwa par 2

Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: