TAKOBIN JINI 4 part A

 TAKOBIN JINI 4 part A
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Nov, 2017
Upload Time 9:12 pm
Hits 1227 Hits
Comment 1 Comment

Description


Upload : 25 Jul 2017 – 19:14
Size : 149 kbTAKOBIN JIN 4!!!
Littafina hudu (4)
Littafin Shuraih Usman
Part 1
.
Wannan macijiya na faduwa kasa take ta fara konewa , nan ta kone kurmus burbushin tokanta, iska ya janyeshi zuwa sararin samaniya,
.
Nan take wannan jeji yafara sauya kala izuwa asalin siffarsa bishiyoyin cikin jejin suka fara fidda ganyayyakinsu wayanda suka bushe , sakamakon zuwan wannan bala’eiyiyar maciyar,
.
Komai a cikin wannan jeji yadawo yadda yake yadda kasan wani bala’I bai taba faruwa ba,
.
Sarki gulmanu yana gefe akwance baisan ma inda yake ba sakamakon galabaitar da yayi a hannun wannan macijiyar,
.
Sarauniya lasmin itama tana gefe a kwance magashiyan,
Hilal ya debo ruwa daga jakansa ya yayyafa masu take suka farka a cikin wani yanayi, gulmanu ne ya mike sannan ya dubi sarauniya lasmin yace “
Ina wannan macijiyar take”
.
Sarauniya lasmin ta budi baki cikin galabaita tace mai” ai daga gani kasan wannan macijiya ta dade da mutuwa, kuma ba kowa bane ya kasheta ba face yarima hilal.”
Jinjina kai kawai gulmanu yayi daga nan bai sake cewa komai ba,
.
Anan suka shafe kwanaki biyar cikin wannan jeji suna maganin raunikan jikinsu akwana shida ne suka yi shiri suka cigaba da tafiya,
.
Kimanin kwanaki uku suna tafiya acikin wannan jeji basu kara haduwa dawata muguwar dabba ba ko kuma wata masifa, har suka fice daga cikin jeji suka doshi dajin fatalwi
.
Da shigansu cikin wannan jeji sai suka ga yanayin jejin tamkar wani kwarine , gaba daya bishiyoyin cikin jejin guntayene sannan marasa ganyayyaki da yawa,
.
Sun yi tafiya mai dan nisa kenan sai suka ga wasu fatalwi su bakwai tafe da wani aljani sun bankare shi suna zuwa dashi,
Su wayannan fatalwin suna da maka makan kawuna da wani sololon kafa wanda yake barazanar karyewa ako wani lokaci,
.
Acikin bakin wayannan fatalwi akwai wasu hakora biyu sun firfito har gaban bakinsu,
.
Koda wayannan fatalwi suka yi arba da su gulmanu sai suka fashe da dariya daya daga cikinsu yace” yauwa kunga yanzu saimu raba gardama, tunda dama muna ta rikici akan wannan aljanin ,”
Dayan shima yace” maganarka dutse dukda baza su ishemu ba amma haka zamuyi maleji da su, “
.
Dayankuwa cewa yayi” na dade ban ci naman bil adama kullum sai aljanu muke farautowa , gashi yau tsuntsu yafado mana daga sama gasasshe,” wanda yafara magana da farko ya mangare na biyun yace” kaini kun fara isata da surutu gashi sai dalalar yawu nake,”
Yana gama fadin hakan ya dubi su lasmin yace ” yaku wayannan biladama kusani yaune karshen rayuwarku a doron kasa, don kuwa dukkanku zamu karkashe ku sannan mu cinye namanku, izan har kuka bamu hadinkai toh zamuyi muku kisan sauki, amma in kukace zaku yi gardama toh da ranku zamu ringa bantalan sassan jikinku muna cinyewa,
.
Sukuwa su sarki gulmanu wayanda suke ganin abinda ke faruwa tamkar a majiki,
Babu abin da ke basu mamaki tamkar wai su bada hadin kai sai kace wasu gaulaye,
.
Yarima hilal na gefe sarki gulmanu ya zaro takobinsa, batare da yayi wani furuci ba ya dumfari wannan fatalwowi da takobinsa tsirara,
.
Itama sarauniya lasmin da yarima hilal take suka mara mashi baya da takubbansu tsirara ,
.
Koda wayannan fatalwowi suka gane nufin su gulmanu sai suka kyalkyale da dariya sannan ko wannensu ya zaro makaminsa,
.
Gulmanu na isa gabansu ya zaro takobinsa cikin tsananin zafin nama ya sari daya daga cikin wannan fatalwi, nan take wannan sara ta sameshi a wuya kansa ya fita daga mahadan wuyansa, wani koren ruwa ya fara fesowa daga dungulmin kan nan take wannan fatalwa ya fadi matacce ,
.
Koda ganin haka sai yan uwansa suka afka ma su gulmanu nan take aka rincabe da mummunan yaki
,
Hilal ya shammaci daya daga cikinsu ya soke sa da wuka a ciki take shima ya fadi matacce , sarauniya lasmin kuwa takaima wani sara ya kare amma sabida karfin saran saida takobinsa ta karye,
.
Ya saceta yai mata dundu a baya nan take ta kife da ciki amma cikin zafin nama da nuna tsagwaron jarumta tayi wani alkafura ta mike tsaye sannan tayi wulli da takobinta koda wannan fatalwa yaga tai cilli da takobinta sai ya nufota yana murmushi, yana zuwa yakaimata naushi ta tsuguna naushin yabi iska kafin ya juyone ta yi tsalle ta kama kansa nan take ta murde kan , take yafadi matacce,
Sauran biyun kuwa da sukaga haka sai suka fita da gudu, suka nausa wani bangare na wannan jeji.
.
Sarki gulmanu ya dubi wannan aljanin da wayannan fatalwin suka kamo sai yaga ashe ya dade da mutuwa ma
.
Yarima hilal ya dubi gulmanu yace mai” Lallai mu hanzarta barin wajennan don na tabbata wayannan fatalwin da suka tsira zasuje su kai labari wajen yan’uwansu kuma tabbas sai sun dawo”
.
“Maganarka dutse amma saide wani hanzari ba gudu ba” gulmanu yafada
Lasmin tace “muna jinka mene wannan”
Gulmanu yayi murmushi akaro na farko yace” ai duk inda zamuje baza mu fita a wannan dajin ba harsai mun fafata da wayannan halittu, dun haka a ganina gwamma mu tsaya mu fafata da su kawai”
.
Yana rufe baki kenan sai suka hango kura ya toshe sararin samaniya wani bakin hadari ya gangama , kuma wannan kurar kara matsowa take kusa da su
.
Duk sai suka maida hankalinsu ga wannan kurar, ai nan take suka fahimci ko menene ya haddasa wannan kurar ba komai bane face , tarin rundunar fatalwi sahu sahu babu iyaka har ba’a ganin karkensu
.
Koda wayannan rundunar suka karaso sai suka dubi su gulmanu sannan wani fatalwa ya fito gaban wannan runduna , da alamu shine babba a cikinsu
.
Wannan fatalwa ya dubesu yace” yaku wayannan biladama kuyi sani cewa kunyi babban kuskure da har kuka shigo cikin jejin, sannan har kuka kashe mani mutane lallai yau zamui maku mugun kisa sannan mu shayar da gunkinmu jininku naman ku kuwa dashi zanyi kalaci gabe da safe
.
Koda su gulmanu sukaji haka sai sarauniya lasmin tace ” kusani ku wayannan fatalwin kun tari karshenku, lallai yau kun gamu da gamonku, kuma yau zaku dandani kudarku, don sai mun dadana maku dacin mutuwa, sannan mu shafe wannan jejin naku, daga doron kas”
.
Wannan fatalwa yai kara kara mai razanar wa sannan ya dubi dakarunsa yace ku kama mun su araye nake bukatansu
.
SHIN YAYA ZATA KAYE
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Copyright (c) Shuraih Usman
Marubuci:- Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

1 responses to “TAKOBIN JINI 4 part A”

  • Pls ina son in karanta part B amma ban ganiba

  • Leave a Reply
    Related Files

    error: Alert: Content is protected !!
    %d bloggers like this: