Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

BABBAN GORO part 1D

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

BABBAN GORO
————————-
Littafina daya
.
Part 1D
.
With shuraih 99%
Typing by :- http://facebook.com/shuraih.usman

.
Al’amarin kifyan sarkin aljanu kuwa wanda gidansa yake cikin karkashin kasa , a tsakiyar ruwa, rabon daya fito tun lokacin daya bayar da tsaron bishmalu dan sarki kan’anu na misra
.
A halin yanzu bishmalu ya zama saurayi dan shekara sahirin da biyar. Kuma a iya tunaninsa bai da wani uba wanda ya fi kifyan , amma bai taba ganinsa ba a zahiri sai acikin madubin tsafi
.
Fitowar sarki kifyan keda wuya aka lullubeshi masu gaisuwa nayi, masu bambadanci nayi shikuma sai ya hau kankaragarsa ta mulki ya zauna , sannan yace aje a zo masa da dansa , nan take aka zo da bishmalu , bishmalu ya durkusa yayi gaisuwa.
.
Kifyan yace” na fito ne domin ganinka , dakuma son gabatar da wani muhimmin zance a gareka , wanda baka san dashi ba , yanzu ne lokacin da zan yi maka bayani ka fahimta tunda ka mallaki hankalin kanka .ya kai bishmalu ka dubi kowa dake cikin fadar nan ka dubi kanka ,zaka ga cewa ba irin kirar halittar ka bane , domin mu aljanune kai kuma bil’adama ne, to kasani kai ba dana bane . iyayenka bil’adama ne kamar kai , ni sato ka nayi tun kana jariri sakamakon laifin da mahaifinka yai mini, ya auri matar dana ke so”
.
Nan take kifyan yai nuni da hannunsa izuwa wani madubin tsafi ! Sai ga hoton sarki kan’anu kwance bisa gado a turakarsa yana jinya.
.
“Wannan shine mahai finka, daga nan zuwa inda mahaifinnan naka yake tafiyar wata da watannice . Kasani ya kai bishmalu son dana kewa mahaifiyarka shine ya dawo kanka a yanzu.
.
Kifyan ya sake nuni da hannunsa izuwa wani madubin tsafi sai ga hoton ashwar bisa doki a dokar daji yana tafiya.
.
“Wannan wani jarumine da ake kira ashwar , wanda ya taho da niyyar fitar dakai daga cikin gidannan ya mai da kai hannun babanka, amma bai san cewa yayi babban kuskure ba , har duniya ta tashi ba wani mahalukin bil’adama daya isa ya shigo cikin fadata”
.
Kifyan na gama wannan jawabi ya tuntsure da mahaukaciyar dariya wadda tasa gidan ya kama girgiza , har sai da ya rufe bakinsa sannan gidan ya tsaya daidai.
.
Bishmalu ya dubi sarki kifyan yace ” ya kai sarkin sarakai badan kada ranka ya baci ba da nace kasa akaini wajen mahaifina mu gana “
.
Cikin fushi sarki kifyan ya mangare bishmalu da iskan bakinsa sannan yace” a kul nakara jin kace na kaika wajen babanka”
.
‘Da nine inba sai ankaini wajena babana ba ko ata masifa 99% ke magana
.
.
“To kasani daga yau duk kimarka ta zube a idanuna gwarama ka kasheni na huta da takaicin abin daka yiwa mahaifina”
.
Kifyan ya sake bushewa da dariya , sannan yadubi fadawansa yace” ku na son wannan yaron ko kuwa na kasheshi yanzunnan?”
.
Gaba daya suka rude da cewa ” muna sonsa ya sarkin duniya”
.
Wannan hayaniya ta fadawan kifyan tasa bishmalu ya firgice ya fadi kasa sumamme,
Nan take sarki yasa akayi wani turare na hayaki , aka fesawa bishmalu ya farfado, sarki ya sake dubansa yace
” Yanzu wakake so mu ko iyayenka”
.
Bishmalu yace” ku nake so, don ku ne kuka reneni , ban san wadan can ba”
.
Koda jin haka sai fada ta rude da shewa , nan take akayiwa bishmalu wanka ya zama dan sarki kifyan, aka yi biki da gagarumat walima , bayan an kare, sarki kifyan ya zagaya da bishmalu cikin fadodinsa guda ashirin da bakwai da ke cikin wannan gida na sarauta, ya nuna masa sirrikansa gaba daya banda sirrin inda ruhinsa yake.
.
Wannan shine abin daya faru tsakanin sarki kifyan da bishmalu dan kan’anu na misra, wanda ke can kwance cikin jinyar rashin lafiya tsawon shekaru ashirin da biyar.
.
.
Shuraih 99% ke ce daku
.
Ashwar na can cikin jeji ya kutsa kai , bai san ma inda yake nufa ba . Kwanci tashi yaje wani gari , yasamu wasu mutane a bakin kofar shiga ashwar ya sauka daga kan ganjarma yayi wa mutanen sallama , sai yaga basu kalleshi ba , ya kuma matsawa yai sallama , kawai sai suk zabura wajen su goma shahudu suka kewayeshi, wani daga cikinsu yace
“Kai yaro mene ne ya biyo dakai ta wannan kofar? Baka sani ba cewa garinnan yana da kofofi hudu amma wannan ta zama mallakinmu? Ba a wucewa ta nan sai anbiya harajinka dana dokinka”
.
Ashwar ya dubesu a wulakance yace” menene kuma haraji?”
.
Wannan batu ya harzuka gudansu, don haka sai ya zagaya bayan ashwar da nufin ya sharara masa mari, caraf sai ga hannunsa a hannun ashwar, ya zaci abin na wasa ne , sai yaji ana rumurmutse masa hannu kamar gyale , mtumin ya ringa ihu da sauran suka ga haka sai suka debi sanduna suka rufe ashwar da duka titim! Titim!! Suna bugunsa sandunan na karairayewa , tamkar akan dutse suke bugawa . Gaba dayansu suka firgita da ganin wannan al’amari, sai suka arce
.
Ashwar ya kada linzamin dokinsa ya shiga cikin gari . Yana cikin tafiya yaga wasu ‘yan mata su shida kyawawan larabawa , sun debo ruwa a tulu daga rafi . Ashwar ya dubi wadda tafi sauran kyawu yace ” ‘yan mata dan Allah taimaka mini da ruwannan mana na sha”
.
Batare da jin kai ko wulakanci ba ta miko masa tulunta, Ashwar ya karba ya kafa kai ya zuke fiye da rabinsa, sannan ya miko mata, sannan yayi godiya .
Sauran ‘yanmatan suka dubeta suka kyalkyale da dariya , wata cikinsu tace
.
“Yanzu ke Asma’u don wahala bata isheki ba shine zaki bayar da kyautar ruwan da kika debo acan nesa da gari , aikuwa mu baza mu koma da baya ba don raka ki debo wani”
.
Nan take suka wucu su kai gaba , ita kuma Asma’un sai ta dora tulunta aka ta juya da baya dan komawa rafi. Koda ganin haka sai ashwar ya sauka daga kan dokinsa yace ta hau , shikuma ya ruke mata tulun , batare da musu ba Asma’u ta hau kan ganjarma Ashwar ya ruke mata linzamin , su kai gaba suna tafe suna hira kai da kagansu sai ka dauka bawa ne da uwargijiyarsa, kasancewar ashwar bakin fata ita kuma balarabiya.
.
Shuraih 99% nake ce daku”Kai kuna tare dani kuwa “
.
“Baiwar Allah shin anan garin kuwa akwai musulmi mabiya Addinin musulunci?”
Ashwar ya tambaya
.
“Kwarai kuwa , fiyr da rabin mutanen garinnan duk musulmine sai de , saidai sarakunanmu azzalumaine , kuma mai karfi shi ke da ikon yin abinda yaga dama , yanzu haka da akwai wasu azzalumai ‘yan fashi da suka addabe mu, shi yasa da zarar magariba tayi kowa sai ya shige gidansa ya rufe kofa , komai zafi ba a isa ayi kwanciyar waje ba , in kuwa mtum ya kwanta a waje saidai da safe a ga gawarsa “
.
Koda ashwar yaji haka sai ya cika da mamaki yace ” Ni kuwa da yardar Allah zanyi muku maganinsu daga yau sun dai na yin fashin”
.
“Haba dan samari wane kai , ai BABBAN GORO SAI MAGOGIN KArFE. Mutanan da sun fi mayakan garin nan ma karfin tsafi da sihiri , ya za kai da su”
.
“To shikenan tunda kina shakka ina so ki amince mini kwana a kofar gidanku”
.
“Wannan mai saukine amma fa duk abin daya sameka kada ka zargi kowa ka zargi kanka”
,
99% ke magana kuna biye dani kuwa
.
Haka dai ashwar da Asma’u suka ci gabada hira har suka je rafi suka debo ruwa suka dawo.
Asma’u takai ashwar gidansu ta gabatar dashi a gaban iyayenta , tare dayi musu bayanin tarar aradu daka wadda yace zaiyi cikin mamaki mahaifin Asma’u ya dubi ashwar da kyau yace
.
“Kai yaro shin rayuwar duniyace ta ishe ka haka ko kuwa wani abin bakin ciki ne yasa kazabi mutuwa akan rayuwa?”
.
Ashwar yayi murmushi yace ” baba babu ko daya amma dai ni nakasance mai son yin fada da karya da kuma azzalumai, na tsani kafirci da zalunci , burina Addinin musulunci ya rinjayi kafirci a doron kasa, bana dogoro ko takama da karfi ko tsafi,face taimakon ubangijina wanda shine masanin dukkan abinda ke fili da boye “
.
Wannan batu yasa jikin mahaifin asm’u yai sanyi yayi shiru daga bisani yace
“To masu magana sunce ba’a kwacewa yaro garma amma wannan garmar da kake shirin dauka tafi ka nauyi sai dai muce Allah yaba sa’a”
.
Haka dai ashwar ya cigaba da hirarsa da Asma’u da iyayenta har rana ta fadi.aka kawo abinci sukaci tare gabadaya , magariba nayi suka yi sallama da shi suka shiga cikin gida suka rufe kofa .shi kuwa gogan sai yai alwala yai sallah a kofar gidan , har ya idar da sallar yayi yan Addu’oinsa baiga wani yazo gare sa ba ,
Ashwar ya debi ruwa arijiya ya baiwa ganjarma sannan yai shimfida. Agefe gida yayi kwanciyarsa tamkar yana cikin dakin matarsa.
.
‘Yan fashinnan da suka saba shigowa sai gasu sun dira akan ashwar kimanin su arba’in ashe Asma’u a soro ta kwanta koda taji magan ganunsu sai ta kwalla ihu take ashwar ya farka , alokacin har daya daga cikinsu ya hau kan ganjarma yana cewa
” Ni kam yau na fito a sa’a na samu lafiyayyen doki”
.
Ashwar ya mike zumbur ya dube su yace ” ku azzaluman bayi me ke tafe daku”
.
Gaba dayansu suka bushe da dariya , dayansu yace
“Yau kuma bakon marar kunya aka samu a garinnan ? Kai yaro yau karar kwana ta kawo ka makasa “
.
Wannan batu ya fusata ashwar nan take ya hausu da duka, gashi babu ko allura agareshi amma su da manyan makamai a hannunsu ya zame musu ala kakai, duk wanda yakai masa sara ko suka sai ya goce cikin zafin nama ya kama hannunsa ya murde ko ya karya. Cikin kankanin lokaci ya zubar da mutum goma kasa sumammu da ‘yan fashinnan suka ga haka sai suka fara jarraba tsafe tsafensu da sihirce sihirce, amma duk suka zama a banza don basuyi tasiri ba akan ashwar , sakamakon Addu’ar daya ke ta karantawa a zuciyarsa , nan fa wuri ya dada ya mutsewa , ihu da kuwwar ‘yan fashin tasa duk jama’ar garin suka bubbude gidajensu suka fito, don ba’a taba jin irn wannan tashin hankali ba a garin . Yayin da jama’a suka taru sai aka iske ashwar tsaye shi kadai a kofar gidansu Asma’u .
‘Yanfashinnan gaba dayansu su arba’in suna kwance cikin jini, wasu a sume , wasu akarairaye. Nan take gari ya dauka da shewa don farin ciki aka yi ta al’ajabin jarumtakar ashwar.
.
Koni nan nafishi jarumta 99% ke magana
.
Ita kuwa Asma’u saita ruga da gudu ta rungume Ashwar tana cewa ta samu mijin aure Mutanen gari sukayi ta kawowa ashwar kyautar dukiya, amma ko daya bai karba ba .
Anan ya sanar dasu labarinsa da dalilin fitowarsa daga garinsu, ya bukaci o akwai wanda yasan inda birnin duma yake .
Gaba daya akayi shiru sai daga can wani dattijo tsoho tukuf wanda duk garin babu mai tsufansa ya dogaro da sanda ya karaso inda ashwar ke tsaye ya dafa shi ya ce
.
“Yaro nasan inda birnin duma yake”
.
Koda jin haka sai farin ciki ya kama ashwar , ya rungume tsohon yana mai matukar farin ciki, daga nan yabi tsohon zuwa gidansa.
.
Daga nan zuwa birnin duma tafiyar shekaru ukune.
Birnin duma garine na aljanu zalla inda sarki kifyan ke mulki” dattijo yafadi tare da ajiye numfashi.
.
Cikin tsananin damuwa Ashwar yayi ajiyar zuciya yace ” hakika duk abin da aka fadi haka yake , amma ni yanzu guiwata tayi sanyi , burina ya yanke ,domin babu yadda za’ai naje birnin duma a cikin kwanankin da aka diba mani wa’adi”
.
Bisa mamaki tsohon ya dubi ashwar yace “ban gane bayanin ka ba “
.
Shuraih ke cewa daku
.
Nan take ashwar yai masa cikakken bayani kan sharadin da sarki Abul dinar ya shimfida masa , kafin ya amince ya aura masa gimbiya mabaruka . Tsoho yayi shiru yana tunani har izuwa wani dan dogon lokaci , sannan yace
“Ya kai wannan jarumi ina da wani dan’uwa wanda zai iya taimakonka a bisa wannan al’amari sunansa raslanu , bawan Allah ne wanda ya kaura daga cikin gari ya koma can jejin surgam yaci gaba da bautar ubangiji, don kada wani abun duniya ya rude shi daga nan zuwa jejin surgam tafiyar kwana goma sha biyuce, amma ka sani akwai ababan hadari a wannan jeji, fiye da shekaru sittin a tarihi babu wani mutum wanda ya keta ta cikin surgam batare da ya zama gawa ba, face wannan dan’uwa nawa wato ruslanu. Shi ma hakan ta farune sabida Allah ya hore masa baiwa mai dumbin yawa . Idan har ka sami nasarar ganinsa , tamkar ka sami nasarar shiga fadar sarki kifyan ne”
.
Ashwar yayi shiru yana nazarin wannan bayani sannan yace ” ya kai wannan dattijo mai albarka , ina tabbatar maka da cewa ko zan rasa raina sai naje jejin surgam na sadu da wannan dan’uwa naka Ruslanu, kuma gobe goben nan zan yi shiri na tafi
.
Ashwar na rufe baki suka jiyo tambura sun cika gari , cikin sauri suka fito daga cikin gidan, kawai sai su kai arba da mutane jingim akasa , sun rako wani doki guda daya izuwa ga ashwar , ba kowa bane akan dokin face Asma’u ta sha kwalliya da ado irin na amare, cikin mamaki ashwar ya tambaya
“Me ke faruwane”
.
“Ai an daura aurenka ne da Asma’u , yanzu haka amaryarka muka kawo maka”
Mahaifin Asma’u ne da kansa tabada wannan amsar
.
.
Laifin dadi karewa
Abdulziz sani m/ gini ke ce daku
Kash! Mai karatu anan zan dakata sai mu hadu a BABBAN GORO KaSHI NA BIYU don mu ji yadda zata wakana
.
SHIN JARUMI ASHWAR ZAI YADDA DA WANNAN AURE DA AKA YI MASA BATARE DA NEMAN AMINCEWARSA BA?
.
ME ZAI FARU YAYIN TAFIYARSA ZUWA JEJIN SURGAM?
.
A CIKIN WANI HALI GIMBIYA MABARUKA TAKE AYANZU?
.
SHIN ALJANIN BOKA GULMANU KUTUNTUMA NA BIYE DA JARUMI ASHWAR KUWA?
.
TA YAYA ASHWAR ZAI SHIGA BIRNIN DUMA HAR YA SHIGA FADAR SARKI KIFYAN YA DAUKO BISHMALU?
.
Toh Alhamdulillah dama tun kafin nafara na sanar daku cewa book 1 ne kadai akasa
.
Sai kun jini a sabon littafi
$ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
,
Tweets:- https://mobile.twitter.com/Shuraih_Usman?p=s

.
.

.νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.