Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

BABBAN GORO part 1C

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

BABBAN GORO
.
Littafina day (1)
.
Part 1C
With shuraih 99%
.
Typing :- http://facebook.com/shuraih.usman

.
Ashwar ya kwance wannan dattijo , sai ya hangi wasu dakarun sun bullo da kwari a hannayensu. Ashwa ya yunkura yai alkafira izuwa inda dokinsa yake , ya ciro mashinsa ya rike a hannu daya yana majajjawa da shi . Dattijo ya koma bayansa ya buya . Dakarun nan suka sako ruwan kibau , ashwar yai ta kadewa da mashin hannunsa , har kibiyoyin nasu suka kare , sai suka zare takubba suka yiwo kansa anan nefa ashwar yayi tunanin yazama wajibi yayi amfani da makami.
Don haka sai ya matsa jikin dokinsa ya dau takobin nan nasa zabbau , nan fa wuri ya yamutse, barade na kai masa sara da suka yana karewa , shi ma yana kai musu , sai da aka sami sa’a guda ana wannan fafatawa sannan ya karar da su.
.
Koda ya waiga bayansa sai yaga dattijannan akwance jini na zuba ta gefen cikinsa . Ashwar ya ruga gareshi ya sunkuya ya dauke shi . Faruwar hakan keda wuya ya hango wata bataliyar ta irin wadannan dakarun da yayi fada dasu , wadannan dakarun yawansu ya ninka na baya sau uku. Badan tsoro ba sai don ya ceci yaruwar wannan dattijon
Ashwar yayi sauri ya haye dokinsa rungume da dattijon yayi cikin jeji a sukwane , dakarun suka bi bayansa amma cikin kankanin lokaci ya basu rata mai yawa , har ya bace musu ,
Dole suka hakura suka koma da baya.
.
Yayin da ashwar ya fuskanci sun tsera wa wadannan makiya , sai ya tsaya a karkashin inuwar wata bishiyar , ya sauko da dattijon nan yayi masa shimfida ya kwanta , sannan ya dauko wani dogon rawani daga cikin jakarsa ta daure cikin dattijon don tsaida jinin dake zuba .
.
Ashwar ya dubi dattijon a yayin dayake kakarin mutuwa yace “yakai babana sanar dani inda zan kaika kusa ayi maka magani”
.
Dattijon ya yunkura cikin karfin hali tare da taimakon ashwar ya hada bayansa da jikin bishiya ya zauna , numfashinsa na fita sama-sama yace
“Yaro kada ka wahalar da kanka ,ni tawa ta kare , kasani daga nan zuwa garinmu tafiyar wata guda ce , nafito daga birnin Nurul islam ne , garine na ma’abota Addinin musulunci , abin dayasa kaga wadannan mutane sun kamani suna tayi mani azaba , saboda sun ga ina bautar ubangijin musulunci ne ina sallah”
.
Koda da jin wannan batu sai ahwar ya tuno da labarin da tsoho makabul ya bashi dangane da maganar boka akan daukakar da zai samu aduniya , nan take ashwar ya sake tallafe tsohon nan akirjinsa yace
“Tuni ina da labarin wannan Addini naka , kuma nayi imani dashi a zuciyata shigar dani cikinsa”
.
Dattijon yayi wani irin tari mai ban tsoro idanunsa suka kakkafe kamar ya mutu , amma sai numfashinsa ya sake dawowa yace a cikin karamar murya “yakai wannan saurayi ka saurari abin da zan fadi yanzu ka maimaita shi, idan kayi haka ka zama musulmi.
.
Nan take dattijon yai kalmar shahada , daa ashwar yakasa kunnensa da kyau dai dai dattijon na gama fadin kalmar ransa ya fita ,
Shi kuma ashwar sai ya maimaita kalmar shahada, sannan ya mike ya haka rami ya binne dattijon yasa alama a kabarinsa , sannan ya hau dokinsa da nufin tunkarar birnin Nurul islam
.
Kwanci tashi ashwar nata tafiya a cikin jeji kwana da kwanaki bai sake gamuwa da komai ba face namun jeji, wasu sai yayi kallon kallo da su , wasu kuma ya fafata da su ko su tsere da kansu don ganin wuya ko kuma ya hallaka su , shi kansa ashwar sai da ya dunga mamakin irin wannan baiwa daya keda ita ta sadukantaka da jarumta da kuma rashin tsoro, ya tuno da cewa tun baifi shekara goma sha ba , mahaifinsa ke tafiya da shi farauta jeji, da hanunsa ya sha kama ‘ya’yan kura da damisa ya murde mudu wuya su mutu.
.
Tafiya dai taci gaba har ya sami kwana talatin cif , duk tsawon iyakar kwanakin nan ashwar yayi a lissafe suke a kwalkwalwarsa , kuma arubuce jikin kefen takobinsa , ba dan komai ba yayi haka ba , sai don kada ya wuce wa’adin da sarki abul dinar ya diba masa ba komawa gida , sau tari idan ashwar ya tuno da gimbiya mabaruka sai yayi ta yan wake wakensa ta soyayya shikadai cikin tsakiyar dokar daji,
In banda tsuntsaye da suke tayashi da sautin kukansu, ba ya samun mai tayashi debe kewa
.
Kwatsam ya hangi karamin gari a gabansa , kai tsaye ya tasamma garin har ya isa , da zuw a ya iske gaba dayan mutanen garin sanye suke cikin kamilar sutura mazansu da matansu, musamman ma matan ko’ina a jikinsu a rufe yake , kwayar idanunsu kacal ale gani Abin da ya fara riska shine wani gini wanda ya iske mutane a kofarsa suna ta shiga, wasu kuma sun tsuguna suna wanke gabban jikunsu da ruwa. Daga can kuma sai yaga wani daga cikinsu ya hau bisa wani tudu dake jikin wannan gini yana wasu maganganu masu kama da karatu, aciki karatun ne ya ji ya ambaci kalmar nan ta shiga musulunci wadda marigayi dattijo ya biya masa .
Koda jin haja sai farin ciki ya lullube Ashwar. Ya gane cewa wannan gari shine Nurul islam
.
Shuraih 99% nake ce daku
.
Ashwar ya sami wuri ya tsaya , ya sauka daga kan dokinsa ya tsaya cak yana kallon mutane suna kallonsa. Jim kadan sai yaga kowa ya shiga cikiN dakin nan, mutum daya ya wuce gaba saura suka tsaya bayansa aka fara wani aiki mai kama da bauta . Ashwar na tsaye yana lekensu da mamakin abun da sukeyi har dai suka kammala , suka firfito wannan mutum wanda ya shugabanci aikin bautar ya nufo inda ashwar ke tsaye
.
Balarabe ne fari , kuma dogo kyakkyawa, shekarunsa zasu kai hamsin da doriya, kamar yadda yake balar
Abe haka dukkanin sauran mutanen garin suke
.
Da zuwa ya kalli ashwar yace” yakai wannan bako daga ina kuma me ya kawoka birninmu”
.
Da ashwar yaji wannan tambaya acikin yaren daya sani ne wato larabci sai murna ta kama shi, nan take ya kwashe labarinsa tun daga farko har karshe ya zaiyana masa . Duk wannan abu dake faruwa sauran jama’ar gari na tsaitsaye a gefe suna kallo.
.
Ashwar na gama bada labari ,sai wannan mutumi ya rungumeshi yace “ai ka zama dan’uwanmu tunda ka shiga Addinin Musulunci, wannan daki daka gani mun shiga masallacine ne inda muke sallah, wannan dattijo daka gamu dashi a wancan gari na baya daga cikinmu yake, kuma yaje ne isar da sakon Allah ga wadannan makafirta , shi yasa suka tsareshi suka yi tayi masa azaba . Kashe shi da sukayi kuwa sun taima ka mashine, don yasamu shahada babban rabo a wajen ubangijin musulunci”
.
Balaraben ya kara da cewa “Ni sunana Imamu Hamid , ni ne shugaba a wannan gari yanzu tunda Allah ya kawo ka garemu sai ka zauna awannan gari don kasab yadda ake bautar Allah kuma ka fahimci Addini , tabbas ubangijin musulunci mai taimako ga bayinsa ne , wadanda suka dogara dashi , tabbas zaka nasara a bisa abin daka fito nema . Izan har baka kaucewa dokokin Allah ba”
.
.
Nan take Imamu Hamid ya rukke hannun ashwar ya tafi da shi izuwa gidansa. Gaba daya garin kuwa ya cika da labarin zuwan jarumi ashwar , da kuma ababan al’ajabin da ke tattare da shi
.
Ashar ya zauna a garin Nurul islam har tsawon sati uku inda ya koyi ibada har da karatun alkur’ani daya ke Allah yabasi kaifin basira cikin ‘yan kwanakinnan ya samu ilmi mai yawa, kuma ya karbi littatafai na sauran fannonin ilimin Addinin kamar tauhidi da dae sauransu, ya kudurce a ransa zai ci gaba da neman ilmin addini a duk sa’add ya sadu da masana.
.
Ranar da ashwar ya cika kwana ashirin da uku a wannan gari na Nurul islam, a rannan yai sallama da su Imamu Hamid aka kawo guzuri mai kyau aka bashi , ya yi godiya sannan yai bankwana dasu , yatafi yana mai bakin cikin cikin rabuwa dasu, suma suna yi, sakamakon shakuwa da albarkar HASKEN MUSULUNCI(next book insha Allah)
.
LoKacin da ashwar yayi dan nisa da gari , sai rubuta adadin kwanakin da yayi ajikin kufe na takobinsa, ya lissafa dana baya sai yaga a halin yanzu ya cimma wata uku saura kadan, ya zamana kenan baifi saura wata guda da ‘yan kwanaki ba wa’adin da aka dibar masa ya cika , wannan yasa hankalinsa yayi mummunan tashi , domin ko abirnin inda Nurul islam bai samu wanda ya taba jin labarin inda birnin duma yake ba.
.
“Yanzu yaushe nasan inda wannan gari yake har naje na dauko bishmalu ,sannan na koma garinmu duk a cikin wadannan kwanaki?”
.
Tambaya ce wadda ashwar yayi wa a zuciyarsa , kuma shi kansa baisan amsarta ba .
.
Bayan kamar rabin sa’a yana tafiya , sai hadari ya hado , nan take ruwa ya kece kamar da bakin kwarya ,dan haka sai ashwar ya ruga karkashin wani dutse ya fake , ya daure dokinsa a jikin kafarsa sannan ya kishingida , cikin yan dakiku kadan bacci ya saceshi.
.
Yana cikin wannan baccine dokinsa yayi haniniya yaja kafarsa , ashwar ya tashi ya duba bai ga komai ba ,
Kawai sai ya koma baccinsa. Dokin ya kara haniniya a karo na biyu . Ashwar ya farka a fusace ya mike ya dada dubawa ko’ina bai ga komai ba , sai yayi tsammanin dokin nasane yake bukatar yayi kiwo, don haka sai ya kwance shi ya koma baccinsa .yin hakan keda wuya , kawai sai yaji saukar wani abu ajikinsa , yana bude ido yaga raga ta rufe shi, wasu dakaru kimanin su arba’in na ruke da ragar da makamai sun kewaye shi
.
“Tashi mu tafi ” daya daga cikin baraden ya fadi.
.
Kada ku manta kuna tare ne da shuraih 99%
.
Ashwar ya dubeshi ya dubi sauran, ya tabbatar babu imani a fuskokinsu, da farko yayi niyyar ya ganar dasu kuransu, amma sai yace a ransa
.
“Bari dai naga gudun ruwarsu”
.
Batare da gardama ba ya bisu izuwa wani gida aka sa shi cikin wani daki aka kulle har magariba ta kawo jiki.
Wannan tsarewa da aka masa batazo masa da illa ba sai dai rashin sallah da kuma dokinsa da yake tunanin ya bace a jeji, gashi duk makamansa na fada na jikin dokin .
Ashwar yadaga hannunsa sama ya roki Allah yasa wannan tsarewa ta zame masa alheri
.
Washe gari wannan tawaga data kamo ashwar suka taru acikin gidan , gaban ubangidansu, inda dayansu da ke bayanin cewa basu samo koda tsuntsu ba sai wani yaro da suka samo yana ajiye a cikin daki.
.
“To yaushe zaku cinyeshi? Ko kuwa kun fison ku gama da tsofaffin da ku ka kamo tukunna”
.
Gaba daya sukace ai sunfi son yaron, saidai yayi musu kadan, dan wani ma bazai samu koda rabon kunne daya ba , nan take ubangidan wadannan mutane yayi musu sulhu, akan a fito da naman gaba daya a cinye don kar ayi fada.
Wannan zance gabadaya a kunnen ashwar akayi shi.
Don haka sai ya cika da mamaki daya ji ana maganar a cinye dan adam kamar yadda ake cin naman dabba.
.
“Ni kuwa naga ta yadda za a cinyeni ina ji ina gani”ashwar ya fadi cikin zuciyarsa.
.
Dankari makari,lallai yau akeyinta inji 99% ke magana’
.
Jim kadan aka bude dakin da ashwar ke ciki, abinci ne aka kawo, wani gajeren mutum ne kato ya shigo da shi cikin wata karamar tasa ko sallama babu ya ajiye , ya juya ya fita aka garkame kofa, ashwar ya dubi abincin na yaga bai san irin saba gashi yana jin yunwa amma sai yafara wasi wasi ko yaci ko ya bari.
Tabbas yasan dae mutanenan kafiraine baisan ma koda me sukayi abincin ba. Kawai sai ya yanke shawarar yayi baccinsa na jiya da baikarisa ba , nan take ya bingire yai ta sharara barci kamar wadda yake cikin gidansa
.
Kwatsam yaji wata murya a sama ance ” tashi mu tafi”
.
Yana bude idanunsa yaga wasu kartine suk uku.
Ashwar ya tashi bako musu suka sa shi agaba sai wajen babbansu , wani katone mai tumbi, ya saki ciki sai kace garwa. Cikin tsawa ya dubi kattin yace
.
“Ku ajiye shi anan ! Ku fito da tsofaffin”
.
Ashwar ya zauna yana kallon ikon Allah sai yaga an fito da mutane sun fi dari, nan dai yaga anjera su gaba daya alayi kamar masu shirin tada sahun sallah,
Hardashi ahwar din
Mai katon cikinnan ya tashi da kyar ya fara zagaya su ashwar, bai dafa kowa ba sai wani tsoho wanda ko kyaleshi akayi ya kalli kisan da za’aiwa sauran zai iya mutuwa don tsananin firgita , don ko ayanzu ma baisan cewa yana fitsari a wando ba , jikinsa na kyarma tamkar mai mugun zazzabi , nan take karti suka kama wannan tsoho suka jefa shi cikin wata katuwar tukunya wadda ke karkashin wata murhun wuta na dafuwa, ruwan ya cikinta sai zabalbala yake ,
Ai kamar hadiyar kwayar gero haka tsohonnan ya lume cikin tukunyar , ko tarinsa ba’a jiyo ba.
Wasu karti su biyu da suke rike da ludayin tukunyar suka hada hannayensu hudu suka tura ludayin zuwa karkashin tukunyar suka tsamo.
Sai ga gangar jikin tsohonnan ta motse kamar curin nakiya, gaba daya fatar jikinsa ta sutale duka akansa kuwa babu silin gashi koda daya , atakaice dai ya dahu yai lugub . Ja daya za aiwa tsokar namansa ta rabu da uwar jiki.
.
Koda ganin wannan al’amari sai ashwar yai salati yace” Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”
.
Kafin a ankara ya suri kato guda ya mai dashi bulala , yai ta dukan sauran kattin , nan da nan gida ya rikice da ihu da kuwwa , katon nan da ke zaune a kujera kamar kula sai kujerar ta karye ya fado ji kake tim! Bama kafiran azzaluman mutanen ba wadanda ma aka kamo don acinye saida suka gigice.
Tsoffin cikinsu suka shiga wani hali don wasunsu ma sun fado sun ture abincin . Azzaliman kuwa duk sun firgice sun dimauce , wasu su kayi waje da gudu wasu suka yiyo kan ashwar wato masu karfin halin kenan , shi kuwa yaci gabada da rugurguzarsu suna zubewa kamar mai kada karmami. Musulman da aka kamo suka hau salati.
.
Bayan da ashwar ya sumar dana sumarwa ya kashe na kashewa , masu gudu kuwa suka tsere ya rage saura shugaban masu cin naman mutanen nan kadai, kwance akas ya kasa tashi bare ya gudu, sai nishi yake da kyar , nan take ashwar ya kaimasa wawura ya sunkuce shi sama duk girmansa ya zama na banza , don tamkar ashwar ya daga buhun audiga ne, tsundum ya jefashi cikin wannan tukunya mai zabalbala , jama’a gaba daya suka rugo wajen ashwar suna yi masa godiya da sa albarja ashwar ya fice ya bar su suna ta murna da wake-wake .
Wani abin mamaki yana fitowa daga cikin gidan sai ya iske dokinsa tsaye kamar dama yasan da fitowarsa yanzu,
Ashwar ya kalli dokin yayi murmushi sannan yace
“Daga yau nasa maka suna ganjarma”
,
Kai masu karatu nafara gajiya fa 99% ke magana
,
Ashwar yayi tsalle ya haye kan ganjarma , ya sukwane shi zuwa cikin jeji.
Wannan shine abin daya faru ga jarumi ashwar, bayan ya baro garin Nurul islam
.
.
Naga kamar bakwason littafinnan
Anya kuna son inci gaba kuwa
.
.
Littafin abdulaziz sani/m gini(kings of adventure stories)
.
Typing:- Shuraih Usman
Tel’ 08133209890
.
.
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.