Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

BABBAN GORO part 1B

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


BABBAR GORO

.
Littafina daya (1)

Part 1B

.
With shuraih 99%
Typing by :- http://facebook.com/shuraih.usman

.
Sarki abul dinar ya mike tsaye da kansa ya daka tsawa , nan take akayi tsit.
.
Sarki ya dubi ashwar cikin murmushi yace” ya kai ashwar kaji jarabawar dake gabanka shin zaka iya ?”
.
Gaba daya idanun jama’a suka zubo kan ashwar.
Ashwar yayi shiru yana kallon jama’a har idanunsa suka kai kan gimbiya, inda ta mike zumbur tana mai kokarin tace ya amsa, amma sai ya da kansa ya dubi tsho makabul, nan take makabul yayi masa inkiya ya amsa.
.
“Ran sarki ya dade na amince da wannan jarabawa , kuma nayi alkawarin zan zo da bishmalu dan sarkin misra cikin wannan fada taka”
.
Cikin tsananin farin ciki ta daka tsalle sama sannan ta rugo da gudu ta rungume ashwar agaban jama’a , nan take fada ta sake rudewa da hayaniya ,
Sarki da ‘yan majalisarsa suka mike suka shiga cikin gidan sarauta ,
Ita kuma gimbiya sai ta tafi da ashwar izuwa gidanta .
Surutai iri iri daga bakin jama’ar gari suka yawaita. Wasu suce hakika ashwar mahaukacine, wasu kuwa suce yarinta ce ta dibeshi yayi wauta, wasu ma har zuwa sukai suna yiwa tsoho makabul ta’aziya suna cewa”dan ka ya zama gawa”
.
Shi kuma sai dai yayi murmushi kawai agaresu su tafi suna gulmarsa.
.
Farin ciki wajen gimbiya mabaruka a wannan rana yafi karfin misaltuwa .
Nan take tasa aka shiryawa ashwar walima ta musamman , inda kuyanginta suka shiga hidimar girke girke .
.
Cikin kankanin lokaci aka samar da abinci iri iri da ababan sha kala kala .wannan walima an yi tane awani daki ta musamman cikin gidan gimbiya mabaruka ,
Kuma ba’a gaiyaci kowa ba face ashwar shi kadai, sai kuma abar begensa wato gimbiya , ma’ana su biyu kadai.
Suka zauna karkashin wani dogon tebur mai dauke da kujeru hamsin, akan wannan tebur aka shirya dukkanin wannan abincin da ababan sha bisa farantai , akan kowane faranti akwai kuyanga tsaye rike da cokali , da zarar gimbiya ta bukaci abincin sai kuyangar ta garzayo ta kawo, ta zuba a cikin wani babban faranti dake gabansu ita da ashwar anan fa mabaruka ta nuna tsantsar soyayyarta ga ashwar domin da hannunta ta dunga bashi abincin yana ci , ganin haka shima sai ya dunga ciyar da ita da hannunsa, har suka ci suka koshi.
.
Nan take mabaruka ta kama hannun ashwar ta kaishi cikin falonta inda take saukar manyan baki suka zauna. Dayake ashwar bai sa ba da ko’ina ba in ba gidan gona ba ,sai ya zama dan kauye yayi ta kalle kalle a cikin falon
.
Mabaruka ta bushe da dariya tace”haba masoyina ya zaka dunga kalle-kalle kamar wanda ya fito daga kauye.
.
Wannan batu yasa ashwar yayi murmushi yace “ranki ya dade dolene ki ga kauyanci a tare dani domin tunda aka haifeni a cikin gidan gona na ke rayuwata , ban taba shigowa cikin gari ba sai ranar dana hadu da ke , hatta sa’adda aka kaini dakin tuhuma hankalina ya gushe ban taba shiga wajen ba sai a ranar. Hakika kece sanadin shigowata cikin Al,umma , tun tasowata ban san komai ba face bauta da biyayya ga sarki abin dana ga iyayena nayi , ban san sanya sutura mai kyau ba irin wadda nake gani yanzu ajikin su, bansan kwanciya ba akan shimfida sai ciyawa da harawar doki.tabbas kin sauya komai na rayuwata bazan taba mancewa dake ba “
.
Yayin da ashwar yazo nan a zancensa sai ya ga idanun gimbiya mabaruka ya ciko da kwalla , nan da nan hawaye ya fara zuba bisa kuma tunta .
Wannan yasa hankalin ashwar ya tashi, yadan matsa kusa da ita ya durkusa bisa guiwowinsa cikin kaskantar da kai yace
.$
“Ya shugabata ki yimin gafara idan na saba miki a cikin maganganun dana fadamiki”
.
Bisa mamaki sai yaga fuskarta ta fadada da murmushi , sannan ta rike kafafunsa suka mike tsaye tare, ta dubeshi da kyau tace
.
“Ya masoyina na rantse da wata ko kadan baka bata mini rai ba, kawai na tausayawa rayuwarka ne . Hakika sai yanzu na tabbatar da cewa mahaifina yana mulkin zalunci, domin an tauye hakkinka dana iyyenka , A matsayinku na bil’adama da ba dabbobiba, bai kamata ace baku da sutura ba face walki, tabbas inda nasan cewa akwai irinku a garinnan da tuni na kai muku “
.
Shuraih ke magana
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yaji duk tsigar jikinsa ta tashi, jikinsa yayi sanyi, ya kura mata idanu kuma ya kasa cewa komai . Mabaruka na ganin sauyin……..
.
Kash kuyi hakuri makaranta fallen littafin ya lalace akalla dai fallen daya lalace yakai goma sha daya. Amma zanyi kokari na dan bayyana muku abubuwan fallen ke kunshe da shi cikin gaggawa
.
Shuraih kemagana
Boka gulmanu yazo ya samu sarki abul dinar ya sanar dashi cewa” lallai wannan yaro kar ya wuce kwana uku bai yi wannan tafiya ba kuma a sanar dashi cikin wata uku kacal akeson ya dawo tare da bishmalu”
.
Sarki abul dinar ya dubeshi cikin mamaki yace ” yakai sarkin matsafa shin meyesa kace haka “
.
“Aljanina ne ya sanar dani haka kuma ya tabbatar min muddin bai bar garinnan cikin kwana uku ba toh tabbas zaiyi nasarar shiga birnin duma kuma ya dauko bishmalu”
.
Sarki abul dinar najin haka yai umarni ga wani bardensa. Dayaje ya sanar da jarumi ashwar cewa cikin ya tabbata cikin kwana uku ya fita daga garinnan ya nufi birnin duma , sannan wata uku gareshi muddin wata uku ta gota koda da kwana dayace to ko yazo da bishmalu wannan gari to tabbas ya fadi
.
Wannan shine abin daya afku a fadar sarki abul dinar
.
Shidai mahaifin bishmalu wato sarkin Misra ya auri wata kyakkywar mata , ita wannan matar duk wanda ya aureta mutuwa yake sakamakon sarkin aljanu kifyan dayake matukar sonta koda sarkin misra ya aureta sai aka ringa tsorota da shi ana mai kashedin ya rabu da ita ,
Wata rana ya fita farauta shida baradensa suna cikin jeji sai sukaji wata murya ta barke da dariya sannan akace da su “ya kai wannan sarki mai taurin kai lallai ka rabu da wannan mata taka don ita mata ta ce ni kadai”
.
Sarkin misra na jin wannan batu yace karyarka tasha karya baka isa karabani da mata ta ba ……
.
Wata sarka yagani ta shake wuyansa nan take ya ringa makyarkyata .
Can sai yafadi wata kalma sai wannan sarka ta tsinke ,
,
Baraden suka juya tare da sarkin misra suka dawo cikin gari
.
Toh fa tun daga wannan rana ne wani ciwon kai mai tsanani ya addabi sarkin misra.
Wannan ciwo ta hana shi sakat domin idan ta tashi mai tamkar zai mutu haka yake .
.
Koda matarsa taga wannan ciwo taki ci taki karewa sai ta tafi wajen boka ta sanar dashi wannan ciwon na sarki take bokan ya bata wata laya yace ta dauara layan awuyan sarki.
.
Tazo ta daura layan , aiko tana daurawa sarki ya ji shi garau tamkar wata ciwon kai bata taba samun saba a duniya.
.
Ana nan ana nan rannan sai matar sarkin misra ta samu ciki ,
Sarkin misra yai murna kwarai , bayan cikin ya cika wata tara sai ta haife santalelen yaro wanda tsabar kyaunsa ma ana zaton aljani ne
.
Sarkin misra yayi murna kwarai amma mai hade da bakinciki sakamakon mutuwar matarsa yayin haihuwa ,
.
Aka saka ma yaron suna bishmalu ,
Wata rana da daddare sarkin misra yai mafarki da wani garjejen aljani yana rike da dansa yace mai” tun da ka kashe mata ta toh na dauki danka daga yau yazma dana baza ka sake yin arba da shiba.
Har ka mutu
.
Washe gari sarkin misra ya farka baiga bishmalu ba yai neman duniya amma bai ganshi ba daga bisani yaje wajen boka toh ananne boka ya tabbatar mai da cewa dansa yana nan a raye wani hatsabibin sarkin aljanu ne ya sace shi ya kaishi birnin duma sunan wannan aljani kifyan
.
Sarkin misra ya tura sadaukai , jarumai da dama amma duka ba labarinsu
.
Daga karshe ya hakura ya sadakar
Amma sabi da bakin ciki kullum cikin kuka yake yanzu haka yana fama da wata irin cuta , wannan cuta anyi magani anyi magani amma ina taki warkewa ,
Amma bokansa ya fadami duk randa yai arba da dansa bishmalu toh zai warke daga wannan cuta .
.
Wannan shine takaitaccen tarihin bishmalu daga bakin shuraih 99%
.
.
Koda ashwar ya sami sanarwar sarki abul dinar kan cewa ya gaggauta barin garin kafin kwana uku
.
Sai yayi shiri
Tsoho makabul ya iso gareshio dauke da wasu makamai , mashine da takobi sai kuma kibiya
.
Tsoho makabul ya mika mai yace ” amshi wayannan makamai kasani wannan bokan daya fadamana cewa zakayi gagarumar shahara a duniya shine ya bamu wayannan makamai yace duk sa’adda ka girma in damka ta a hannunka.to yanzu lokaci yayi “
.
Ashwar ya amsa yana mai godiya ga tsoho makabul
Zuwa asuba ashwar yagama shirin shi sannan yarubuta wasika ya bawa tsoho makabul kan cewa in gimbiya mabaruka tazo ya bata sannan ya sanar da ita shi yatafi .
.
.
Bayan fitarsa daga birnin sarwaliya ya yanki daji yaci gaba da tafiya
Sudai wayannan makamai da tsoho makabul ya bashi sihirtattun makamaine
1.acikin makaman akwai wata mashi wadda duk abin da aka soka da ita to fa saide wani bashiba ita wannan bashi har dutse fasashi take ta tarwatsa shi sannan ta wuce
2sai wata kwari da baka wanda shi wannan kwarin I zan har ka harbata toh zataje ta cake duk wadda kake bukata ta cakeshi sannan ta dawo cikin gwafanta itama wannan kwari tana huda dutse sannan ta tarwatsa shi
.
(Har yanzu dai ni shuraih hakuri nake baku sakamakon lallacewar sauran fejin kuma ni kaina nasan bazan baku labarinnan yadda take ba amma zan dan kokarta)
.
3sannan kuma akwai wata sihirtacciyar takobi wadda take da kaifin tsiya koda bishiya aka sara da wannan takobi toh anan take zai bushe sannan ganyayyen bisansa su bushe yafadi kasa.
Shi wannan takobi idan dare yai sai kaga yayi haske inda zai haskaka ma marikinshi hanya
.
.
Wata rana ashwar ya kwanta yana barci saiyayi mafarki a cikin mafarkin nasane aka sanar da shi cewa akwai wata gari agabansa izan ya shiga garin kada yaci komai ko ruwa ne kada ya yadda yasha
,
Koda ya farka daga barcin ne sai yaga mai ai safiya tayi sannan rana ma ta fito .
Tafiya kadan yayi sai ya hangi wani gari agabansa batare da shakkar komai ba ta dumfari wannan garin yana shiga cikin wannan gari sai yaga wani tsoho yana noma koda tsohon ya gansa sai ya kariso gabashi suka gaisa bayan sun gaisa ne tsohon ya dauko wasu dabino ya mika ma aswar.
.
Har ya kai hannu zai karba sai kawai ya tuna da mafarkin da yayi jiya da daddare .
Sai yafasa amasar wannan dabino.
Tsohonnan yayi yayi da ashwar ya ci dabinon amma ashwar yaki sai wannan tsohon ya tashi mai haikan yana so ya kasheshi koda ashwar yaga haka sai ya zaro takobinsa ya fille kan wannan tsohon sannan ya ci gaba da tafiyarsa izuwa cikin garin
.
Shidai wannan gari sarkinsu ya kasance mugune kuma azzalumi , yana bautar wani dodone kuma wannan dodo kullum sai an yakama sa bil’adama yasha jininsa , kullum barade sukan fita zuwa farautar mutane, sukuma mutanen garin yayin da baki suka shigo gari sai su yan yamesu da abubuwan makulashe wanda aka zuba amaganin bacci aciki kana ci shikenan naka yaja
.
Yayin da dakarun sarki masu farautar mutane suka fita farauta izan har basu sami mutum ba sai sudawo izuwa birnin su a cikin mutanen gari sai ayi kuri’a duk wadda tafada kansa toh shine za’a yanka wa dodon da sarkin ke bautawa ya shi jininsa.
.
.
Ashwar na zuwa kasuwar wannan gari sai jama’a suka yanyameshi dakayan ciye ciye shikuma duka ya basar yace musu bayaci
Koda sukaga alamar cewa ashwar bazaici kayan ciye ciyen ba sai suka hasala suka haiko masa da nufin su kamashi
Koda ashwar yaga haka ai saiya ciro takobinsa yaringi saransu yayin dasuka ga ashwar yayi musu muguwar barna sai suka rabu dashi
.
Can sai gawasu dakaru nan sun kama wani mutumi ma’abocin fararen kaya sun yiwa wannan mutumi jina jina suna tafaman jansa akasa
.
Koda suka kariso gaban sadauki ashwar sai shugabansu yace dashi kai wa ne ne kai da harzaka shigo cikin birninmu sannan kayi mana irin wannan ta’adi
.
Ashwar yace dashi ni bakone
.
Shugabar wannan dakaru ya zaburo domin yakama ashwar aisai aswar yai wa shugabar dakarun karo afuska,
Sai gashi ya baje akas ko shurawa baiyiba da jama’a suka suka ga haka sai gudu, sauran dakarun da suke tsaye suka ce da wa Allah ya hadasu in ba ashwar ba? Ashwar baiyi tunanin amfani da makami ba a wannan fada, don haka hannu da kafarsa ne makamansa cikin kankanin lokaciya tarwatsasu.
.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kuyi hakuri in kunji nayi kuskure ku gyara min
.
Muhadu a part 1C
,
Littafin Amdulaziz sani/m gini(kings of adventure stories)
.
Domin sada zumunci mu hadu a page dina na face book. Shuraih 99%
.

ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч Shuraih usman

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.