BABBAN GORO part 1A

 BABBAN GORO part 1A
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Nov, 2017
Upload Time 9:25 pm
Hits 861 Hits
Comment No Comments

Description


BABBAN GORO
————————-
Littafina daya
.
Part 1A
.
With shuraih 99%
Typing by :- Shuraih Usman

.
Zaku sha karatu har ku gaji
.in naga bakwa respond toh zan ajiye littafina agefe
.
.
Awani zamani can baya anyi wani attajirin sarki wai shi abul dinar ,wanda matsafa da masu harsashe suka tabbatarda cewa babu attajiri kamarsa a duniya ,saboda tarin dukiyar da Allah yabashi wannan sarki yana da matan aure guda goma sha shida kuma yana da kuyangai tamanin gabaday wayannan mata nasa babu wadda ta raba haihuwa sai guda daya ,
Wata mace da ake kira hauziya
Duk acikin matan abul dinar hauziyace yar talakawa ,domin duk sauran daga yayan sarakuna sai yayan mayan attajirai na duniya
.
A ranar da aka fuskanci hauziya ta sami ciki ,sai sauran kishiyoyinta suka cika da bakin ciki .
Batare da da bata lokaci ba suka shiga bin hanyoyin da zasu tabbatar da cewa cikin ya zube ,masu tsafi nayi ,masu surkulle nayi, kai wasu ma kiri kiri a fili sukka ringa yin abubuwan da zasu sa cikin ya zube amma ubangijin musulunci shine mai yin yadda yaso ,sai ya kare hauziya daga sharrin kishiyoyinta .
Shikuwa sarki abul dinar koda yaji cewar hauziya ta sami ciki , sai yadauki son duniya ya kwallafa a akanta . Domin zata share masa hawaye a bisa bakin cikin daya addabi rayuwarsa ta duniya ,wato rashin magaji ,
Dayake ya tabbatar da cewa sauran kishiyoyinta bazasu kyaleta ba, sai ya dauketa ya kaita wani gidansa dake bayan gari .
Ya ajiyeta ita kadai ,
Daga ita sai bayi masu yi mata hidima .
Gidan ya zama ba’ashiga da fita ,in ba shi kansa ba .sarki abul dinar ya tare wajen hauziya , tare suke ta rainon cikin har wata takwas .
A ranar da cikin ya cika wata takwas da kwana shirin da biyar .
Ciwon nakuda ya kama hauziya .
Cikin yan dakiku kadan ta haifi sankaceciyar ‘ya,
Wadda atun tana jinjiniyar aka tsorata daganin kyawunta.
.
Sannu sannu akayi ta rainon yarinyar wadda aka sawa suna Mabaruka ,har ta girma .
Ta zama cikakkiyar budurwa ,
Wadda saboda tsananin kyau labarinta ya cika duniya . Jarumai da matsafa da dama sun hallaka junansu a kan soyayyarta
.
.
Wata rana gimbiya Mubaruka ta fita rangadi , don shakatawa cikin wata babbar gona ta mahaifinta ,kuyangi da barade na take mata baya.
.
Kwatsam sai ga wata katuwar macijiya mai girman gaske , ta bayyana a gabansu .
.
Koda ganinta sai barade da kuyangi suka kwalla ihu, suka ruga baya da gudu ,
.
Baraden nan suka yi ta rige rigen gudu ,sun mance da aikinsu na tsare lafiyar ‘yar sarki .
Ita kuwa mabaruka sai ta tsaya kyam ta kasa gudu , don tsananin razana , hawayen bankwana da duniya suka tsiyayo daga idanuwanta .
.
Katuwar macijiyar ta wangame baki zata hadiyeta , kawai sai mabaruka taga wani bakin bawa yai tsalle ya rungumi wuyan macijiyar
.
Nan fa suka kama kokawa shi da macijiyar su fadi can su tashi can.(Ni kaina shuraih sai dana kusan….basai na karisa ba)
.
Shi yana kokarin ya turmusheta ya rarumi wani icce dake waje guda ya soketa ita kuma tana kokarin kannannadeshi ta karairaya kasusuwan jikinsa . Haka dai suka yi ta dauki ba dadi har tsawon rabin sa’a , macijiyar nan tai masa fata-fata , duk jikinsa ya rune da jinin raunuka
Amma hakan bata sa ya saketa ba ,
A hakan dai Allah ya bashi iko , hannunsa ya kai kan wannan icen cikin zafin nama ya dauki icen ya caka abakin macijiyar , ya bullo ta tsakiyar kanta .
.
Nan take macijiyar ta sulale ta fadi kasa matacciya,
Shi kuma bawan yafadi kasa a sume .
.
Koda ganin haka sai gimbiya mabaruka ta ruga gareshi ta rungumeshi tana kuka ,
Gaba daya jikinta ya baci da jininsa .
Ahaka sarki abul dinar da dakarunsa suka zo suka sameta .
.
Nan da nan aka ban bareta daga jikin bakin bawan , aka tafi da ita shi kuma aka yayyafa masa ruwa ya farfado daya ke shi bawa ne marar gata ,
Sai aka tuhumeshi da laifin rungumar ‘yar sarki ,
Ba’ama duba sai da ran dayayi ba, dan ceton ‘yar sarkin.
.
Saboda haka aka kaishi dakin tuhuma ,aka dauddaureshi da sarkoki aka yita gana masa azaba iri iri.
.
A iya tunanin Mabaruka wannan bawa ya mutu wannan dalili shi yasa tai ta kuka har hankalinta ya gushe ta suma bayan ta farfado ta mike zaune daga kan gadon data ke kwance ,
Inda tai arba da mahaifiyarta hauziya zaune a gefen gadon idanunta cike da hwaye .
Koda ganin mikewar mabaruka sai farin ciki ya kama hauziya.
.
“Mama ina gawar bawan daya ceci rayuwata?”
Mabaruka ta tambaya fuskarta cike da alamun bege
.
“Waya ce miki ya mutu? Ai dogon suma yayi kum, kuma anzuba masa ruwa ya farfado ,yanzu haka yana can daure a dakin tuhuma”
.
“Me yayi za’a kaishi dakin tuhuma?”
.
Batare da mabaruka ta saurari karin bayani ba ta mike tayi waje da gudu ,
Mahaifiyarta tana kira amma taki dawowa , bata tsaya ako ina ba sai a kofar dakin tuhuma,
Da zuwa ta dakawa masu gadin tsawa tace “su bude mata kofa kofar “
.
Jikinsu na rawa suka bude kofar ta shiga , inda ta iske shi kwance magashiyyan cikin jini .
Nan take tasa aka kwance sarkar dake jikinsa , tasa aka kaisa gidanta inda taimasa wanka ta sama magani a raunukan jikinsa sannan tasa aka kawo masa abincin sarauta , ya cika tumbinsa ! Daga nan aka kaishi wani dakin hutu ya kwanta yai barci, har sai da rana ta fadi sannan ta shiga dakin ta tashe shi , duk su biyun suka kurawa juna ido
.
“Yakai wannan jarumi menene sunanka”
.
Bawa yayi murmushi yace “ni sunana Ashwar “
.
“Ya akai kana matsayin bawa a gidanmu na sarauta amma ban taba ganin kaba ?”
.
Ashwar yasake yin murmushi yace “yake gimbiya kisani babu yadda za’a yi ki taba ganina , domin tun da aka haifeni ban taba fitowa ba daga cikin lambun sarki na can bayan gari sai ayau .
Mahaifina shine bawan dake kula da wancan lambu na sarki , tun yana saurayi yake wannan bauta harya tsufa ya mutu , nikuma na gajeshi
Mahaifiyata ma acikin wannan lambu ta rasu yanzu haka kabarinta na cikin lambun
A yaune sarki ya aika mini naje daya lambun nasa nayi aiki wanda shine kika ziyarta don rangadi
To ina cikin aikine na hango shigowarku keda kuyangi da barade .
Kuma sai naga wannan katuwar micijiya ta tarwatsa kuyanginki da baraden
Duk sun gudu sun barki shi yasa na sai da raina don ceto rayuwarki”.(Ni 99% nace lallai kacika sadauki)
.
.
Koda jin haka mabaruka tai ajiyar zuciya hawayen tausayi kauna suka zubo mata tace “ya kai Ashwar kasani daga yau bawani namiji da zan aura in ba kaiba
.
Cikin razana Ashwar yaja da baya ya takure jikinsa ga bango yace” ranki ya dade ki rufa min asiri , ki tuna fa ni bawane , bawan ma bakin fata ,ke kuwa gaki balarabiya ‘yar sarki,ina ni ina aurenki”
.$
Mabaruka tayi murmushi tace “ai babu ruwan so da matsayin jinsi ko launi ,idan duk duniya zata taru banga wanda ya isa ya raba ni dakai ba , abu daya nake so na ji daga bakinka kawai , kana sona ko baka sona?”
.
“Haba gimbiya ai babu wani namiji da zai ganki yace baya so , amma ai wutsiyar rakumi tai nesa da kasa kuma BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE”
.
“Kwarai kuwa”wata murya ta amsa daga bayan su.
.
Mabaruka da ashwar suka dubi bakin kofa a tsorace , sukayi arba da sarki Abul dinar fuskarsa a murtuke wasu kartin barade shida na tsatsaye a bayansa suna muzurai tamakar saci babu.
.
Cikin fushi ya dubi mabaruka yace “haba gimbiya shin kin mance da martabar gidannanne ?kin manta da matsayinki na ‘yar sarki ne?har zaki wulakanta kanki ki dauko bakin bawa ki shigo dashi har cikin gidanki mai Albarka.
.
Maimakon mabaruka ta nutsu kota firgita da wannan tambaya sai ta kyalkyale da dariya sannan tace “haba Abba ka runa fa mahaifiyata ta fito daga dangin talakawa ,me yasa ka aurota har kuka haifeni? Shin baka tsammanin zubar martabar sarautarka ne? Hakika sone yasa idanunka suka rufe , tunaninka ya gushe ka manta da matsayinta……”
.
Cikin hanzari abul dinar ya tari numfashin mabaruka yace” yata kada ki yi la’akari da wannan , domin inki kai tunani akwai alaka ta jinsi da jini tsakanina da mahaifiyarki amma tsakaninki da wannan bakin bawan babu alakar komai”
.
“Abba ni dai Ashwar nakeso”
(Shuraih 99% ke magana)
.
Wannan bayani ba karamin girgiza Abul dinar yayi ba , don tsabar takaici sai da yaji kwalla ta zo masa amma sai ya juya baya yayi shiru yana tunani , daga can ya juyo ya dubi mabaruka yace” na amince da niyyarki amma bisa sharadi “
.
Cikin mamaki mabaruka tace “wane irin sharadi ne?”
.
“Zakiji sharadin gobe da a fada gaban dukkanin jama’a.
.
Nan take sarki ya juya ya fice daga dakin ,barade suka take masa baya.
.
Ashwar da mabaruka suka dubi juna cikin tsananin damuwa
.
“Ai daman na san wannan al’amari bazai taba yiwuba , nagaya miki cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE”
.
Mabaruka tayi murmushi tace “ashwar ina so ka kalli cikin kwayar idanuna kaga ya mini abinda ka gani aciki “
.
Ashwar ya kura mata ido har tsawon ‘yan dakiku kadan sannan ya kawar da kai
“Me kagani acikin idanuna?”
“Banga komai ba face digon baki da zagayen fari”
.
“To wannan zagayen farin daka gani ba komai bane face fadar zuciyata , wannan digon bakin kuwa daka gani guda daya tilo ba komai bane face kai Ashwar Kai kadai nake so bazan so wani ba yan kai ,idan kuwa aka aura mini wani ba kai ba saidai ya zauna da gawata”
.
Haka dai Ashwar da mabaruka sukaci gaba mahawara yana ta kokarin nuna mata matsala har zuwa gabannin magariba ,sannan ya tafi gidan gona ita kuma taci gaba da tunanin hanyar dazata bi ta shawo kan al’amarin .
Wannan shine abin daya faru tsakanin jarumi ashwar da gimbiya mabaruka .
.
Shuraih ke magana
.
Al’amarin sarki abul dinar kuwa lokacin daya bar gidan ‘yarsa mabaruka sai hankalinsa ya dada dugunzuma ya rasa abinda yake masa dadi aduniya , har ya isa turakarsa yana cikin wannan hali , ya kasa zauni ko tsaye sai da dukkanin barorinsa da fadawansa suka fahinci lallai akwai abin da yake damunsa .
Bayan yayi dogon tunani sai ya tura aka kirawo masa yan majalisarsa cikin turakarsa daga cikin yan majalisarsa sarki Abul dinar akwai waziri, galadima ,wambai da Gulmanu sarkin matsafa na garin.
.
Bayan dukkaninsu sun zauna , sai sarki Abul dinar ya basu labarin abinda ke faruwa tsakanin ‘yarsa mabaruka da kuma jarumi Ashwar, sannan yace
“Kunsani cewa abin kunya ne ace ‘yarmu ta auri bakin bawa ,tabbas idan akai martabar masarautarmu ta zube , sauran kasashe ma dake makwataka damu sai sunzage mu sun raina mu ku sani idan muka sanar da mabaruja kuru-kuru cewa ba zamu amince ta auri ashwar ba , tabbas zata iya hallaka kanta, nidai nace da ita zan bata shi amma bisa sharadi ,sharadin kuma nace sai gobe da safe zan tara jama’ar gari na fadi a gabansu .
.
Toh ku sani sharadin nan fa ni kaina ban san shi ba , wannan shine dalilin dayasa na tara ku anan, inaso muyi tunani mai zurfi mu kafawa ashwar sharadin nemo wani abu mai tsananin wuyar samu a duniyar nan, wanda a sakamakon neman sa ma zai hallaka in yaso kun ga dole mabaruka ta rungumi kaddara”
.
Yayin da ‘yan majalisa suka ji wannan bayani na sarki abul dinar sai duk suakayi shiru suka shiga tunani aka rasa wanda zaice kala , har ya zuwa wani lokaci daga can sai gulmanu sarkin matsafa ya mike yace
.
“Ya sarkin sarajkai hakika ni ina da mafita akan wannan al’amari kuma na rantse da wata sharadin da zan dora Ashwar akai bai is ya haye shi ba ina so ku yi hakurin jin wannan sharadi har zuwa gobe da safe “
.
Koda abul dinar yaji wannan batu sai fuskarsa ta fadada da murmushi yace na yarda dakai sarkin matsafan duniya gulmanu , shikenan na sallameku, kowa ya tafi gida sai gobe da safe mu hadu a kofar fada
.
Nan take ‘yan majalisa suka watse batare da wani daga cikinsu yace kala ba aka bar sarki acikin dumbin farinciki
.
Birnin sarwaliya babbar garine mai tsohon tarihi ,wanda a halinm yanzu sarki abul dinar yake sarauta a cikinsa gaba daya al’ummar farin ma’abota Addinin bautar wata ne , duk sa’adda wata ya cikja kwana goma sha biyu gaba dayansu maza da mata yara da manya sukan fito tsakar dare , suyi sujjada ga watan suna masu fadin bukatunsu da rokon gafarar kurakuransu, wannan abu ne wanda ya yi matukar tasiri zukatunsu
.
Bayan sarki yagama shawara da yan majalisarsa sai yasa akayita shela da yekuwa aka sanar da jama’ar gari cewar gobe da safe ana gaiyatar kowa a fada ba ayafewa ko da yara ba . Masu shela basu daina sanarwa ba har sai da dare yayi , sannan suka je suka kwanta.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kashe gari jama’a sukayi ta tururuwa suna zuwa fada kungiya kungiya ,ayari ayari ,har daga kauyuka,kai wasu ma saga makotan kasashe sai da suka zo don son ganin kwakwaf,saboda labari ya bazu cewa akan maganar ‘yar sarki ne da bakin bawan data nace tanaso.
A cikin wadanda suka halicci wannan taron akwai wasu jarumai kimanin su shida masoya mabaruka , wadanda suma ashirye suke dasu salwantar da rayuwars son ganin sun sami aurenta.
.
Bayan sarki abul dinar da’yan majalisarsa sun hallara , sai aka tura wani bafade yaje yakira ashwar daga gidan gona . A sannan ne gimbiya mabaruka ta iso tare da kuyanginta da baradenta , nan take taje ta zauna bisa kujerar dake daf da karagar sarki ,
Sarki ya dubeta yai murmushi .
Hakan keda wuya kuma sai ga ashwar tare da da bafajen da aka aika ya kirawo shi sun iso, da zuwa aswar ya fito tsakiyar filin fada , ya fadi yayi gaisuwa ga sarki , bayan an amsa gaisuwar ne aka yi masa izinin mikewa tsaye , yana mikewa ne yayi ido biyu da abar begensa tana mai yi masa wani irni murmushi mai tona asirin zuciya .
Cikin karfin hali ashwar ya yiwa mabaruka murmushi , sannan ya kau da kai ga barin kallonta don tsoron kada tsananin kyawunta ya rinjayi zuciyarsa ya kamu da sonta .
Tun daga ranar da ashwar ya fahimci cewa gimbiya mabaruka na sonsa , tsoro da damuwa suka cika zuciyarsa .
Badon komai ba sai don ya tabbatar mahaifinta ba zai maraba dashi ba , wannan dalili yasa ya danne sha’awar bege da so a zuciyarshi ,har a halin yanzu ashwar bai yadda son mabaruka ya shige shi ba , kai in ba don ma bin umarnin sarki ba da tabbas ba zaizo wannan kira da akayi masa ba.
.
.
A cikin wannan gona ta sarki wadda ashwar ki aiki , akwai wani dattijo abokin aikinsa wanda ake kira makabul. Makabul tsohone sosai , domin shekarunsa sun kai kimanin tamanin da doriya . Makabul aminin baban ashwar ne , don asali ma tare aka siyo su a matsayin bayi daga nahiyar kasar bakaken fata,
Tun suna samari yan shekara sha tara.
Tun ashwar na yaro karami ya taso yake ganin abotar da ke tsakanin mahaifinsa da makabul, don haka bayan rasuwar mahaifinsa sai ya rike makabul tamkar mahaifinsa komai zaiyi sai ya shawarce shi . Yanzu hakama makabul dinne yabashi shawarar yazo fada don amsa kiran sarki kuma yace dashi kome aka bukaci da yayi akan mabaruka kada yaji tsoron komai ya amsa cewar zaiyi, komai wahalar al’amarin. Koda ashwar ya tambayi makabul dalilin da yasa yace ya sai da ransa.
.
Sai yace dashi” tun mahaifinka nada rai mun taba zuwa wajen wani boka wanda yayi bincike akan ka , bokan ya sanar damu cewa zaka shahara a duniya , kuma zaka auri ‘yar sarki, amma sai ka karbi Addinin musulunci
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yayi shiru yana tunani daga can yace” kai baba makabul yanzu a ina zan sami ma’abocin wannnan addinin daka fadi? Kasani cewa babu masanan sa anan garin dakuma kasa shen kewayenmu”
.
Makabul yayi murmushi yace “kada ka damu akwai tafiya da zakayi tabbas zaka hadu da ma’abota Addinin musulunci,da zarar kun hadu ka karbi Addinin, in da rabon mu ma zaka dawo gida ka sanar damu wannan Addini mu karbe shi, don tabbas shine Addinin gaskiya , amma kiri kiri sarakunanmu sun ki shi don kwadayin duniya , da son mulkinsu na kama karya “
.
,
Duk wannan hira ta wakana ne adaren jiya tsakanin ashwar da makabul.
.
Yayin da ashwar ya karbi umarnin mikewa tsaye gaban sarki a tsakiyar fada, sai sarki Abul dinar da sarkin matsafa gulmanu suka dubi juna , nan take gulmanu ya mike tsaye , yayi gaisuwa ga jama’ar gari sannan yace
.
“Yaku al’ummar sarwaliya kun sani cewa sarkinmu ya dade da rashin samun haihuwa sai bayan shekara da shekaru ya sami mabaruka,
Yau gashi Allah ya yarata takai mun zalin aure, ku sani cewa ‘ya’yan sarakuna jarumai, da mtsafa sunzo da yawa ba adadi sun nemi aurenta , amma basu samu ba saboda tace bata sonsu .
To yau an wayi gari gimbiya mabaruka ta budi baki ta fadi wanda takeso ,kuma bawani bane face bakin bawannan dake tsaye agabanku wato ashwar”
.
Nan fada ta rude da hayaniya sai da aka yi tsawa sannan kowa ya yi shiru.
.
Boka gulmanu yaci gaba da cewa ” to mu muna da ka’idoji a wannan masaruta ta mu muna kafin mu aurar da yar mu duk wanda zai auri ‘yar sarauta dolene ya kasance daya cikin uku, abu na farko shine sai ya kasance. Mashahurin mai arziki , abu na biyu dole ne ya kasance dan sarauta , abu na uku dolene ya zama jarumin da yayi mashahuriyar jarumtaka a duniya . Kun sani cewa wannan saurayi ashwar dake tsaye a gabanku bai kasance cikin daya daga cikin wadannan ka’idoji dana lissafa ba saboda haka yanzu dama daya gareshi dole ne yaci jarabawar da zamu yi masa akan jarumta , indai yaci wannan jarabawar to zamu amince mu aura masa gimbiya mabaruka”
.
.
Ehem shuraih 99% ke magana muje zuwa
.
Koda jama’a sukaji wannan batu sai akayi shiru kai kace mutuwa ce ta gifta ,
Kowa ya kasa kunne don yaji wace irin jarabawa ce za’ayi wa jarimi ashwar.
.
Boka gulmanu yayi shiru zuwa ‘yan dakiku kadan sannan ya nisa yace”Abin da muke so ashwar yayi don mu tabbatar da jarumtakarsa shine , munasa kaje birnin Duma ka shiga fadar sarkin Aljanu kifyan, ka dauko mana Bishmalu dan sarkin Misra wanda tun yana jariri sarki sarki Kifyan ya sace shi, ahalin yanzu Bishmalu ya cika shekara ashirin da biyar. A duniya .
Kasani indai kayi nasarar dauko Bishmalu , sarkin Misra yayi alkawarin zai raba kasarsa biyu yabaka Rabi , mu kuma take zamu aura maka gimbiya mabaruka , kaga ka jefi tsuntsu biyu da dutse guda kenan wato ga sarauta ga auren ‘yarsarki
.
Boka gulmanu na gama wannan jawabi fada ta sake rudewa da hayaniya, kowa na cewa wannan aikora da haline , dan tabbas an san cewa babu wani mahaluki daya isa yaje birnin Duma don gari ne na Aljanu zalla , Aljanun ma bakake mazalunta kuma kafirai, sarkinsu kifyan shine ubangijinsu don shi suke bautawa.
.
Ragowar jaruman nan guda shida , wadanda suka zo da niyyar sallama rayuwarsu son aurar Gimbiya mabaruka sai duk suka zare jikkunansu suka boye a cikin jama’a don sun tabbatar da cewa ba zasu iya cin wannan jarabawa ba, dominn labari ya bazu ko’ina a duniya cikin wannan zamani cewar sakin Aljanu kifyan ya zama gagara badau, ya Addabi dukkan aljanu da bil’adama dake doron kasa.
.
Littafin :- king of Adventure stories(Abdulaziz sani madakin gini)
.
.
WANE NE BISHMALU
.
YA AKAI SArKIN ALJANU KiFYAN YA SACESHI
.
SHIN AShWAR ZAI YADDA YA AMINCE DA WANNAN JARABAWAR
.
IN MA YA AMINCE SHIN ZAI SaMU NASARAR DAUKO BiSHMALU DAGA FADAN SARKI KIFYAN
.
.
Domin jin wayannan amsoshi sai ku tareni a babbar goro part 1 B
.
.

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: