Takobin jini 1 part 8

 Takobin jini 1 part 8
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 29 Aug, 2017
Upload Time 3:41 am
Hits 543 Hits
Comment No Comments

Description

TAKOBIN JINI»» . Marubucin Littafin
Shuraih usman . Part 8⃣ . . . . Yayin da
waziri da hakimai da sauran fadawa
sukaji Abin da sarki gulmanu yafada , .
sai farinciki ya lullubesu Dalilin
wannan farincikin kuwa shine izan har
muddin sarki gulmanu ya kyalkyale da
dariya haka kawai batare da wani
daliliba , toh hakan na nufin yana
marmarin yin kisa, Sannan kuma
wannan kisan kowaye ya samu kashewa
yake don ya kashe babban hakiminshi
da kuma galadima duk ta dalilin
wannan dariyar. . Shiyasa yanzu dayayi
dariyar hankalin waziri ya dugunzuma
ainun , amma koda yaji sarki ya ambaci
abin dayasa shi wannan dariyar sai
shima ya kamu da farinciki. . Sannan
Gulmanu yace kayi sani yakai wazirina
sannan kuma dirkar birnina Na samu
macen da zan aura kuma ba wata bace
illa Sarauniya Lasmin mai mulkin
birnin Dimashka. . Koda waziri dariku
tare da sauran fadawa sukaji abinda
mai martaba gulmanu yafadi nan take
suka shiga hankalinsu farincikin dake
fuskarsu yakau sannan wani alama na
tashin hankali ya ziyatarci fuskokinsu,
nan take Gulmanu yacigaba da bayani
sannan kuma kai waziri dariku kaine
zaka wakilceni kaje birnin dimashka ka
nemo min auren sarauniya lasmin,nan
da kwana biyu zakuyi shiri kutafi izuwa
birnin dimashka , . koda sarki gulmanu
ya idar da maganarsa bai jira amsar da
wziri zai basa ba ya tashi sannan
yanufi cikin gidan sarautarsa Wannan
shine Abun dayafaru abirnin ashdamir
sannan afadar sarki gulmanu . . ¤¤¤¤.
¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤ . . Al’amarin gimbiya
suraila kuwa wato matar marigayi sarki
ashbir yayin dataga wannan bishiyar ta
rikide izuwa masifaffen wuta , sai ta
rufe idanunta da tafukan hannunta.
Don tagama sadakarwa cewa mutuwarta
tazo, yayin da wannan wuta yai sama
can kololuwar sama , . sai wata murya
mara dadin sauraro maikama da karan
aradu ta Barke da dariya sannan takara
ta fashe da kuka ,haka tacigaba da kuka
mai hade da dariya bayan tayi mai
isanta sai tayi shiru sannan kakkausar
muryar tafara magana; . ki yisani yake
wannan bil’adama kin gama cutata
Aduniya gabaki daya Amma kafin na
hukuntaki,zan fadamiki sanadiyar
wannan dariyar mai hade da kuka
danakeyi, Da farko sunana sham’una da
ga dubyalu sarauniyar bakaken Aljanu
na duniya gabaki daya , Mun kasance
muna bautawa wata gunkiyace wadda
muke ta maciji sannan duk bayan sati
muna yankamata bil’adama sannan
jinin mu bata tasha. . Mahaifiyata ta
gaji sarautar sarauniyar aljanuce a
hannun kanin mahaifinta mai suna
saxraz , Wata rana mahaifiyata tana
fada anacikin fadanci sai ga wani
manzo, Yana sanye da fararen kaya
wadda akayimata ado da
zubarjadi,sannan daura wata rawani
wadda tarufe fuskarsa , . koda wannan
bako yakaraso. Gaban mahaifiyata wato
dubayalu , . Sai ya fito dawata takarda
sannan ya mika mata , . Dubyalu tai ma
magatakarda umarni akan ya amshi
takardar ya Karanta afili Domin aji
abinda ta kunsa. . Magatakarda ya
amshi wannan takarda , Yafara
karantawa kamar haka; . sako daga
sarkin musulmai na bil’adama zuwa ga
sarauniya dubyalu na bakaken Aljanu,
kiyi sanicewa nasmi labarin cewa kina
bin hanyar bata amma ban damu ba
nace ma fadawana, . aiku Aljanu ne
wata kila acikin Aljanu yan uwanku
asamu wadda zasu nuna muku tafarkin
Allah madaukakin sarki, Amma koda
nasmi labarin jahilcin naki har yakai ga
kina kamo bil’adama a cikin birnina
kuna yankawa wannan gunkiya ta
maciji,sai hankalina ya dugunzuma
ainun , . Ina mai kira agareki yake
wannan sarauniya daki bar wannan
hanya dun bamai bullewa bane ,kidawo
tafarki na gaskiya, Ki shaida babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma
Annabi muhammadu(saw) manzonsa
ne. . Izan kuma kikayi taurin kai Wato
kika bujire zan zo da runduna in
yakeki. . Sannan inkafa daular
musulunci abirnin naki Daga sarkin
musulmai Abul Abbas bin hafiz, sarkin
birnin nurul Ansar. . . END OF BOOK 1 .
SHIN SARAUNIYAR AlJANU ZATA
AMINCE DA BUKATAR SARKI ABUL
ABBAS . . WACECE SARAUNIYA LASMIN
. SHIN ZATA AMINCE TA AURI
GULMANU . . IZAN SARAUNIYA
DUBYALU TAKI AMINCEWA DA
BUKATAR ABUL ABBAS SHIN WANI
IRIN YAKI ZA A KWAFSA . YAYA
LABARIN SURAILA DA ALJANI
SHAM’UNA . . SHIN WANI HUKUNCI NE
ZAI MATA SANNA WANI LAIFI NE TAYI
MASA . . Domin wayannan tarin
amsoshin sai ku tsumayeni a TAKOBIN
JINI littafi na biyu . . MARUBUCI:-
Shuraih Usman . SHEKARAR
RUBUTAWA:- 2016 .

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: